Sashe 11
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zama tayi tana ƙaƙƙyafta idanun ta kamar wadda tayi ƙarya.Rabi mai aikin Ummah a asashen dafa abinci dake tsaye gefe, da sauri kuwa tayi serving nata bayan ta zaɓi abinda take buƙata.Sauƙin ta ma babu wanda ya kula kan ta dan sun saba da rashin fitowar ta ta da wuri sai taga dama Dan haka suke fara cin abincin su ba tare da sun jira ta ba idan ka gan ta ta fito da wuri to Abba ya dawo ne kafin shima a cire marmarin sa.
Tun da suka fara cin abincin babu wanda ya cewa kowa ƙala dan sun saba da rashin yin magana idan ana cin abinci sai dai koda magana kaji to bakin LINA ne kuma Abba na kusa.Shirun ne ya ishe ta gashi har yanzu babu wanda ya tashi tsakanin Ummah da BILAL hakan ya sa ta yin ɗan tari na farko babu wanda ya Kalle ta na biyu ma haka ana uku ne UMMAH ta miƙa mata ruwa cikin kulawa shiko BILAL spooon ɗin hannun sa ya ajiye yana zuba mata idanun sa da suke saurin kaɗa hantar cikin ta,Tana kafa bakin ta a ruwan kuwa jikin ta ya fara tsuma ganin kallon da yake mata wanda ya sa ta sarƙewa Dagaske idanun tane suka firfito take suka yi jaaa na azaba.
Hawaye REENA ta fara tana miƙa mata ruwa cikin Tausayin yar uwar Tata.
Itama umma da rarrashi take ɗan bubbuga bayan ta tana furta mata kalmar sannu.Shiko BILAL Allah ya ƙara kawai ya iya furta wa A hankali yana Hararar ta wanda dama da gangan yayi saboda ya fahimci tarin munafunci ne,miƙewa daga gurin yyi yana yin falo ba tare da ya bi ta kan su ba..
Rashin Chaji ya sa baku samu page jiha ba saboda biyu ya kamata a samu.âœï¸
Wannan labari na kuÉ—i ne akan N#1000. Yanzu muna kan free pages, kuma baza,a same su da yawa ba gaskiya dan haka kuna iya fara yin payment.
1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
*08069059746*
Daga
AlÆ™alamin âœï¸
GIMBIYAR TASKIRA 👑
FA'EEH BG âœï¸
FIRSTLADY 🙌
LIKE,REACT, COMMENT sune kawai nake buÆ™ata,shine zai nuna mini yadda kuka karÉ“i book É—in..âœï¸
_Typing_
*💋KURMAN ƘADDARA💋*
©®*FA'EEH BG*
*BOOK ONE*
free pages👌
P..0ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
''''"""$""""$"""""
*Contact dis line👉08069059746 for advert.*
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn
💋💋💋
Hawaye ne suka silalo mata masu zafi na azaba cike da Haushi da baƙin cikin sa na furucin da yayi mata cikin rashin tausayi ta matsa gefe tana sakin kuka Itama REENA zama tayi gefen ta kafin kuma ta rungume ta suka haɗe kai waje ɗaya.
Ummah murmushi kawai tayi cike da ƙaunar ya yan nata ta furta " wai duk saboda kin samu chocking ne zaku mayar muna da gida gidan kuka,Allah idan baku daina ba zan bar ku dashi kun san sauran ".
Shiru suka yi kamar ruwa ya cisu dan kamar sun manta waye yake zaune cikin falon.
REENA ce ta riƙo hannun yar uwar ta da idanun ta suka yi jazir na azaba.
Fisgewa LINA tayi tana barin dinning É—in tana gunguni wanda ba kowa zai iya cewa ga abun da ta ke faÉ—a ba.
