← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 110

Sashe 54

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Koda ya fito duk suna nan zaune suna kallo wanda an kwata faɗa yayi kusan sau biyar Hajiya na tare wa ta raba.Haka Samir koda ya fito cikin shirin sa na kaya marasa nauyi ya same su Leena sai aikawa Reena harara take yi kamar idanun ta zasu zube murmushi kawai yayi ya ƙaraso wajen yana furta "Take it easy My Baby ".Kunya ta ji dan haka ta sauke kan ta ƙasa tana Murmushi shi shiko Dariya yayi kafin ya miƙar da ita tsaye haka ma reeena da Ninah suna dariya.Yadda ya tallabo kamar wasu yan teddies.Tare suka isa bakin dinning da dama An riga an shirya sa shi kaɗai ake jira dukkanin su ka zazzauna har su Ayman da ake firar da su dan sun riga shi ma fitowa.Cike da sakewa su Leena da aka zubawa ko wacce nata suka fara cin abincin hankali kwance.Sai dai Leena ko rabi ba tayi ba ta koma kusa da Samir wai na shi take son ci babu musu kuwa yana murmushi yace ta wanke hannun ta da gudu kuwa ta wanke hannun a nan cikin robar da aka ajiye ta wanke hannun saboda Samir da yake cin abinci da hannu a mafi yawan lokuttaa yanzu hakan ma shine kawai ke cin abincin sa da hannu hankali kwance.
Cike da murna ta zauna suna cin abincin tana kallon sa tana Murmushi shima murmushin yake yi Reena dai bata tanka mata ba sai cin abincin ta take yi a haka suka yi ta shirita wajen cin abincin kafin suka koma Falo su Abduljabbar da Ayman Sai tsokanar ta suke yi ta yiwa Hajiya ya ji yau tunda Samir ya dawo ta zo harda zama, idan ba ya nan kuwa gaisuwa kawai ke kawo ta,ko ita ba kullum ba Haka suka zauna suna ta fira suna bashi labari yana kwasar dariya dan harda labarin islamiyya aka taɓo masa harda dukan da Ustaz Babba ya yi mata ta bashi labari tana dariya tana nuna yadda wai cikin ustaz Babba yake motsawa idan ya ɗaga bulala.sai da ya gama cin dariya sannan ya ce " Yanzu Leena Uztaz Babba mai makaranta gaba ɗaya shine kike kwaikwayo "?
Dariya tayi itama kafin ta ce " To Ai shi ya dake ni yaya ai da faÉ—a kawai yayi mini kamar yadda kai da su Ummah kuke mini ".
Ta kai ƙarshen maganar tana turo ɗan ƙaramin bakin ta gaba.
Dariya yayi kafin yace " Gaskiya ba,a.kyauta mini ba an sako mini Baby gaba ".
" Ai wallahi yaya wannan da kake gani sai dai Allah ya shirya shekaranjiya fa wani ta gani yana jan wata mota mai kuka kamar mataccen injin kawai ta saka mishi dariya tun bai gane da shi take ba har ya gane,haka fa ta tura kan ta a glass tana kwasar masa dariya,shi ko fahimtar da shi take ya hau zagi harda kira ma Su Abba ɓarayin gwamnati ".
Ayman ne yayi zancen.
Dariya Ce ta kama Samir kafin ya ce " ohh ina kuka je hala ?"
" Mun je aikar Sir Ni da ya'ya Abdul Shine fa kafin mu fice ta ganmu ta ƙalla sau ta tace sai ta bimu,muka ce ba zamu je da ita sai kuka,sai aka sa,a Dada ya fito ya motsa jiki shine ya saka mu dole muka fita da ita aiko munyi dana sani dan mutumin nan ya ji haushi sosai yana fama da kan sa shi kaɗai ya san halin da yake ciki amma yarinyar nan saboda rashin ta ido ta fara sakar mai dariya tana nuna yadda motar ke rawa " .
Har Hajiya da bata wani shiga firar ba bayan zaman ta wajen yanzu dariya tayi tana furtawa A ranta Allah ya shirye ku Albasa bata yi halin ruwa ba Leena mahaifiyar ku mutuniyar kirki koda yake ba haushe yace kana haihuwar ɗane baka haifi halin sa ba addu,a ta cigaba binsu da ita duk su duka tana rokon Allah ya ƙara shirya musu zuri,ar su.
Samir bayan ya tsagaita da dariyar sa ne ya kalli Leena da ta haɗe rai tuno yadda Ayman ya janyo ta ya rufe glass kafin ya balbale ta da faɗa dan haka tun da suka yi mata haka dan shima Abduljabbar ya taɓa faɗan ta rufe komai.
Hannayen ta ya riƙo kafin ya kalli fuskar ta yana jan kumatun ta take kuwa ta washe baki tana dariya kamar Ba ita ba dan tana mugun shiri da Samir sosai idan ka ga dariyar ta da ya Samir ne a irin mabanbanta lokuttan.
