← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 110

Sashe 4

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Baffa na dake É—akin sa ya fito haka ma Inna ni da sauri ta fito nata É—akin dama a tsame take hankalin ta na kan Shatun ta.
Jikin ta na bata sai ta zo musu da wata rigimar.

" Na rantse da Allah sai na kakkarya Shatu kosongo shegiya mara tarbiyya "
Laƙanin da wasu daga cikin mutanen ƙauyen suka mata kenan,kuma daga bakin Iro ya fito saboda guje gujen ta da Shegen gudun da Allah ya bata,sai suma mutanen gari suka ɗauka,A ɓoye Dan ya taɓa ganin wata dabba mai Shegen gudu mai suna kosongo shine ya kira sunan gaban abokan sa yana kaman ta Shatu dashi sai suka ɗauka suna kiran ta dashi.Amma saboda fitinar ta ba kowa ke iya kiran ta hakan ba saboda bata shiga sabgar kowa Shatu yarinya ce mai halin manya dan Shegen wayau ne da ita duk faɗan da ake mata tana takatsan tsan amma da zaran an Jata sai tace katt,musamman irin su Iro yan na iya.

" Iro ta ciza har sai da ta fasa shi yanzu haka yana chan hannun na sa yana zuza yana kuka, saboda ta saka masa mugayen haƙoran ta masu kama da na kura sun zabci naman daji har sun gaji wallahi sai na lallasa ta kafin ma mai gari ya yi maganin ta ko shi iro Ni zan yi " Ya kai ƙarshen zancen ganin Baffa na ya zuba masa idanun sa yana kallon sa cikin mamakin yadda yake zagin yar sa gaban sa babu kunya harda wani Shegen suna da suka mata wanda shi bai taɓa jin sa ba sai yau.
A jiyar zuciya Baffa na ya sauke kafin ya ja numfashi Yace " Zaidu a riƙa tausasa harshe koba komai Ni mahaifin Shatu ne ba komai ya kamata ka faɗa a gaba na ba,kuma na san Shatu na bazata iya aikata abin da ka faɗa ba ba tare da an tsokane ta ba wannan halin ta ne na sani,Dan haka ba zan gaji da bada haƙuri ba kamar ranar ayi mata haƙuri yarinta ce ke damun ta duka duka Shatu shekarar ta Sha biyu cikin ta sha Uku Zamu je yanzu na kai shi a duba hannun "..Baffa na ya kai ƙarshen zancen yana sauke numfashi.Dai dai kuma lokacin ne saƙon mai gari ya iso masa na neman Shatu da iyayen ta.
Mai bada saƙon Yana gama sanar da Baffa ya wuce cikin mamakin abun da Zaidu yake yi anan amma ya san bai wuce takakka ce ya kawo gidan ba saboda ɗan uwan sa.
" Wallahi aja mata kunne ko na lafira ya fi ta jin daɗi wallahi yau ta leƙo barzahu ta gane mana asarori ".Zaidu yayi zancen yana barin wajen shima.
Inda ya bar Baffa na cike da takaici na rashin mutun cin sa da kuma neman da mai gari yake masu.Tunanin yadda case ɗin zai ƙare ne ya fara a tsaye ganin tsayin bazai amfana masa komai ba ga dare na yi hakan ya sa ya juya ya koma cikin gidan inda ya isko Inna ni tsaye ƙofar ɗakin Bibu ga Shatu daga ciki tana ta kuka kamar wadda aka yanka kafin ma ta taɓa ta dan duk ta ji komai da ya faru kuma tana da tabbacin Shatun ta dawo gida dan haka ta leƙa ɗakin ta sai dai babu ta ciki hakan yasa ta koma ɗakin Bibu Tun kafin ma ta shiga taji ƙusƙus ɗin su Bibu na ce mata kar ta ji tsoro ai itace mai gaskiya waya sa ya taɓa ta ai ya taɓa jin akwai lokacin da Inna ni tace mata kar ta riƙa bari maza su taɓa jikin ta koda hannun ta ne kar ta bari Indai ba Bibu ba sai Baffa na.Hakan da Inna ni taji ta tabbatar da yar ta ce mai gaskiya hakan ya sa ta dakata da ga shiga ɗakin sai dai ta ɗaga murya cikin kaushin murya tana kiran Sunan Shatun,ita kuwa Shatu cike da tsoro ta fara kuka dan ta san yau sai kashin ta ya bushe A hannun Inna ni.
Baffa na bai cewa Inna ni komai ba ya shiga ɗakin ya riƙo hannun Shatu yana share mata hawaye cikin Tausayin ta kafin ya tambaye ta ta faɗa masa gaskiyar abun da ya haɗa ta da Iro a karo na biyu idan har itace da gaskiya zasu tsaya mata a bata gaskiya komai wahalar samun gaskiyar.
Cikin kuka ta sanar masa da komai dake faruwa.Ɓacin rai ne ya bayyanar masa hakan ya sa rai ɓace ya ja hannun ta suka fice daga gidan ba tare da ya cewa Inna ni komai ba da ma shi ya san akwai dalilin da yasa Shatu ta masa haka.
Inna ni ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Bibu da yaji Tausayin yar uwar ta sa shima ya fara hawayen dan bai yi tunanin zata sha ba ko yanzu ma bai jin Inna ni zata ƙyale Shatun sa.....