Har ta kusa shigewa lungun da zai sada ta da bedroom ɗin su dake ƙasan ta taji saukar Muryan sa " Wallahi kika shiga ɗakin nan sai kin yi tuman kwaɗɗo ɗari "
Cikin sauri ta juyo tana share hawaye kan ta ƙasa saboda fushi take yi dashi ta zo ta zauna kusa da REENA da ke zaune kusa dashi ta yi shiru tana kallon Cartoon da ya kunna mata bayan dawowar su Falon ita da Ummah.Ummah da ta gama bawa masu aikin na ta umurni ne ta zo ta zauna cike da kulawa ta furta " Soja ya hanya ya kuma aiki,tunda ka ƙi bari mu ko gaisa sai ka fara ganin ƙannen ka ". Sunan Soja itace kawai ke kiran sa dashi.Murmushi yayi yana kallon mahaifiyar ta sa Abar son sa sanyin idaniyar sa sannan ya furta " Ummah Alhamdulillah komai lafiya lau".
" Amma baka cin isasshen abinci ko Soja,dan wannan karon ban ga kayi wata ƙiba ta arziki ba ".
Murmushi yayi kafin ya ce " Ummah ai idan nayi ƙiba aikin zai min wahala,Gudu ma sai ya gagare ni "
Idanu ta zuba masa tana ƙara ƙare masa kallo kafin cikin cire Muryan wasa ta furta " Dagaske fa nake yi Soja ka yi rama a wannan karon,me yake damun ka ".
Shiru yayi zuciyar sa na wani irin chanza sauti kafin ya samu damar bata amsa yana furta " Ummah aiki ne kawai,kin san munje wani mission na sati biyu to Bama samun isasshen abinci achan ko daga ni har ya ra na kowa kika gani zaki ga ya chanza saboda yanayin wurin da muka samu kan mu " .
Kai ta girgiza masa kamar ta yarda kafin ta sauke ajiyar zuciya da ita kaÉ—ai ta san ma,anar ta.
A ɓangaren sa ajiyar zuciya ya sauke a ɓoye yana rufe idanun sa bayan ƙare ma LINA kallo da ke zaune kamar wadda an ka yiwa mutuwa fuskar nan Tata ta sauya ta wani karkace kai irin bata son magana da kowa ma.
Ammah ce ta ƙyafato ta bayan sun haɗa ido yanzu ganin har yanzu ranta a ɓace yake ta furta " Zo nan ".
Zama LINA tayi a kusa da ita wanda ya ƙara tabbatar mata da fushi take yi da kowa dagasken.Dan da ba haka ba kan ƙafafun ta zata haye.
Murmushi tayi tana ɗago face ɗin tace " ALINA my baby girl waya taɓa min ke,waya taɓa sanyin idaniyar SS family ne ''Tayi zancen tana janyo ta jikin ta duk da ta san kan wa ake fushin.
Kuka LINA ta fashe da shi mai cike da shagwaɓa tana furta " Ba Yaya Bilal bane ya min Allah ya ƙara ai dama na san baya sona,ya fi son REENA ai ban manta ba yace ni ba ƙanwar sa ba ce bai haɗa komai dani ba ".
Buɗe idanun sa da suka masa nauyi yayi saboda bacccin da ke cin su yayi yana sauke su kan ɗan ƙaramin bakin da ke zuba kalaman da baka taɓa tunanin ta iya zaro su saboda yarintar ta.
Murmushi kawai ya saki yana kallon REENA da ta zuba masa idanu tun ajiyar zuciyar da ya sauke wanda kaÉ—an ya rage tace masa Yaya Ba ka lafiya ne naji ka yi ajiyar zuciya.Sai kuma ta dakata saboda Ummah ta katse mata zancen na zucin ta da take son fito dashi ta hanyar yiwa LINA magana.
