← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 110

Sashe 24

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Kutumar Uban nan,Amina kunji wanki ".
Ta furta ganin yadda duk aka wanke musu jiki ita kaɗai ce ruwan bai sama ba.Amma taji kamar itace dan cike da masifa da ɓacin rai tayi zancen ganin ko ta kan su ba,a bi ba kamar ba mutane aka yiwa haka ba.

" Yau ko uban waye sai ya yi bayanin abun da ya aikata sai ya baku haƙuri ko shine ɗan gidan Shugaban ƙasar Nigeria,na rantse da Allah sai ya yi dana sanin zuwan sa ƙauyen nan,Amina kun jin yadda kuke wari wallahi haƙƙin ku ba zai ta fi banza ba sai ya san ya taɓa ƙawayen SHATOU ".

Sai dai bata rufe baki ba wata motar tayi mata wankan kwata a fuska sage hannuwan ta ta yayi tana runtse idanun ta cike da hargagi tana tofar da yawu take furta " Allah ya isan mu,Allah ya isan mu Azzalumai ɓarayi,masu kuɗin jini ".
Cikin dabara ta samu ta goge fuskar ta dake ta wari sauƙin ta ma basu kai cikin baki ba ruwan iyakar su akan leɓen ta. kafin ta yanka da gudu ta cimma asalin motar da ta watsa wa Su Amina kwata da tarin duwatsu a hannun ta da ta tsinta a yanzu cikin hasala da wani irin zafi da zuciyar ta ke na wulaƙanci da aka musu ba,a kuma tsaya aka basu haƙuri ba ......✍️

# MMG#
# SHATOU#
# IRO#
# LINA SSS#
# REENA SSS#
# BILAL SSS#
# SAMIRA MAI BILLIONS.

Wannan littafi na kuÉ—i ne.akan farashin 1000

Page ɗaya ya rage a free pages da na muku alƙawari dan haka duk wadda ta shirya yin payment ga details a ƙasa.👇
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Idan ba shaida kika tura ba kar kimini wani zance pls serious one nake buƙata,ga komai nan a sama na ajiye muku.

Last free page on Monday.

Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh 💞

*_Typing_*

*💋KURMAN ƘADDARA💋*

*©®Faiza Almustapha Murai*

*FA'EEH BG*✍️

*BOOK ONE*

__Paid__

*_Last free pages👌_*

P..1️⃣2️⃣

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Posting room link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn

*LITAFFAN MARUBUCIYA*
*A MAFARKI NA SANTA*
*RAYUWAR MU A YAU!*

_*Ina yan kasuwa Manyan Hajiyoyi masu Capacity ga damar ku tazo domin kuwa muna tallata muku hajar ku a farashi mai sauƙi idan ki/ka na buƙata,sai ku tuntuɓe mu wannan lambar +234 808 750 4734 dan tallata hajarku.Sai mun ji ku.*_

✨🕳️💦🕳️💦✨

Cike da masifa ta fara ƙoƙarin jifar motar sai dai bata kai ga yin jifar ba aka daka mata tsawa inji ɗai daga cikin garda garda dan masu tsaron sa dake tare da shi wanda suka diro daga kan buɗaɗiyar motar su su biyu kasancewar sun hango abun da take shirin yi.
Zare mata idanu suka yi suna jifar ta da mugun kallo.

" Hey girl what are you up to ? "

Wani daga cikin su ne yayi tambayar yana kallon hannayen ta da suke rawa jiran take ta samu dama ta jefi motar yadda zata yiwa na ciki rauni.

Aiko cike da rashin tsoro itama zaro idanun ta dan bata fahimci abunda ya faɗa ba.Hararar su ta dinga yi ɗaya bayan ɗaya kafin ta faki idanun su ta yanka a guje ganin haka ya sa suka bi bayan ta tana isa dai dai ta wajajen motar ta ja baya ta saita danƙon kafin ta saki dutsen na ta da ta saka a kan danƙon da ta fito dashi a ɓoye wanda ita kan ta bata san dalilin da yasa ta ɗauko shi ba ta saka aljihun.Sai yanzu.

Tasss haka glass ɗin ya bada ƙarar tsagewa saboda yadda dutsen ya dake sa na farko kafin na biyu ya ƙara hawa kan sa sai da tayi harbi uku sannan taga ta tarwatsa glass ɗin ta dakata ganin sun kusa isowa wajen ta dan ta musu nisa.
Dariyar farin ciki ta kece da ita cike da jin daɗi dan ba haka ta so ba ma so tayi ta ta zubar da shi duka ta ga asalin ɗan ikon da ke ciki zaune wanda da alama babba ne dan ta ga yadda ake ƙoƙarin kare sa tun da ga waɗan chan gardawan.

Motocin chak suka tsaya dai dai saitin ta kasancewar umurnin da suka samu na dakatawa.
Dai dai lokacin su Amina sun ƙaraso cike da tsoro sai zare ido suke yi ganin abun da ta aikata dan su kan su basu san ta fito da danƙo ba.Tun da gardawan nan suka biyo ta.

Ƙoƙarin kama ta bodyguard ɗin suke yi dan hasale suke sai dai maimakon ta gudu sai ma riƙe ƙugu da tayi tana jifar su da kallon banza cike da masifa ɗayan ya ɗaga hannu yana batun kai ma ta mari sai dai ƙamshin turaren sa da yaji a akusa da su ne ya sa shi dakatawa yana kallon sa cike da mamakin uban gidan na su dan bai ma san fitowar sa ba.

