← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 110

Sashe 83

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shatou ta bata amsa tana cunno baki gaba.
Kai maman Jawairiyya ta gyaɗa bata ƙara cewa komai ba dan dama ita bata tauye yar ta abu ɗaya ne bata so shine ta yowar dare,dan ma dai kawai ta san dalilin da ya sa Inna ni take yi wa Shatou katange ya sa yanzu tayi mamakin fitowar Shatou haka da wuri dan haka ta shanye mamakin ta da amsar da shatoun ta bata.
A haka suka shirya cike da murna da sakewar da shatou tayi haka suka fice da Jawairiyya daga gidan, gidansu Amina suka wuce nan ma maman ta sai da ta magantu amsa É—aya ta bata itama dan haka itama Amina da take cike da tunanin shatoun ta yi ta murna maman ta kuwa abun har mamaki ya yi ta bata dan da ta dawo harda kuka tayi mata na yadda Shatou ta share su sai gata kuma ishain farin ta zo da sakin fuskar ta kamar ba ita ba.
Suna fita suka yi gidan su Ramata chan ma basu jimaba sun same ta har sun gama sallah dan haka a take su ka yi dandali su hudun su a jere suna wasannin su har suka isa duk da suna É—an shakkun Shatou É—in amma sun sake ganin yadda ta wartsake musu kamar ba ita ba.
Sune farkon wayen da suka buÉ—a dandalin yau dan haka suka samu waje suka zauna suna yan wasannin su na hannaye a haka wajen ya fara cika da jama'a yan yara matasa irin su kafin suma Mazan su fara zagaye wajen suna zama akan É—an dakali da ke wajen wasu akan kara wasu jingine a kan bangon dake kusa da wajen na tsohon gidan mai gari.
Waje na cika dan har su iro sun cika wajen suka fara wasannin su cike da nishaÉ—i da burgewa.
Ita da Nazihwa kamar ba su yi faɗa ba suka sake ma juna aka cigaba da wasa sai dai shi Shamsu fa ya riga ya ƙullaci Shatou da gaske dan haka ya ke Binta da ido duk motsin ta yana kallo dan yau ya sha alwashin sai yayi maganin ta cikin daren nan dan bata isa ta taɓa masa Nazihwa ba ya ƙyale.Shi ko Iro ganin an ɗan kwana ya sa ya share da zancen Shamsu dan tunanin sa ya bar maganar duk da ya san halin sa mugun mutum ne Shamsu ko tsakanin su ta haɗa su sai anyi da ƙyar yake saki maye ne ɗan Bala'i dan sun tabbatar da ace Shamsu maye ne duk wanda ya kama sai buzun sa.
A haka suka yi wasannin su cikin sakewa cikin ikon Allah yau har an ka gama ba,ayi rigima da kowa ba an wanye lafiya.
Suna gamawa kowaccen su ta kama hanyar gida Iro hankalin sa ya ɗauku saboda wata gardama da suke yi a tsakanin su har Shatou da yake ta bi da ido ta bar wajen bai lura ba, yau ba ma hanya ɗaya suka bi da su Amina ba kowa ta sa ya kama dan haka tafe take tana juya ɗan karen dawar ta,da ta samo a wajen dandalin tana yan waƙe waƙen ta.Sai dai Turus ta ja ta tsaya ganin mutun gaban ta kamar an jeho sa.
Wata irin ƙatuwar sanda dake hannun sa ta tsirawa ido kafin ta kai kallon ta kan fuskar sa da take babu annuri ko magana bai yi ba ya ɗaga ƙatuwar sandar yana neman Kaita jikin Shatou wadda ta waro idanun ta da ƙarfi ganin da Dagske a jikin ta zata sauka ga wani tsoro da ya saukar mata ganin bata da mace ci sai Allah bata kuma da abun kare kan ta sai dai ba zaka taɓa gane cewa a tsorace take ba ta shanye harda riƙe ƙugu irin in ka isa ka taɓa ni,ai kuwa akan ta ya sauke sandar da wani irin ƙarfi sai dai wani abu ta ji ya tokare mata akai sandar bai sauka akan ta ba hakan ya sanya ta buɗe idanun ta da ta rufe ruff tana jiran tsintar kan ta wata duniyar mai cike da wahala.
Iro ne ta gani gaban ta yana zare ido cikin ɗan hasken farin watan da ke zagaye da su ga hannun sa ɗaya akan ta riƙe katuwar sandar Shamsu da ya fara kiciniyar sai ya sauke ta jikin Shatou ɗin ran sa ɓace dambe ne ya kachame tsakanin su ita kuwa Shatou cike da mamakin yadda akayi Iro ya san ta nan ta biyo ta matsa baya tana haɗiye tsoron ta tare da ɗan jin sanyi a ranta na zuwan Iron dan ta san da yau sai su Baffa na sun yi kukan rasa ta.
Ganin yadda dambe ya kachame tsakanin su hakan ya sa da baya baya ta fara tafiya kafin ta ɗaga ƙafa ta yanka a Guje tana ɗan waigen su.
Su ko su Iro abokan sa ne da suka biyo bayan sa suka raba faɗan dan dama wani daga cikin su ne da bai je da wuri ba ya sanar da Iro ya ga shatou a wannan hanyar da zai taho nan dan haka ya biyo bayan ta sai sai dai kuma ya tarar da shamu ya tare ta yana batun mata illa dan ya san ya aje wannan sandar ta sa jikin shatoun sa sai ya mata illa ƙila ma ya karya mata ƙashin baya.
Da ƙyar suka raba faɗan abun ka ga ƙarfi da ƙarfi sai da suka yi da ƙyar suka raba dan kowannen su yaji jiki babu wanda yake baya wajen ƙarfi da rigima.
Gida suka wuce da Iro sai dai ya zille sai bin bayan Shatou da yayi yana huci.
Sai dai har ya kusa isa gidan su bai ga mai kama da ita ba dan haka ya tabbatar cewa ta isa gida lafiya.Sannan ya wuce gida yana jin yar natsuwa na saukar masa.
Shiko Shamsu wata sabuwar gobarar ƙiyayyar Shatou ce ta ƙara ruruwa a cikin zuciyar sa nan yayi ta shan alwashin illa ta ta, ta hanya da ban da ban.Sai da ya zage ta tass ita da Iro kafin ya wuce gida yana ƙara jin zafin ta har Iron musamman ganin bakin san ya fashe dan ya shafo jini ga shi yana jin zugi kaɗan kaɗan.