Ba zamu daÉ—e muna free pages ba gaskiya zaku iya fara payment...
1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Daga wannan sati bazan ƙara posting a weekend ba gaskiya saboda ranar Hutu ce.🙏

Ƙarin bayani.
08069059746

Daga Alƙalamin ✍️
Gimbiyar taskira👑
FirstLady 🙌

React and Share, Comment PLS 🙏

*UPDATE*

https://chat.whatsapp.com/BzXaAD3pB6yJ1wBBrkE4V0

*Masu son ganin ƙarshen labarin sai suyi following channel ɗita.👇*

https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*💋KURMAN ƘADDARA💋*

©®Fa'iza Almustapha Murai

Daga Alkalamin✏

👄FA'EEH BG👄

💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18.A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

_Daga marubuciyar littafin_
*A MAFARKI NASANTA*
*RAYUWAR MU A YAU*

'''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''’'''""""""""
*_𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭_*

Best kayan kwalam

09025859622 or 09163353050

*END OF DISCUSSION PACKAGE*

Now available in- candies package stop in and stock up on a sweet piece of summer! 🍬🍔🧆

𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭: ce ta shirya tsafff domin kawo muku.

Samosa
Spring rolls
Filled doughnut
Glazed doughnut
Puff puff
Shawarma
Cupcake
Birthday cake
Bento cake
Egg roll
Milk cake

Candy's
Alewar madara
Gullisuwa
Tsami gaye
Coconut laddo
Milky gireba
Albishir
Mandula

Sayen daya ko sari muna aikawa ko ina cikin aminci muna karɓar order bikin suna ko aure

Location zamfara state ,gusau

What's no :-09025859622 or 09163353050

Hajiya karki bari wannan garaɓasa ta wuceki domin taken mu shi ne 𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝘿𝙀𝙇𝙄𝙂𝙃𝙏 Koda kuɗinka seda Rabonka...

Se kun zo
_______________&&&&

*BOOK ONE*

Free pages👌

P..0️⃣3️⃣

💦💦💦

ÆŠaki ta juya ta shige zuciyar ta cunkushe.Shi ko Bibu a sace yabi bayan su.

A ɓangaren su Baffa na da Shatou kuwa har suka isa Fadar mai gari yana Rarrashin ta dan ta kasa tsaida kukan ta Muryan da mahaifiyar ta tayi amfani da ita wajen kiran sunan ta ne abun da ke ƙara tayar mata da hankali.
Dai dai sun kusa isa Fadar ta mai gari ne ta tsayar da hawayen ta chak tare da haÉ—iye fuska dan kar ma a ga ruwan ta a samu damar yi mata rainin wayau ko ta muzan ta tana kuka gaban shi yayi zaton tsoro ne.

Zama suka yi a gafe kamar yadda Iro da abokan sa suke zaune.Gayar Da Mai Gari Baffa na yayi,sannan yayi shiru bayan ƙare ma su Iro da kowannen su yake cike da batsewa jira kawai suke yi a basu dama su illata shatou sai abun ya bashi dariya da ya kalli girman Shatun sa da kuma yan matasan da ke ta cika suna batsewa kan ta ,wani ko cikin Hancin sa zai iya tura ta amma nan dama suke jira su ci zarafin ta,ƙila har su karya masa yaaaa.
Ba su É—auki mintina uku da zuwa ba sai ga duka abokan nan wasan na su Shatou an tattataro suma tare da iyayen su.
Gaggaisawa suka yi da mai gari kafin kowa ya samu guri ya tsaya masu zama kuma suna zaunawa.
Gyaran murya mai gari yayi tare sallama ga kowa dake wajen har da wayen da ba,a gayyata ba a wajen yan ganin ƙwamm.
Sannan ya cigaba da magana...

" Shatou Iro ya kawo ƙarar ki,kumaa na samu shaidu da dama anan dan ga abokan sa sun tabbatar da ke kika aikata masa wannan ɗanyen aiki,ki duba ki ga yadda hannun ya kumbura lokaci ɗaya,sun ce bai Miki komai ba kika aza masa haƙora haka ".

Ai da sauri Shatou ta É—aga idanun ta tana zuba ma mai gari da ya sauke ayar zan cen da ya É—auko.Ido cikin ido ta ke kallon sa kafin kuma ta É—auke idanun ta tana mayar da su kan Zaidu da yake furta " Uban kike kallo haka ".
Samun kan ta tayi da sakar masa murmushi irin na baka da hankali kafin ta furta ƙasa ƙasa ta yadda shi kaɗai zai iya gane abun da ta furta masa " Ubanka dai "
Idanu zai du ya zaro da sauri yana ƙoƙarin yin kan ta aka riƙe sa inji wani daga cikin ya yan mai garin mai suna Ali wanda duk yafi su hankali kuma yaga lokacin da Shatou ta furta masa amsar da ta bashi,wanda sai da ya saka sa murmusawa da mamakin ƙarfin halin shatou.Ciccika Zaidu yake yi yana cije bakin sa ran sa ɓace ji yake ina ma akwai wuta ya jefa Shatou ya futa dan wata irin tsanar ta yaji jin yadda ko tsoron sa babu a idanun ta ta basa amsa.

Ita kuwa Shatou Hararar sa tayi tare da kallon Baffa na da yake kallon ta ganin tana Hararar Zaidu gashi yaga ana riƙon sa wanda kuma yana jin sa yanzu ya gama zagin ta a gaban sa,gashi kamar kan ta yake son ya zo.Kan sa kawa ya girgiza yana mamakin abinda ya ƙara harzuƙa sa haka.(Niko nace yar ka ce Baffa na 😂)
Kafin ya bata damar magana da idanun sa sannan ya furta " ki faÉ—i gaskiya kinji Shatou na ".kai ta gyaÉ—a masa tana sakin ajiyar zuciya.
Chapter 4 · 0% Book details