← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 110

Sashe 22

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi kawai Inna ni tayi kafin ta furta " Kuje kuma idan an taso kar ayi biye biye nan dare ne yanzu ba rana ba banda rigima ".

Tsalle SHATOU tayi tana murna tana cewa " to Inna ni ".

Bibu da bai so fita ba baccin sa ya so yayi ya miƙe yana saka takalmin sa.
Babu littafin karatu babu komai haka ta fice kuma Inna ni ta gani sai dai kawai ta girgiza kan ta tana fata da Addua,a Allah ya dawo mata da su lafiya babu wata rigima.Dan ta san asalin inda za.,aje ba makarantar ba kawai.

Makarantar daren suka fara zuwa basu ko yi mintuna goma ba ta nemi izinin zuwa gida wai kan ta ke ciwo haka aka saka Bibu ya raka ta.

Tun a makarantar yake kallon ta yana son ya ce wani abu sai da ya bari sun fita sannan ya ce " Adda SHATOU ƙarya fa kika yi,kwanan nan sai zuba ƙarya kike yi ".

" Eh nayi ai ƙarya akwai inda ta halasta "

" Yawwa Bibu fili zamuje in zaka je idan kuma ba zaka je ba ka ce Baka da lafiya sai kayi gida kace shine ya sa ka dawo,ni kuma sai na zo daga baya "

" Kuma dan Allah Karka faÉ—awa Inna ni na tafi Filin wasa ".

Baki Bibu ya turo gaba kafin ya ce " Ai tare muka zo tare zamu koma Ni bazan koma nikaÉ—ai ba mu tafi na yi kallo ko na shiga nima kuyi dani ".

Dariya tayi tana laƙƙamo hannun ta wuyan sa shima ya laƙƙaama na sa sannan tace " Yawwa Bibu na kusa zama SHATOUn birni haka nake jin kamar zan tafi,kuma Allah Dagske haka nake ji ".

Dariya yayi kafin ya ce " Babu inda zaki je Adda SHATOU,to me zaki je yi chan ".

" Oho Nima ban sani ba,Allah ya sa alkhairi ne na siyo maka Raken birni mai ƙara wa kan ta zaƙi da ragewa ".

Dariya Bibu ya ke ce da ita yana furta " Kai Adda SHATOU ya sifn ban yadda akwai wannan raken ba ke har kin yarda da maganar Iro ,ance shi ya kawo zancen nan wai akwai wannan raken ".

" Mtsww" taja tsaki jin an ambaci sunan maƙiyin ta kafin ta furta.

" Eh lallai ƙarya ne Bibu amma zan maka tsara ba mai kyau kana so ko ".

Kai ya jinjina mata cike da Murmushi haka suka cigaba firar su har suka isa chan firar wata shirme wata dai dai.

Koda suka isa filin cike take yara na ta wasa sai yan manya irin su Iro gefe ɗaya suna shan rake suma taɓa firar su suna kallon abun da ke waka na.

Cike da farin ciki sauran yaran suka tarbe ta suna kiran sunan ta.
Wasar yar jari ri bisa gado suka cigaba da yi inda aka yiwa SHATOU ta4fna ta dariya sai dai rabin hankalin ta na na ga kan jama'ar dake wajen dan akwai hasken kara da aka kunna.
Bibu ma cikin maza irin sa ya shige suka cigaba da wasa.

Ita kuwa SHATOU a jirgi na tara ne da aka wulla ta baya a lilon da suka koma yi yanzu ta hango dai dai kalar yaguwar dake ga rigar da ta gani a barcin ta.Hakan ya sa cike da sauri ta ce su ajiye ta dan tabbatar da abun da ta gani.Wanda ke sanye da rigar ya juya baya yana Marmara gyaɗa.Cikin azama suka sauke ta ganin yadda take ta ɗaga musu murya dan har sun tsorata.A hankali take sanɗa dan fara ganin wanda yayi aikin da kyau.Aiko sai aka yi sa,a dai dai lokacin da ya juyo da fuskar sa...✍️

Wannan littafi na kuÉ—i ne akan1000

*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh 💞

*_Typing_*

*💋KURMAN ƘADDARA💋*

*©®Faiza Almustapha Murai*

*FA'EEH BG*✍️

*BOOK ONE*

*~Paid~*

*Second to the last free pages*👌

P..1️⃣1️⃣

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Posting room link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn

*LITAFFAN MARUBUCIYA*
_*A MAFARKI NA SANTA*_
_*RAYUWAR MU A YAU!*_

_*SHAGALI💃💃💃💃nace!! Ina yan kasuwa manyan Hajiyoyi masu Capacity nace ga damar ku tazo domin kuwa muna tallata muku hajar ku,kowace iri ce a farashi mai sauƙi idan ki/ka na buƙata,sai ku tuntuɓe mu wannan lambar +234 808 750 4734 dan tallata hajarku.Sai kun zo.*_

🪐🪐⚡🪐🪐⚡🪐🪐

A hankali take sanÉ—a dan fara ganin wanda yayi aikin da kyau.Aiko sai aka yi sa,a dai dai lokacin da ya juyo da fuskar sa
yana kallon ta jin sauran Abokan su na maganar nufowar ta wajen su dan yace kowannen su ya fita iskan ta sai an manta sai su rama abun da ta musu..