A ɓangaren shatou kuwa a Guje ta faɗa gidan Baffa na da ke zaune yana duba wasu littafan sa dan jiran Dawowar ta saboda hankalin sa da ya ƙi kwanciya ya ɗaga ido ya Kalle ta dan abinda Inna ni tayi bai masa daɗi ba amma ya san tana da dalilin barin ta fita gashi ba ta ma san rigimar da aka yi shekaranjiya ba.Dan ya san da ta sani da ba zata barta ta fita ba gashi shi da na shi dalili mai ƙarfi da bai son yawan fitar ta ta dan haka ya ke ƙoƙarin saka mata ido akan komai da take yi.
Inna ni da ta fito wanke hannu kasancewar tana ɗakin ta ne ta ɗauke kallon ta daga kan Shatou da ta gama ƙare ma kallo wadda ke ta sauke numfashi daga inda take tsaye.
Sai kuma a hankali kamar wadda aka matsi bakin ta,ta ce " Lafiya kika faɗo haka babu sallama ".?Ta yi mata tambayar ba tare da ta kalli ƙwayar idon ta ba.

" Inna ni faÉ—a fa ake yi da Iro da Shamsun mai guru ".

Sai da ta yi zancen sannan ta rufe bakin ta tana zare ido dan ta san dole za,a tambaye ta dalilin faÉ—an na su wanda dole zata ce itace sila gashi Inna ni bata san farkon rigimar ba,haka ma Baffa na wanda bata san ya san komai ba.
Hmmm kawai Inna ni tayi kamin ta ce.

" Ki wuce ki kwanta ki tabbatar kinyi addu'a kafin ki kwanta,abincin ki na nan ki tabbata kin ci ".

Kai ta gyaÉ—awa Inna ni kafin ta wuce sum sum alamar rashin gaskiya.Inna ni idanu kawai ta bi ta da su tana girgiza kan ta haka ma Baffa na ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani tunani akan wannan rigimar na É—arsar masa.A haka ya gama duba littafin na sa ya shige bayan sun yi sallama da shatou da ta masa sai da safe haka ma Inna ni dan Bibu yayi baccin sa tuni tunda suka dawo ya ji labarin shatou ta fice kuma ta ce ta yau bazata je da shi ba yayi alwallah ya shigewar sa yayi baccin sa hankali kwance bayan ya ci abincin daren sa.
Miƙewa Baffa na yayi ya saya gidan kamin ya shige shima.
Sai da yayi ta juye juye kamin bacci ya kwashe sa, ya daɗe yana tubka da warwarar yadda zai yi da rigimar da ta shiga tsakanin Shatou da shamsu sauƙin ta ma ta samu mai tare mata duk da bai son wannan shisshigin na Iro amma yakan ji daɗi da kariyar da yake bata.
Inna ni yau ma ta daÉ—e zaune kafin ta kashe haske ta kwanta bayan ta yi addu'a cikin yardan Ubangiji kuwa bacci ya kwashe ta mai daÉ—i sai dai bacci ne mai cike da mafarkai.
A ɓangaren shatou kuwa bayan ta gama cin abincin ta,wanda ta ci kadan ta sha ruwa,ta kwanta,ta daɗe tana tunanin wannan ƙarfin hali na Iro duk da ta ji daɗin yadda ya shige mata faɗan matuƙa dan ta san ko giyan wake ta sha bazata iya dambe da Shamsu ba.
A haka cikin tunanin bacci mai nauyi ya kwashe ta kasancewar tayi Addu'an kwanciya bacci.
Chapter 83 · 0% Book details