← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 110

Sashe 15

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A ɓangaren su LINA kuwa bedroom ɗin su suka koma kasancewar lokacin makarantar islamiyya yayi suka yi shiri kafin Yayan su ya kora su da kan sa dan ya saba musu hakan idan suka buga latti saboda mafi yawan lokutta suke tsayar da yan uwan na su,kasancewar a tare ake kai su makarantar islamiyya dan dama dalilin raba su shine fitina da suke yawan yi a mota.

A jere suka fito cikin shirin su kowacce riƙe da jakar ta mai ɗauke da Alqur'ani da sauran littafin sanin addini saboda makarantar suna karatu sosai gashi ana zube kuɗaɗe masu tsoka a cikin ta.
Gwanin burge wa kowaccen su ta sha niƙab da Safa saboda bin ƙaidar dokar makarantar amma duk da haka LINA wata rana haka take shiga makarantar,ko yanzu ma bata ɗaura nata ba,ƙiri da muzu wai takura ta yake yi tun malamman basu fahimci halin ta ba har suka fahimci haka take idan suka ce su tilasta ta mata saka wa dole za,a samu matsala domin zata iya hinjire musu shi yasa suka saka mata ido sai gashi abun ya zame mata shan ruwan tsuntsaye wata rana ta saka wata rana ko ta ƙi sakawa.

Ya'u ne driven su shine mai haƙƙin kula da kai yaran islamiyya hakan ya sa ya ke shirin sa da wuri amma duk da haka sai sun ɓata ma kan su lokaci da shi.Yau dai Allah ya taimaka saboda kasancewar wanzuwar ya yan nasu hakan ya sa kowaccen su tayi shirin ta da wuri.Koda suka fito sun tarar da Hamrah,da Nina kowaccen su ta hakimce a kujera suna taɓa fira kaɗan kaɗan.
Cikin washe baki REENA ta ambaci sunayen su,suma haka cike da ƙuruciya suka amsa mata suna matsa mata space alamar ta shigo bayan kusa da su duk da motar irin mai seat da yawa ce prado new design.Da sauri kuwa ta shige tana zama tsakanin su.

Ita kuwa REENA bata cewa kowaccen su ƙala ba haka su ma sai ma wani haɗe rai da tayi tana bin su da Harara daga cikin niƙaf ɗin da ta saka yanzu,dan duka haushin su take ji akan su Yaya B ya taɓa tabkar ta.dan ko wancan zuwan na sa ya tabke ta akan Hamrah da ta zaga kafin kuma ta hau ruwan cikin ta tana ta nusa.ba,a ma zancen Nina da basa ga maciji dan itama fitinanniyar kan ta ce duk da wata rana tana shayin REENA dan ta taɓa cire mata haƙori a achan baya,Allah ya taimake ta lokacin suna fira ne.

Tana zama ya'u ya Kalle ta yana washe baki yana ɗan gyara sumar kan sa a madubi kasancewar sa saurayi mata shi ya furta " Yan matan Ummah yau waya taɓa mu " Dan shi dai haka kawai Allah ya ɗaura masa son REENA tana matuƙar burge shi yana son mace yar tujara,kamar ta.

Mugun kallo ta jefa masa kafin ta taɓe bakin ta ta mai da fuskar ta kan glass tana ƙarewa haɗaɗɗiyar estate ɗin ta su kallo da koda yaushe ƙara kyau take yi kamar kullum ake renovation nata.

Murmushi ya ƙara saki kafin ya furta "Allah ya huci zuciyar Hajiya ALINA SS ".

Murmushi ne ya suɓuce mata jin ya kira ta da sunan manya wanda ya sanya ta jin kanta yayi wani ƙato.
Sai dai bata kalli ko gefen da yake ba ta cigaba da kallon wajen.

Haka ya tada mota yabar estate ɗin bayan wangale masa ƙaton gate da aka yi.

Wani tunanin da ya shige sa ne ya san ya shi jan mugun tsaki yana bin motar da ƙwafa dan duk abinda ke faruwa a ciki Yana gani saboda ba tinted glass bane da motar ta su.Lallai dole ya taka wa wannan Drivern burki ya fara wuce gona da iri akan ƙannen na sa.
Shigewa yayi part ɗin da babu kowa a cikin sa sai kayan dake zube na alfarma a ciki da wani irin ƙamshi.
Da shigar sa ya nemi waje ya zauna yana sauke ajiyar zuciya,abubuwa da dama suna dawowa masa aƙwakwalwa hawaye ne masu zafi suka silalo masa kafin ya yi ƙarfin halin share su yana ambaton sunayen Ubangiji zuciyar sa na cigaba da ƙuna da raɗaɗi wanda ya daɗe yana dunƙula na rashi,shekara da shekaru a duk lokacin da ya tuno da abun da idanun sa suka gane ma sa sai yaji wata iriyar zafi ta mamaye zuciyar sa baida tabbacin abinda ya gani.Dan haka tsawon wannan shekarun ya rasa wazai tun kara da wannan maganar wa zai masa fashin baƙi akan ta.Sai dai kunya da nauyin maganar sun sa ya kasa iya kallon kowa da ita kuma ya hana zuciyar sa saka masa mugun dafi mai illa a tsakanin makusan tan sa.Kuka ne ya ƙwace masa mai zafi sai da yayi mai isar sa sannan ya miƙe ya shige wani haɗaɗɗen bedroom da yake ƙal ƙal saboda kullum cikin gyaran sa ake,saboda umurnin sa ne.
Kwanciya yayi akan gadon inda take bacci ya kwashe sa anan cike da tunani iri iri mai cike da mafarkayya masu daÉ—i da marasa daÉ—i.

Shine bai farka ba sai ana kiraye kirayen sallar la,asar a Babban Masallacin dake cikin estate É—in.
Miƙewa yayi da sauri ya faɗa toilet wanka ya ɗauro tare da alwallah sannan ya chanza kaya saboda yana da wasu sutura anan.Wani ƙaramin frame yayiwa kiss sannan ya fice zuwa masallacin da ke cikin estate ɗin ta su.

Bayan fitowar su Sallah kuwa sai Alokacin ya fara kame kame ganin yadda Mai gayya Alhaji Sada tsohon Arziki wanda dukiya ta ƙara wa tsufan sa kyau yake kallon sa yana taɓe baki.Kafun ya ɗauke kan sa daga idanun sa yana mayarwa kan Junaid da yake gayar da shi cike da girmamawa.
Murmushi ya ƙaƙalo dan ya san cewa yayi laifi tun safe ya shigo bai neme sa ba sai yanzu da sallah ta haɗa su.Babu ma.wanda yaje ya gayar a cikin iyayen na sa duk da ya san suna nan kuma yana da niyyar yin haka zuwa dare.
Junaid ma cike da farin ciki ya matsa kusa da É—an uwan na sa da ya lura da shi yanzu ya rungume sa yana masa sannu da zuwa kasancewar ya ga alamar sa a cikin estate É—in ga sojojin sa na birjik.

Waye Alhaji Sada Saleh( SS )

*TUSHE*
Chapter 15 · 0% Book details