Ƙarar wayar shi ce ta sanya shi dakatawa yana kai duban sa ga screen murmushi ya saki kafin ya ɗaga kiran.
Da sallama É—auke a bakin sa ya É—aga tsadaddiyar wayar ta sa ya saita a kunne.
Daga chan ɓangaren Amsawa aka yi kafin cike da barkwaci ya ce " Allah ya taimaki soja ni na 'isa " " ai Reena mutuniyar kirki ce gasu nan ma kusa muna fira ,kuma an kawo mini ƙarar ka daga jarumar gidan nan ".
Ban san abinda aka faɗa masa ta chan ɓangaren ba naga ya saki murmushi yana shafa kai kafin ya kalli Leena ya ce " Mu dai Dan Allah kar a ƙara taɓa mu kaga ka sa ka mu fushin ka da yawa "
Fahimtar da wa ake yin waya hakan ya sa Leena ɓata fuska sai hawaye kafin ta miƙe tana shirin fita daga part ɗin gaba ɗaya hannun ta ya riƙe da sauri yana girgiza mata kai.Kafin ya kafa mata wayar a kunne.
" Kin gama fushin,ko da saura na ƙara miki lokaci " ?
Shiru tayi tana haÉ—iye kukan ta jin yadda yayi magana cikin kakkausar muryan sa da babu wasa a cikin ta kafin ta ce komai ta kara tsinkayar Muryan sa yana cewa " Sakaryan yarinya kawai,Mara hankali,zanyi maganin ki duk abun da ke kan ki sai na cire Miki shi mark my word " kafin ya ja karamin tsaki yana kashe kiran .
Ai Leena bata san ta saki wayar ba tana ɓarkewa da kuka kafin ta kai ƙasa harda murje murje kamar yar shekara huɗu.Kan ta suka yi ganin abun na ta kamar mai Aljannu dan ta birkice dagaske hankalin su ne ya ɗaga jin tana kuka kamar ranta zai fita,sai an samu ta rage sautin kukan bayan ya dago ta ya rungume ta kaɗan sai kuma da ta tuna kalaman sa sai ta ji wani irin baƙin ciki tana ji ina ma ba Ya Bilal Bane ta masa rashin mutunci kuka tayi mai isar ta ana Rarrashin ta.Shiko Samir hankalin shi duk ya ta shi dan haka ya ce " B da yace zai bada haƙuri ashe wata rigimar zai tsokano mana ya bar mu da rigima ".
" Cewa fa yayi na baki ya rarrrashe ki ya baki hakuri ".
" To ba ce min yayi Sakarya ba kuma wai duk abin d ke kaina sai ya cire mini,kenan yana nufin ina da aljanu Ni wallahi lafiya lau nake,wai sai yayi ta haɗa Ni da Aljannu " ta ƙara fashe wa da kuka cike da sangarta itama Reena ganin kukan Leena abun ka da ɗan uwa tuni ta fara tsiyayayar da hawaye itama kafin ta ɓarke da kukan haka suka jeru su biyu Ninah babu batun dariya ga abun dariya dan haka ta zuba musu ido kawai kamar ta samu tv.
" A yafe ma yya B kinjin my baby shi fa big brother ne duk abinda yakeyi saboda ke ne da samun kammaluwar ki,You should not be like that hakuri zaki yi kinji Babyn SS kin san Ya ce ke ce matar ta sa Farko ba Hajo ba " Cike da barkwanci Samir ya kai maganar ƙarshe.Dariya duk suka sanya kafin suka tsinkayo Muryan ta tana shesshekar kuka bayan gama yar dariyar da tayi yanzu tana cewa bata son Sir ya mata tsufa " Ya Samir fa harda mara hankali ya kira mini wallahi kuma Ni ba mahaukaciya bace ai dai ka sani ko " Kai ya ɗaga mata kawai har ta gama maganar ta yana murmushi ganin hawaye sun ƙara silalo mata hakan ya sa ya ƙara janyo ta jikin shi ya yi wiping tears ɗin.Yana furtawa common is ok chill up my baby a hankali.
Su ko Su Abduljabbar da Ayman yar dariya kawai suke yi wa Reena da ta lafe gefen sa itama idanu sun yi jazir wanda har yanzu idanun ta hawaye suke yi sai dai basu kai na Leena ba.Ta tsani ganin yar uwar ta cikin damuwa ko ƙalilan ta dan haka kukan ta bai da wahala akan abun da ya shafi Leena ɗin.
A haka suna nan aka kira Sallan azahar dan haka suka miƙe kowa yayi wajen Sallah ,Su ko Su Leena Sashen Ummah suka koma da niyyar zasu dawo haka ma Ninah tare suka fice tayi na su sashen.
Chapter 54 · 0% Book details