Sashe 85
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Lallai fa kamar baƙin nan ne suka zo masu aiki zasu duba aikin ina ga kamar motocin su ne ".
Iro yayi zancen yana ƙara ƙure motocin da kallo da suka ɗan yi nesa da su kaɗan kamar zai hango wanda ke cikin motar.
Shatou kuwa bakin ta,ta mere bayan ta É—auke idanun ta daga kallon motocin.
Iro kuwa da gama furucin ya cigaba da bata labarin faɗan nasu kafin ya koma bata wani labarin daban.Shatou tayi zaton zai wuce sai dai ta ji ya cigaba da tsiyaya surutu kamar fanfo dan haka tun tana ƙaƙalo murmushi har ta kai ta haɗe fuskar ta dan dole fahimtar hakan ne da Iro yayi alamar ta gaji hakan ya sa ya fara ɗan kame kame yana ƙyafce ƙyafcen ido.
Haka ta cigaba da tafiya kafin ta fara zabga sauri tun Iro na cimmata har ya kai tafiyar ta su ta rabu dan ta yi gaba.
Kafin kuma ta runtuma a Guje sai kuma ita da kan ta abun ya bata dariya ta cigaba da ƙyalƙyala dariyar ta ita kaɗai tana gudu tana waigen Iro da shima ya biyo bayan ta yana dariyar sa kamar wani wawa yana kiran sunan ta da alamar ta tsaya,sai kayi zaton wasu masoya ne na asali yadda suke yi.Har ta zo ta gota mutanen da ke tsaye gurin bata lura ba duk da ta ji yadda wajen ya gauraye da ƙamshin daddɗan turare.
Bata tsaya ba sai da ta tsinci kan ta cikin makarantar sannan ta dakata tana nishi.
Malam Bello dake nan yana duba wasu takardu daga tsayen da yake ya ɗago idanun sa ya kalle ta,ganin Shatou ce ya sa ya galla mata harara.Ita kuwa shatou sanda ƙirjin ta ya buga ganin malam Bello dan ta san halin sa duk da haka kuwa ta shanye tsoron ta.Baka taɓa ganewa sai dai idanun ta da take ta ƙyaftawa,alamar rashin gaskiya,dan ta san bata da gaskiya ta yi latti ta san dole zata iya samun hukuncin sa tunda mugu ne.
Malam Bello kuwa cike da faɗa bayan gama sakar mata harara,Ya furta " Zo nan " .Babu musu Shatou kuwa ta zo ta tsaya kusa da shi kaɗan tana tura bakin ta gaba ga ƙirjin ta dake bugawa kaɗan na ɗan tsoron bulalar sa.
" Uban me ya hana ki dawo wa da wuri har aka shige aji " ?
Shiru ta masa taƙi ko ɗaga ido ta kalle sa.
Ran malam Bello ne ya ɓaci dan haka ya ce " Sun kuya nan ".
Bakin ta, ta ƙara turawa gaba kafin ta kai guiwowin ta ƙasa tana yin kneeldown.
Malam Bello yayi zaton ta bashi haƙuri sai dai shiru har bayan ɗan lokaci hakan ya ƙara tunzura shi dan haka ya ƙara sanya ta ɗaga hannuwan ta sama tare da rufe idanun ta.
A ɓangaren shatou ƙafafun ta sun fara ciwo matuƙa amma saboda taurin zuciyar ta kasa ce masa yayi haƙuri.
Ga wata zuciya da take jin tana ta so mata kamar ta miƙe ta yi gida,taana ji duk wanda ya tara ya samu.
Kuma ta sha alwashin ba zata taɓa bada haƙuri indai har malam Bello ne.
A ɓangaren su MAHAJ kuwa suna zuwa bakin inda aka gina ruwa tare da sanya manyan tankuna na ruwa da ake akan aikin su, nan suka dakatar da motocin na su.Da ƙyar uban gayyar ya fito daga mota.
Ko shi sai da ya gama shan ƙamshin sa sannann ya fito yana gyara zaman p cap ɗin sa da ya juyar da ita.
Bakin motar da ya fito ya jingina bayan sa yana ƙare wa wajen kallo da sauran filayen ƙauyen dake zagaye da wajen.
Bai É—aga daga nan ba har su Muby suka fara zagaya wajen.
Tare da jama'ar garin da suka ɗan taru a gurin,suna satar kallon MAHAJ ɗin da gaida shi wanda sai dai ya ɗaga musu hannu kawai fuskar sa sanye da glass ɗin sa da yake ta ƙara yiwa kyakkyawar fuskar sa armashi.
Mafi yawan jama'a sun bi bayan Muby da yake duba ayyukan dan ogan ya gincire anan ya ce su je kawai.
Yana É—an ganin komai daga nesa.
Sai ya zamo daga shi sai masu tsaron sa aka bari sai yan tsirarun mutane da ke bin sa da kallon ƙurilla.
Da kallon ya ishe sa sai ya juyar da jikin sa yana facing motan tare da ɗaura hannuwan sa jikin kan motar yana jan ƙaramin tsaki.Na kallon da yake jin ya dame sa dan shi mutun ne wanda ya tsani a yi masa kallon da ya wuce ɗaya ya tsani kallo yana daga cikin abinda ke takura masa.
Ya É—an daÉ—e tsayen inda a hankali a hankali yake jan tsakin da bai san dalilin jan sa ba yanzu ga idanun sa da suke a lumshe ta cikin space É—in.
Gajiya da tsayin da yayi ne abun ka ga É—an Hutu ga yar ranar da ta fara yin zafi da haske tana kasar masa fata hakan ya sa ya juyo a hankali da niyyar komawa cikin motar da bawa masu tsaron na sa umurni.
