← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 110

Sashe 3

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani daga cikin Abokan na sa ya faɗa kai tsaye bayan tsaida dariyar sa ta ƙeta ganin iro na masa kallon bana son haka.
Iro dai sauraren sa kawai yake yi sai wani cije baki da yake yi yana jan yaji irin na ɓacin rai wanda ya taso masa yanzu.Musammman da ya tuno rashin mutuncin da tayi masa a ranar da ya so buge ta da mashin ɗin sa mara shalan sa da ya addabi ƙauyen da shi wanda ya zo dashi bayan gama JLC ɗin sa da yake faɗin degree ce da ya kwashe yan shekaru a A birni.Anan ƙauyen ma ana secondry school bayan primary wanda kuma nan iya bokon na su yake ƙarewa bakin SS3 wasu ma basu kaiwa ake musu Aure wasu kuwa sukan fitar da ya yan su birane masu kuɗi kenan sai su cigaba da karatun su.Kamar dai Iro ɗai daga cikin ya yan mai gari wanda bai ma fara karatun a nan ba ya fara karatun sa a birni tun Daga jss1 zuwa jss3 bayan gama primary ɗin sa wanda rabi da kwata yawon banza ne da kashe ma matan hanya kuɗaɗe da tangaririya a cikin gari sai ya dawo ƙauyen yana fafa da sunan Jami'a yake yi har ya ci wasu shekaru a chan bai haɗa ko Takardar gama secondry ba sai ƙaryace ƙaryace duk da kuwa yana da ƙananan shekaru shima dan bai wuce sha shidda ba amma Allah ya zuba masa ƙarya ga ɗan ruwan da ya iya ɗan watsawa na mutumen ƙauye da ya je birni shi ya sa mutanen ƙauye suke ji dashi haka ma mai gari da aka rufe da wasu takardun bugi shima ya zauna akan ɗan sa ya haɗa degree yayi karatu mai zurfi a yanzu haka ya na nema masa aikin yi ne da takardun sa,kuma idan aka yi baƙo a ƙauyen shine mutun na farko da ake kira gudun kar a haɗu da Bature wanda bai jin Hausa su kasa iya communication.Ga kuma Case na biyu daga bata Shawara bai daddara ba dan ya san guje gujen ne nata suka sa yayi niyyar kaɗe ta sai komai ya juye.Wannan kenan.

'Zuwan yara ne su biyar da basu wuce shekarun ta ba yan sha uku sha biyu ya sa ta miƙe tana washe baki hankalin ta kwance ta tare su itama da gudun nan na ta kamar yadda suka zo a guje gurin dan dama sun san ta iso tun da har gidan su sun leƙa basu gan ta ba.Sannan suka fito a guje kafin Inna ni ta gan su ta riƙe su gidan kamar yadda take musu idan sun biyo mata haka wanda daga ƙarshe dole Shatu ta baro wajen dan ta san muddin bata gan su ba har lokaci ya cika suna gurin Innar ta tana musu fira Dan bata son fitar kwata kwata ta Shatu wanda kuma da shatu ta ga haka take komawa gida baki kunbure na rashin yin wasar daren da basu yi ba.Abu kamar jaraba.
🤭 Yo Shatu wasan Dole ne.Bari dai nayi shiru kar amini rashin mutunci😂

" Shatu ! Shatu ! Shatu " !

Shine abun da suka haɗa baki gurin faɗi dai dai isowar su kusa da juna cikin washe baki itama bakin ta washe ta riƙo hannun Babbar ƙawar ta Amina daga cikin su ƙawayen nata tana furta " Nidai na zaɓi Abokiya ta ".Kallon ta kawai suka yi babu mai bakin magana a cikin su dan sun san kullum aka zo haka take musu wayau kuma har Amina ta saba duk da tana da ɗan tsoro shi ya sa kafin su iso sai sun gargaɗe ta ko da an zo tace bata son Shatu matsayin Abokiyar haɗin ta.Amina dai bata iya cewa komai ba sai ɗan murmushi da ta ƙaƙalo kafin ta koma gefen Shatun tana ƙara washe bakin ta.
Su kuwa sauran ƙawayen na su kowacce kama Abokiyar ta tayi cikin jin haushi kafin su fara gabatar da wasan na su duk da sauran ƙawayen na ta na amana biyu suna cike da jin haushin abun fifikon da Shatu ke Nuna wa a tsakanin su.Wasannin su suka fara kamar yadda suka saba irin dai wasannin nan na dare da yara ke yi na tsalle tsalle da yar goye goyen nan,wanda yar goye goyen ce ma ke saka Shatu zaɓar Amina saboda sune basa da jiki amma duka sauran sun fi su girma ita cewa take bazata iya ɗaukar ƙatuwa ba.Dan shi take zaɓen Amina kai tsaye bata ma bari ayi wasan a fitar da wanda zai goya wani.Sun yi wasannin su cikin nishaɗi sai dai me suna gab da kammalawa kowa ya watse mazan da ke gurin su Iro kenan suka yo cikin su suna hudi irin abun nan na iskanci suna shigewa cikin su duk wadda ka samu ka rungume.Cikin rashin sa,a Iro ya faɗa hannun Shatu bada sanin sa ba Aiko tana jin yadda ya ke ƙoƙarin rungumar ta ta yi masa mugun cizo a hannun sa da iya ƙarfin ta har sai da ta ja sosai fahimtar shine dama da Haushin shi take matuƙa na ƙazafin da yayi mata kwanan baya wai ta zage shi ta zagi mai gari da ga kawai ya ma ta faɗan ta daina guje guje,bayan rashin mutuncin da ta masa ranar da ya tashi kaɗe ta,bata kula sa ba,dan bata son shigar shigula,ko ranar ma rayuwar ta yayi niyyar illatawa da mashin ɗin sa shi ya sa ta masa tass,Alhalin kuma ƙarya yake mata bata zage sa ko ranar dan daga ƙarshe ma da ya ishe ta sai ta masa tsawa,shine da ya ji Haushi ya je ya faɗa ma Mahaifin ta shine aka mata faɗa ta ji haushi ta gan shi kan hanya ta ƙara gaggaya masa magana cikin rashin tsoron sa.Haka magana tun tana ƙarama har ta zama Babba ta kai ga mai gari an taɓa ɗan gaban goshin sa hasken ƙauyen su,ya tara zaman ba,a si,sai dai mutane sai faɗar suke itace bata da gaskiya saboda a gaban jama'a ta yi masa rashin mutunci kamar sakon ta,kuma sun lura da lalama ya mata maganar guje gujen na ta,haka aka yi zaman babu daɗi daga ƙarshe aka yi sulhu aka tsayar da kowa matsayin sa.Tun daga wannan rana kuma duk da kashe din dake tsakanin su yake bibiyar ta dan shi burge shi take yi musamman ma faɗan na ta ɗan ƙaramin bakin ta ya ke son ganin yana motsi saboda yana burge sa,shi ya sa yake ƙara shisshige mata musamman da ya ke ji da kan sa shima sai yake ganin yafi ƙarfin ta ma dan haka yake da ya gan ta yake mata magana kamar wanda ya bata ajiya ita kuma tana share sa dan mugun tsanar sa take ji dan kan shi Baffa yayi mata faɗa sosai Inna ni ma ta so ta dake ta,da ƙyar ta sha kuma itace mai gaskiya...

