← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 110

Sashe 43

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kafin gurin ƙara riƙe wuƙar da kyau ta yanke hannun ta.Jini yana ɗai daga cikin abinda yake bugar da ita a duk lokacin da ta gan shi yana zuba haka da sauri idan an samu ozzz sai kan ta yayi ta sarawa ko a cikin haukar take ta asali ko sama sama.Dan haka cikin abun da bai fi secconi ba sai gata ƙasa luuuu.Da sauri Rayyan ya taro ta yana ƙwala kiran sunan ta cike da tausayi ƙanwar ta su.Hawaye ne suka wanke masa fuska ganin yadda jinin yake zuba wani ƙaton ɗan kwalin Nana da yake yashe gefe ya yajawo ya ɗaure mata hannun sai dai babu sauƙi dan haka babu wani kuzuri jikin sa jin kamar bata numfashi.Sun kasa saboda ciwon MA'ISHA sun kasa aminta bata taɓa samun lafiya, kasancewar ba,a san dalilin ciwon ba har yanzu bare a yi maganin sa.
Da ita ya faÉ—o Babban falon Amoh yana share zufan da take keto masa.
Da Suhaila ya fara cin karo wadda ta fito É—aukar wani abu ta saka ma cikin ta dan bata da jimirin yunwa tun fil azal.
Ƙara ta saki mai tada hankalin mai hankali kafin ta sulale wannan ƙarar kuwa itace ta ankarar da Amoh da Alhaji Sardauna.Wanda suke kira Dady.