ÆŠan kallon gefen sa na dama yayi a hankali sai dai kamar haske hakan ya hango ta tana falfala gudu kamar wata balbela,Bakin ta sake tana dariya,Sai ga Iro bayan ta shima yana dariya kamar wani wawa.
Kallo ɗaya dukkanin su yayi musu ya ɗauke idanun sa yana yatsine fuskar sa kamar wanda ya ga kashi da jan ƙaramin tsaki da ya tsaya iya laɓɓan sa.
Hakan ta wuce a Guje kuwa ta gaban su ba tare da ta kalli ko ɗayan su ba kasancewar hankalin ta ba nan yake ba kawai ta tsinci kan ta makaranta take buƙata dan ta san ta yi lattin dawowa sannan bata son wanchan nataccen ya ƙara tsayar da ita,dan ita kaɗai ta san yadda ta ji tsayuwar dashi mugun Haushin hakan take ji bata da yadda zata yi ne dan hakan kawai take ganin mafita wa kan ta.
Ta ƙasan ido ya bi ta da kallo bayan shuɗawar ta gaban sa.
A jiyar zuciya ya sauke da numfashi na gajiya da tsayuwar sa kafin ya buɗe seat ɗin baya da kan sa ya shige motar ya rufo murfin yana sauke numfashi tare da jingina bayan sa da seat ɗin sa, p cap ɗin da ta yi wa lallausan gashin kansa mai taushi rumfa ya cire ya ajiye gefe ya zamo kyakkyawar fuskar sa ta bayyana gaba ɗaya.Wadda take ɗaure kamar wanda bai taɓa koda murmushi ba bare dariya.
A hankali ya duba wristwatch É—in sa mai tsada da kyau ya É—an kalla a hankali wanda ke É—aure akan tsintsiyar hannun sa,Kallo É—aya yayi ya É—auke idon sa yana jan guntun tsaki,ganin lokaci ya É—an ja.
Bai jima da shiga Motan ba sai ga Muby da Sauran jama'ar.
Shisshiga motar su kayi babu ɓata lokaci dan ya san ogan na sa a cike yake dan bai son jira ko kaɗan duk da aikin sa ne ya bar masa.
Sannan haka kawai zuciyar sa ke ayyana masa MAHAJ ya ga wucewar Shatou da jelar ta da ya dakata daga nan.
Motsin sa ne ya sanya MAHAJ dake zaune shiru kamar kurma ya ɗan buɗe manyan idanun sa dake cikin glass ɗin kafin ya ƙara rufe su.
Shiru ne ya ratsa domin kuwa Mubarak ya san cewa ya na jin sa yan ikon ne ke kai dan haka yayi shiru shima yana É—an satar kallon sa ta madubi tare da nazartar yanayin sa sai dai bai gane komai ba daga abinda yake son gani saboda Glass É—in da yayi wa kyakkyawar fuskar sa kawanya.
" Idan ba zaka iya driving É—in ba let me take over "
Maganar sa ce da Mubarak ya tsinkayo cikin natsuwa hakan ya sa ya É—an juya ya kalle sa kafin ya furta " Zamu shiga waccan Makarantar ".Kafin ya tada motar dama already sauran na gaba sun tada na su.
Har suka É—aga daga wajen bai cewa muby komai ba.
Shi ma kuma muby bai ƙara cewa komai sai dai nanata Muryan da ta fitar da sautin maganar sa ta ƙarshe yake yi da amon ta saboda son gano ƙwaƙƙwafi da wani hange na sa da yayi da bai san ma yadda hakan zai iya faruwa ba.
A ɓangaren shatou kuwa haka ta kasance a wajen saboda taurin zuciya duka malamai sun taru kan ta ta bada hakuri ta ƙi dan shi ya ce da ta bada hakuri ta amsa tayi kuskure zai sake ta.
Baiwar Allah fuskar ta tayi jaaa na wahala ga ƙafafun ta da hannuwan ta sun yi mugun sanyi da ciwo na gajiya.
Suna hakan kuwa sai ga motoci sun fara kutso kai ta cikin makarantar sai dai daga
Gefen sabon ginin da ake musu domin kuwa kwangilar ta koma ta sababbin building bata renovation ba wannan kuma duka aikin MAHAJ ne shi ya bada umurnin hakan sai dai Abbu ya hana ya shiga aljihun sa dole sai nasa dan haka dole ya amince aka shiga ƙarƙashin aljihun Abbun badan ya so ba.
A wannan karon bai wani jima ba ya fito da kan sa bayan buÉ—e masa motar da muby yayi domin kuwa yana son ganin yadda aikin ke tafiya.
Da p cap É—in sa ya fito a hannu kafin ya É—aura ta akan sa muby kuwa ganin yadda yake ta yatsinar fuska saboda ranar da ta buÉ—e ne ya koma cikin motar ya ciro lafiyayyen umbrella ta kare rana ya buÉ—e masa.
Jin yadda ranar ta sauka daga kusa dashi ne ya sa ya ɗaga kan sa ganin lema ruƙe hannun muby ya sa shi ɗan ƙare masa kallo kaɗan ta cikin glass ɗin da muby ke ta Allah Allah ya cire sa ƙwayar idon sa yake son gani fili.
Idanun sa ya lumshe a hankali yana ware su wanda shine ke nuna alamar yaji daɗin abun da muby din yayi kuma hakan godiyar sa ce ya nuna masa duk da kula da shi aikin sa ne alƙawarine da yayi Abbu har gaban abadan.
A hankali suka fara zaga wajen ma'aikatan wajen na na gayar da shi yana gyaɗa musu kai kamar ƙadangare,wasu kuwa ɗaga hannu,wasu ma idanu kawai yake lumshe musu sai kayi zaton wulaƙanci ne ma.