Itako SHATOU bata juya ba sai ma rufe idanun ta da tayi tana jiran saukar marin da take ganin idan aka yi shi sai kowa ya mutu cikin su saboda yadda zata addabi rayuwar su.Duk da taji ƙamshin wajen ya sauya da wani daddaɗan ƙamshi hakan bai sa ta yi ƙoƙarin juyowar ba still sai ma buɗe ƙofofin Hancin ta da tayi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin tana jin ta kamar ta faɗa wata duniyar dan take taji bacci na son ƙwace mata ta gurin.

Sanyayyiyar Muryar sa ce mai cike da Izza ta daki zuciyar ta yana furta " Bike Stop this She's young ".Yayi zancen yana ƙare mata kallo ta ƙasan ido cike da mamakin rigimar ta ta dan tun farkon fara rigimar yake ɗan hango su ta madubi.

Dai dai lokacin ne kuma ta buÉ—e idanun ta tar akan sa kasancewar ya dawo gaban ta yanzu.

Ƙirjin ta ne yayi muguwar faɗuwa ganin mutumen dake gaban ta Bature sak har wani kashe ido yake yi yana sanye da baƙin yadi mai taushi sai dai babu hula akan kwantaccen gashin sa da ya sauka har akan wuyan sa.Kyakkyawa ne fari mai ɗan jiki kaɗan bai wani tara irin muscles ɗin nan ba dan da alama yanzu yake tashe yaro ne shakaf wanda ba zai wuce Shekara ishirin ba da uku a duniya.
Yana da tsawo sosai da faffaɗan ƙirji,Kyakkyawa ne dai na asali,Irin asalin kyawon nan na turawa masu kyau da suka samu surki da fulanin mu,Yana ɗauke da manyan idanu masu haske da gashin gyara wanda yake cike tabb akan gyaran sa ga dogon Hancin sa da ya ƙara ƙawata Kyakkyawar fuskar sa bakin sa na ɗauke da red lips masu kyau da suka ƙawata ƙaramin bakin sa.Sai da ta gama ƙare masa kallo sannan ta sauke numfashi dan ya ɗan bata Tsoro,ganin sa take kamar ba mutun ba,Samun kan ta,tayi da galla masa harara bayan haɗa idon da suka yi yanzu tuno da shine cikin motar da ta yiwa su Amina wankan kwata.

Masifar ta ce ta dawo sabuwa inda ta fara girgije girgije kamar wadda ke ɗauke da wani abu aƙirjin ta tana furta " Wallahi sai kun ba su haƙuri sannan zan haƙura na bar ku ku wuce ko na ƙara sa fasa muku glass ".

Idanun sa ya lumshe a hankali yana É—auke idanun sa a kan ta dan tsafff yake kallon ta ta gefen ido yana kallon duk abun da take yi.

" Is that all " ?

Ya yi tambayar yana ya mutsa kyakkyawar fuskar sa da rana take ƙarawa haske gashi ranar ma ta ishe sa dan haka yake son su gama abun da ya kawo su subar garin dan tun asali bai yi niyyar zuwa ba Aka tilas ta masa.

SHATOU da bata fahimci komai ba ta cigaba da faɗan ta tana furta " Babu ruwa na ko turawan duniya zaka tara nan,kai ko mamamar ka elibabeth da donath trup wallahi sai kun bamu haƙuri babu ruwan mu da masu jajayen kunnuwa ".

Yanzu kam ido cikin ido yake kallon bakin ta da ke zaro zancen kafin ya koma kan kyakkyawar fuskar ta,ta ƙuruciya da take fitar da wani haske fess.Kalmomin ta sun so saka shi dariya amma shi ba ma,abocin dariya bane dan haka yadda ta ambaci su Elizabeth da donald trump suka sa shi ɗan lumshe idanun sa dan sun bashi dariya matuƙa,sai dai babu dariyar.

Hangame baki tayi tana kallon sa yadda zararan eyelashes É—in sa suka kwanta akan fatar idanun sa,gashi taga kamar fuskar ta sake ba zata iya kiran abun da yayi da murmushi ba ko wani abu daban.
Ƙirjin ta ne ya ƙara bugawa haɗa idon da suka yi ayanzu karo na biyu kai ta sauke ƙasa jin ƙafafuwan ta sun sanyi.
Lemar da aka lulluɓe sa da ita har ta shiga ciki ce ta kalla kafin ta kalli ƙafafun sa dake sanye da sandals na maza masu shegen kyau da ɗaukar ido da suka ƙara haska farar fatar ta sa saboda suma black ne.Mere bakin ta tayi ganin ƙafafun na sa da ko ita da take mace nata basu kamo na sa haske da tsafta ba cikin zuciyar ta kuwa mai bilicin kawai ta furta sai dai bata san cewa zancen ya fito fili ba
Kawai ta tsinkayi Muryar sa yana furta " Hey bana bilicin,Amma ke kin yi kama da su ai".

Ya kai ƙarshen zancen yana sauke numfashi saboda bai cika magana sosai ba hasalima bai cika yin ta da cikakkiyar Hausar mu ba amma yau an saka shi dole.
Ido ta waro cike da masifa kafin hawaye ya wanke mata fuska duk da mamakin jin Hausa a bakin sa " Wallahi bana bilicin nima,Allah ya isa na duk wanda ya ƙara ce mini ina kama da masu bilicin ".
Bai ce mata ƙala ba sai ƙara lumshe idanun sa da yayi yana ja baya ya bar ta cikin rana dan lemar sa tayi mata rumfar dai dai itama.
Chapter 24 · 0% Book details