ALHAJI IDRIS SARDAUNA.
Shine cikakken sunan Dady,ana kiran sa Hon Sardauna daga abokan aikin s,da kuma wajen gari,Saboda kasancewar sa Minister mai kula da har kar Noma,a gida ya'yan sa suna kiran sa Dady,Amoh Cikakken sunan ta Amina yara da dangin ta suna kiran ta da Amoh.
Amoh nada yaya Biyar Babba shine Suhail sai mai bi masa Suhaila,sai kuma Rayyan sai Kuma ƙaramar su MA'ISHA Wadda suke yiwa wani irin mugun so sai dai lalura ta musu shamaki sai dai duk da hakan suna iya kar ƙoƙarin su na bata kulawa yadda ya dace yadda bazata cutu ba bare ta cutar da wani,Amoh ko da yaushe cikin kukan zuci take na damuwa da ɗimuwa yanayin da yar ta ke ciki.Haka Dady kowa dake gidan yana ji da MA'ISHA sosai.Dukkanin Wannan a hali suna zaune ne A buja a cikin Ministers estate inda su MAHAJ suke.Suhail yana da ya kammala degree ɗin sa a fannin likitanci tun shekarar da ta gaba ta wanda Bama aƙasar nan yayi karatun ba,Yanzu yana aiki a wata Babbar private hospital dake nan Abuja, Suhaila kuwa yanzu take kusan kammala degree ɗin na farko,Sai Rayyan shi yana ug 2 ne a jami'a tare yake da Suhaila a school ɗaya,MA'ISHA ba,a ma zancen ta dan bata samu ilmi ba saboda yanayin ciwon ta ko school ba,a saka ta ba,saboda yadda abun ya taɓa ta dan tun tana ƙarama take da abun kamar yadda muka sani tun farko.Dan haka kowannen su yake jin mugun tausayin ta.Duk da haka kuma Suhail yana iya ƙoƙarin sa dan shi ya koyar da ita sign kamar na kurame kafin ta samu damar iya yin magana dan wasu lokuttan har bakin na ta bai iya yin magana,Kuma yayi ƙoƙarin sanya mata Abcd sai dai ba lallai yanzu ta iya kawo su ba.Su Suhail sun taso cikin Gata kamar yadda iyayen na su ke ƙokarin faranta musu,da basu tarbiyya gwargwadon ta Addinin Musulunci...
Da wani mugun sauri suka sauko daga benen kowannen su fuskar sa cike da tashin hankali babu ma kamar Amoh da duk guiwowin ta sun Sage saboda tashin hankalin abun da ta hango dan kuwa Kuka Rayyan yake yi kamar ƙaramin yaro ya kasa yin komai ga Suhaila kwance ƙasa a sume ga kuma hannun MA'ISHA na reto alamar babu rayuwa a jikin ta.Daddy Ma koda ya iso wajen hankalin sa yayi matuƙar ɗagawa da abinda idanun sa suke gane masa dan ga alama ta bayyana babu lafiya dan ko ina na jikin ta jini ne wani wajen shatin kwalba sai inda yafi tada musu da hankali inda ta yanke dan ɗan kwalin da ya ɗaure ne yake ta tsiyayar da jini saboda yadda ya tsuma.
Daddy bai tsaya wata wasa ba ya zari car keys dama a shirye yake da Jallabiya jikin sa saboda basu jima da dawowa daga masallaci ba.
Hannun Rayyan ya karɓe ta da sauri dan shi kamar ya zama hoto haka ya koma sai dai ya kalli MA'ISHA ya kalli Suhaila ya ƙara ɓarkewa da kuka.
Bayan Daddy ya bi da kallo yana ɗan dawo wa hayyacin sa ganin Suhaila da Amoh ta watsawa ruwa ta dawo dai dai tana sauke numfashi kafin ta ɓarke da wani irin kuka mai ban tausayi da katse zuciya.
Riƙota Amoh tayi kafin ta taimaka mata ta zauna sannan ta juya da sauri ta koma sama ta ɗauke hijab Babba ta ɗaura akan kayan Kwanan dake jikin ta.
Shafa bayan Suhaila tayi da ta rafka ta gumi kafin ta fice sai dai bata karasa ficewa ba sai ga Rayyan ya dawo yana furta " Amoh Nana,aje duba halin da take ciki ".Cikin sauri Amoh ta juya ta koma zuwa ɗakin a sume ta isko Nana da ta yi zaton kwanan ta sun ƙare.Ruwa ta Yayyafa mata bayan ta kunna hasken ɗakin kan ta ta dafe da wani irin sauri da ya sara mata saboda ganin yadda komai ya koma upside down.Hawaye ne ta ji sun silalo mata.Ta sanya Nana ta kwashe Kayan kwalaben nan, amma bata san yadda ake dawo da su ba dan toilet ko cikin lockers nan aka ce a mayar da su saboda yadda zasu iya zama illa a gare ta.Saboda sun lura idan so ɗari za,a cika madubin sai ta hargitsa komai kuma hakan bai taɓa damun su ba sai ma ƙara son ganin sun gyara rayuwar yar su.
Tuno yadda ta ga kwalabe duk sun soke ta hakan ya sa ta runtse idanun ta da ƙarfi tana share wani hawayen da ya zubo mata mai zafi.Wani rauni ne ya ƙara bayyanar mata ta san muddin da ace Suhail yana nan sai ya fi kowa shiga tashin hankali dan haka ba zata bari ya san da zancen ba,saboda duk yafi shaƙuwa da Ishaan ta.
Dan haka ta sauke ajiyar zuciya bayan dawowar Nana cikin hankalin ta tana ta sauke numfashi tana jan Ajiyar zuciya.

Nana kuwa a tsorace ta miƙe tana neman guduwa tana cewa " Dan Allah MA'ISHA ki min rai bani bace wadda kike nema,bani ce ba kar ki kashe ni "...Ta kai ƙarshen zancen tana ɓarkewa da kuka bayan Amoh ta janyo ta tana bubbuga bayan ta.
Kafin tace. " me kike nufi da bake bace wadda take nema "?

" Ta ambaci sunan wani ne hala "

" Ehh kamar haka "

Nana ta bawa Amoh amsa jikin ta na rawa saboda tsoro tana mugun tsoron yanayin MA'ISHA sai dai tana kaunar ta matuƙa Allah ya ɗaura mata son ta,dan haka ko ta so ta ajiye aikin sai ta kasa dan haka take kula da MA'ISHA da zuciya ɗaya cike da so da ƙauna kuma ba yaune ta fara yi mata irin hak baa,sai dai na yau ya bata tsoro ganin ta da yuƙa sabuwa.
" Tou Ikon Allah Sunan wa kika ji ta kira Nana " ???✍️✍️

# Wannan labari na kuÉ—i ne #800

# _FA'EEH BG CE✍️_

Book one free
Book two paid#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haÉ—a document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞

Like,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔

_*💋KURMAN ƘADDARA💋*_

_©®Faiza Almustapha Murai_

_FA'EEH BG✍️_

P_____2️⃣2️⃣

*BOOK ONE*
_FREE._

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*
Chapter 43 · 0% Book details