Ƙarar da Iro ya sanya ce ta ankarar da mutane halin da yake ciki,kan su aka yo kafin su an kara Shatu ta falfale a guje wasu daga cikin ƙawayen Iron ne Musa da isaka suka bi bayan ta sai dai kafin su an kara ta ɓace ma ganin su saboda mugun gudun da take yi gashi ɗan jikin ba wani ba kamar balbela.Haka suka dawo suna cizon baki da wassafa yadda zasu ci uban Shatu in suka riƙe ta Iro bai so matsawa ga re su ba amma suka matsa masa gashi sun ja masa wahala dan ya cizu.Haka suke kallon sa cikin tausayi sun zagaye sa,suna masa fifita tare da mayar da bakin yadda aka yi.
Su kuwa Su Amina kowaccen su gida ta nufa bayan samun kuɓuta daga hannun Mazan hankalin su a tashe dan sun tsorata basu taɓa musu haka ba sai yau.Kuma sun ji daɗin abun da Shatu tayi ma ɗai daga cikin su duk da basu san kowaye ba dan ta cece su matuƙa.

Hannun sa da ya fara tartsar da jini wani ya yanki gefen hannun rigar sa da ta ji jiki yana furta " Yarinya kamar mayya duba yadda ta fasa maka hannu wallahi sai taci uban ta yarinya mai Shegen tsiwar tsiya wallahi Iro kabar ni da ita Sai na koya masu hankali shegiya dangin Mayu masu farautar naman mushe ".
Ya kai ƙarshen zancen yana ɗaure masa hannun da ke masa zuji shiko Iro Wata irin kunya ce ta dabaibaye shi da baƙin ciki lokaci ɗaya yadda zai wulaƙan ta rayuwar Shatu kawai yake hangowa.Shi da ya san ita ce ai ba zai faɗa mata ba,Amma wallahi zata gane kuren ta sai zaman ƙauyen ya gagare ta haka yake ta tunani kala cike da baƙin ciki dan a cikin a bokan na su akwai masu masa dariya ƙasa ƙasa musamman da suka ga yana jin jiki sosai ya wahala matuƙa.
Suna barin wajen direct gidan mai gari suka wuce maimakon su wuce ɗan ƙaramin chemist na ƙauyen a bashi maganin rage raɗaɗi.

" Keh Adda lafiya kika faÉ—o muna gida a hargitse keda kike shigowa a sace yau sai gaki a guje da alama wayen nan idanun naki basu da gaskiya Adda Shatu".

Bibu yayi furucin yana kallon ta bayan kiciɓus da suka yi saboda ganin bata dawo da wuri ba shine zai saci hanya yaje neman ta.Sai gata a guje tana neman kai shi ƙasa tana zarar ido kamar karen da yayi ƙarya.

Hararar wasa ta sakar masa kafin ta sauke ajiyar zuciya ta yi masa raɗa a kunne tana sakin ƙaramar dariya.
Idanu Bibu ya zaro cike da tsoron abun da ta faɗa masa kafin ya riƙo hannun ta da sauri ya shige ɗakin sa da ita yana kallon ƙofa.
Ba,a fi mintina biyar da shigar su ɗakin na sa ba sun yi jugum sai ga Ƙatuwar Muryan Wani Babban yaron mai gari ya'yan Iro mara kunya yana rabka sallama cikin hargowa.Ƙirjin ta ne ya buga da sauri kafin ta shanye tsoron da ya shige ta domin ita yanzu mahaifiyar ta take tsoron ta ji abun da ta yi duk da ta san da gaskiyar ta duk inda za,aje amma ta san da wanchan mugun ba zai faɗi shine mara gaskiya ba ko a yanzun.
Chapter 3 · 0% Book details