Jinjina kai yayi yana furtawa azuciyar sa Lallai LINA bata da mantuwa shi da yayi zancen ya daɗe da mantawa kuma lokacin tun tana yar shekara bakwai ne a duniya lokacin tana cikin ganiyar rashin jin magana babu wanda bata addaba ba cikin estate ɗin ita faɗa da wanchan yau gobe da wani wanda shi kuma ya sako ta gaba dan ya tsani rashin jin magana dan duka yaran familyn suna tsoron sa sosai itace kawai mai kunnen ƙashi ya rasa dalilin rashin jin na ta gashi kullum abun nata gaba yake yi,shi ya sa ya ke matsa mata kamar yadda take cikin rashin ji kullum yake hukuntata sai dai banza dan Tsoron nasa ma bai wuce shekara uku da ta fara yin sa ba.May be ko saboda suna gida ɗaya ne bata jin maganar sa Oho.
Hararar sa Ummah tayi bayan sun haÉ—a ido.
Kafin ta furta " Soja kar ka ƙara ta kura ma sanyin idaniyar gidan SS kaji ka iya bakin kaji abun da aka yi tun shekara huɗu Bata manta ba abun na ran ta,yanzu dai kar ka ƙara dakar min Yaa kuma ka bata haƙuri ,ko muci ga da fushi da kai ".
Idanu ya zaro yana furta " Ummah Haƙuri fa,ai ita ya kamata ta bani haƙuri,a gaban ido na nagan ta tana dakar REENA kamar Allah ya aiko ta,sai kace ba yar uwar ta ba,kamar ba ciki ɗaya suka fito ba,wannan wane rashin ji ne idan har tayi wa wasu dake waje ai bai kama ta ta yiwa REENA ba,bana son yawan faɗan nan na su abu kullum kamar gaba yake yi,kuma a duk lokacin da za,ayi rigimar itace fa mara gaskiya fa Ummah ".
Shiru yayi dan har ransa ya ɓaci tuni bayan tunano irin rashin jin da tayi tayi a baya dan bata ragawa kowa a cikin yaran gidan ga rashin kunya ga manya sai in bata ga damar ka ba,ko bata ga dama tana yi sai dai a dake ta tayi kukan ta ta share hawayen ta.Ta sha yin dambe iri iri da yan matan har haƙora ta taɓa cirewa Ninah ɗiyar ƙanen mahaifin su.Shi yasa har yanzu ba wani shiri take yi da ita ba.
Kan sa ya sauke ƙasa cike da haushi yana ƙara furta " Allah Ummah ke kike ƙara wa aya zaƙi kamar kina goyon bayan yarinyar nan akan abun da take yi,ace mutun bai son zaman lafiya,kowa ya buɗa baki sai ya faɗi mara daɗi kan sa,ni bazan lamun ta ba gaskiya Ummah,ba zan iya jure shirmen ta ba ".Ya kai ƙarshen maganar matuƙar ransa ɓace.Jikin sa har ya fara ciccira LINA dake hango sa ƙara shan jinin jikin ta tayi tana rufe idanun ta saboda tsoron da ya ƙara kama ta ganin yadda ya'yan na su ya juye lokaci ɗaya da alama zuciyar sa ta ke son motsawa dan Allah ya zuba masa zuciya dan haka baya son a kawo masa wargi sannan bai cika shiga harkar yaran gidan ba,bare ma kuma duk tsoron sa suke yi.
Ganin yadda ko ƙanwar sa da suke ɗaki ɗaya bai raga ma ba.
Murmushi Ummah ta sauke kafin ta kalli fuskar LINA da idanun ta suke a rufe.Kan ta ta ɗauke kan ta ,tana mayar wa kan REENA da take cikin tsoro ji take kamar a ce ƙyat ta ruga ganin yadda ran yan maza ya ke son motsawa LINA zata janyo musu Masifa da rana tsaka.Dan idan yana irin wannan yanayin ko Ummah da ƙyar take tanƙwasa sa bare ma Abba da yake ba zama yake yi sosai ba saboda harkar business ɗin sa.
Kai ta girgiza kafin ta furta "SSB" dan wata rana haka take kiran sa.