Idanu ta ƙara buɗewa da kyau dan tabbatar da zargin ta shi ɗin dai ne dan tass haka fuskar shi ta bayyana gare ta.Cike da wani irin haushi da baƙin ciki take kallon sa sai dai ta kasa cewa komai sai ma Riƙe ƙugu da tayi ,tayi tsaye tana ƙarewa dukkanin su kallo.Bibu ne ya matso gurin da sauri gudun faruwar wani abun hakan ya sa ya riƙo hannun ta yana furta " Addah SHATOU lafiya ".??

Ƙin bashi amsa tayi sai bin hannun ta da ya fara jaaa da kallo tayi kafin ta yi murmushin da ita kaɗai ta barwa kanta sani.Su Amina ma duk zuba mata idanu suka yi haka ma sauran abokan na Iro sai Surutun su suke wasu suna hayayyaƙo mata na lafiya kallon da ta ke yiwa Iro,Wanda wasun su har sun fara kiran ta mayya mai cin naman mushe Indai Iro ne kurwar sa tafi ƙarfin ta.
Bata tan ka ma kowa ba har ta daina ganin duhun jama'ar wajen dan kai tsaye Bibu hanyar gida ya nufa kuma bata hana sa ba dan ta riga ta sha alwashin ta ƙara tabbatar da shi ne sai ta masa wulaƙancin da bai zata ba.

Sai da suka kusa isowa gida ne suka lura da su Amina a bayan su.Ashe tun É—azu suna biye da su.Dakatawa tayi tana furta " Ku kuma lafiya kuka sako mu gaba ".?

Amina ce cikin ɗan ƙarfin hali ta furta " Dama mun ga kamar ba lafiya ba ne SHATOU shi ya sa nace bari mu biyo bayan ku "

"Idan na faÉ—a muku kuna iya É—aukar mini mataki "?
Tayi furucin tana kallon Amina.

Kai Amina ta girgiza kafin ta furta " Indai wanda bai fi ƙarfi na ba zan iya SHATOU Ni kaɗai ma ".

Murmushin na samu banza SHATOU tayi kafin ta furta " Yawwa Iro nake son Ki tsaya gaban sa ki zazzage sa saboda ya ci mutun cin ƙawar ki ".

Idanu Amina ta zaro ba ita ba har Bibu da ke kallon Shatoun.Haka ma su Ramata.

" Adda SHATOU kin san dai abun da ke tsakanin ku da shi,to ma ai bai Miki komai ba kuma naga yanzu bai ma kula ki ba ".

Hararar Bibu tayi sannan tace " Shine fa yayi rubutun nan a makarantar mu,kuma wallahi ba zan yafe masa ba sai na rama dan ma kar wanda ya dakatar da ni Gara ma Karka faÉ—a a gida kayi shiru da bakin ka ".
Ta kai ƙarshen zancen a hasale kafin ta ƙara furta " Mafarkin sa nayi jiya,da kayan da ke jikin sa,Dama neman mai kayan nake yi sai gashi a she shine dai dan da farko nayi zargin sa.

Idanu da baki dukkanin su suka saki suna kallon ta kafin Amina cikin ƙarfin hali ta furta " SHATOU mafarki fa ba gaskiya bane,sheɗan na iya zuga ki Shine ya nuna Miki Iro,nidai Dan Allah kiyi haƙuri ki bar zancen nan ko kuma ki bari mu tabbatar da gaskiyar ta fili ".

Kallon Amina tayi tana gyaɗa kan ta,ta san gaskiya take faɗa amma tabbas tana buƙatar Son yin maganin sa idan dai har shi ne.Dan haka zata yi binciken kamar yadda ta tsara tun farko da ta tabbatar da shi ɗin ne sai ta masa wulaƙanci.

" Naji " kawai ta furta ta cigaba da tafiyar ta har ta shige gida babu wanda ya ce ƙala a cikin su sai dai suna mamakin yadda zaka ga abu a mafarki kuma kace zaka yarda da abun da ka gani.Gashi Malamin su ya sha faɗa musu bakowa ne mafar ki ne gaskiya ba wani mafarkin sharrin shaiɗan ne kawai.
Sallama Bibu yayi musu ya wuce gida sannan suma suka juya suka yi gida kowace zuciyar ta cike da zullumi.
Jawairiyya ce ta furta " Ni dai ko da an ƙara kirana shaidu zance ban da lafiya gaskiya dan na san sai an yi rigima babba akan wannan zancen dan ba barin sa zata yi ba ".

" Nidai tsoro na kar su bata kashi,na san idan dukkanin su suka dake ta mutuwa zata yi " Amina tayi furucin tana jin hawaye ya cika mata ido.

" Ke Amina ba dai daga magana ba har kin fara hawaye " Cewar Ramata dake kallon ta cikin hasken farin wata.

Dariya ta kece da ita tana furta " shi ya sa duk SHATOU ta fi raina ki wallahi ".
Tsokanar ta suka dinga yi har suka iso gida kasancewar gidajen su suna kusa da juna kowaccen su tayi shigewar ta.

Koda suka shigo Inna ni ce kawai zaune a tsakar gida tana jiran su hankalin ta ba kwance ba ganin lokacin ta shin na su yayi amma ba su iso da wuri ba.

Numfashi ta sauke mai nauyi bayan shigowar SHATOU gidan sannan Bibu.

Bata ce musu komai ba sai umurnin kowa yayi Alwallah ya je ya kwanta tare da tunatar da su mahimmancin Addu,ar kwanciya bacci.

Haka suka shigewar su É—aki kowa ya kwanta bayan yin Addu'a.
A ɓangaren Inna ni itama da baffa na sai da safe suka yiwa juna kafin suka yi Sallama.
Chapter 22 · 0% Book details