Sashe 16
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
SS Babban ɗan kasuwa ne da yayi gwagwarmayar rayuwa da turawa iri iri a fannin kasuwan cin sa kuma shine magini na arzikin wannnan zuri,a,shida ɗan uwan sa. Sada Saleh,Haifaffen garin Kaduna ne su biyu suke ga mahaifin su shida ɗan uwan sa,Usman Saleh tun farkon asali mahaifin su yana ƙaramin kasuwan cin sa a ƙofar gida irin na ƙaramin shago haka kafin A hankali Allah ya buɗe masa ya cigaba ya mayar dashi kasuwa daga nan ne komai ya fara chanza wa cigaba ya samu mai yawa.A lokacin kuwa Sada da ɗan uwan sa basu wuce shekaru bakwai, shidda a duniya ba,dan babu tserewa a tsakanin su mai yawa, dan haka suka taso cikin Gata saboda sune ƙwal a gun iyayen su,sune kyautar da Allah yayi masu bayan barowar su mahaifar su,dan Saleh mata ɗaya yake da ita Aisha,Sada Saleh shine Babba sannan Usman Saleh.Iyayen su irin fulanin nan ne da suka baro garuruwan su saboda tsaro suka fara gina kan su a cikin birni cike da gwagwarmayar rayuwa.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya ana ta samun cigaba ta ko ina,su Sada da Usman kuwa suna cigaba da samun ingantaccen kulawa da ilmi mai kyau.Kwatsam ana zaune wata rana Saleh Ya tsiro da zancen ƙarin Aure A'isha bata tada hankalin ta ba kasancewar ta mace mai alkunya da haƙuri duk yadda yake ɗarare da zancen amma ganin yadda ta kwantar da hankalin ta dan shi kan shi bai san abun da zai sanya shi ƙarin Auren nan ba saboda idan ya ce A'isha ta rage shi da wani abu yayi ƙarya.A haka har aka yi Auren kuma gwargwado sun haɗa kan su suna mutunci sosai a tsakanin A'isha da amaryar ta sa Ruƙayya.Ya haɗu da Ruƙayya ne a kasuwa tana kai masa tallan Nono mai kyau.Cikin aminci suka cigaba zaman su babu hayaniya har amarya ta samu rabo ta samu yar ta mace.Aka saka mata sunan Yar uwar Saleh mace ƙwaya ɗaya tal da suka fito ɗaki ɗaya da ita mai suna Sakina wadda yayi kukan rabuwa da ita saboda ya neme ta bai gan ta ba bai san inda ta faɗa ba dan da alama ɓacewa tayi,basu lura bata cikin ayarin ba sai da suka samu kan su a cikin jama'a,kuma har yanzu bai cire rai da sake ganin fuskar yar uwar shi ba.Sakina ta ɓata ne a lokacin da suka yi gudun hijira daga asalin mahaifar su a chan wani ƙauyen Adamawa.
Sakina ta samu kulawa ta ko ina ga yayyen na ta ga kuma mahaifin ta da A'isha da suke kira Mama.
A haka yarinya ta fara girma da wayo har ta gane dukkanin yan uwan ta itama ta tashi cike da gata.
Ana nan kwatsam sai Allah ya ɗauki ran Ruƙayya da tayi fama da masassara ta kwana biyu.
Mutuwar Rukayya ta taɓa kowa a cikin gidan babu ma kamar Sakina tayi kuka matuƙa saboda ta fara yin wayau sosai.Su kan su su Sada da Usman sun ji mutuwar haka ma A'isha da ta saba da Ruƙayya sosai kamar ya'ya da ƙanwa haka zaka ga suna mu,amalar su.Bayan rasuwar Ruƙayya Ciwo ya sako Sakina itama da ƙyar ta sha cikin yardar Ubangiji ta samu lafiya.A hankali ta fara sakewa cikin yan uwan ta tana samun kulawa fiye da wadda mahaifiyar ta take bata haka suka taso cikin so da ƙauna Sakina yarinya mai shiga rai da tarbiyya.
Akwana a ta shi rayuwa ba wuya yau kusan shekara biyar da rasuwar ruƙayya kuma a yau ne Alhaji Saleh ya kwanta dama,sunyi kuka sun ƙoshi cike da kewar bangon su,ana haka kuma Babban shagon sa dake kasuwa ya kama da wuta,babu abinda aka tsira da shi,a kuma dai dai lokacin da iftila'in ambaliya ya afkawa gidan su,cikin ikon Allah sun tsira da rayuwakan su,amma babu maganar kayan inganta rayuwa.Rayuwa tayi wa su A'isha da su Sada zafi babu duk tarin dukiyar su ta bi ruwa sun koma basu da komai sai kayan jikin su da rayuwar da Allah mai rahama ya bar musu.lokaci ɗaya suka fara fita hayyacin su saboda rashin bangon na su ga yunwa da take son sako su gaba.Gashi suna zaune cikin gidan kamar dole saboda yadda yake dawo musu da moment tare da mahaifin su.
Karatun su,na boko na Arabia komai na su ya tsaya chak domin ko taimakon su babu wanda ya iyayi sai wani bawan Allah da yake maƙwabcin Saleh a kasuwa shine mai basu hatsi.A haka rayuwa ta fara tafiyar wa da Su sada babu daɗi koda yaushe cikin ƙunci.ƙara fahimtar rayuwa da suka yi ganin babu mai taimaka musu hakan ya sa suka koma neman na kan su suka shige kasuwa suka bazama nema dama ance zafin nema baya kawo samu to haka dai suke kalato wanda zasu saka a abaki ko bai ishe su ba koda mahaifiyar su ce kawai da Sakina za su yi farin ciki dan sun san sune mafi buƙatar kulawa yanzu..