← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 110

Sashe 96

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

To subscribe yours contact this number
08069059746

_*KURMAN ƘADDARA*_

*_©®Faiza Almustapha Murai_*

_*FA'EEH BG*✍️_

P________4️⃣ 3️⃣

*BOOK ONE*
*_FREE_*

*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t

_*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_

💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕
💕💕💕💕
💕💕💕
💕💕
💕

Wani table ne dake kusa da Bilal ta ɗaura tiren Saboda Reena ta faɗa mata saƙon sa ne.
Gaisawa suka yi kaɗan sannan ta ƙara yiwa yan biyu ya gajiya sannan ta bar falon tana amsa umurnin Ummah dake tabbatar musu da a ƙara kimtsa dinning tunda sun gama aikin Su da wuri ita da masu aikin.
Miƙewa Ummah tayi tana cewa " Kuma fa ina ga har da yunwa ke ƙara nuƙurƙusar ta fa,da zata iya ai da an haɗa mata abu mai sauƙi ta sha".
Cike da yar natsuwar sa da kulawa ya ce " Ummah ai wannan ita aka haÉ—awa ko kaÉ—an ne sai ta sha ".
Kai Ummah ta jinjina kafin ta ce "Eh yayi hakan bari na tashe ta ".
" Alina,! Alina ! Alina ! "
Haka Ummah ta jera mata sunan na ta inda kafin a hankali ta fara buÉ—e idanun ta da suka fara mata nauyi.Ya Mutsa fuskar ta tayi kafin ta ce " Ummah na fi son kwanciya ".tana batun sakar mata kuka.
Ummah cike da kulawa tace " yi hakuri ki tashi zaune,kin ji ki saka wa cikin ki wani abu ".
Ɓata fuskar ta tayi kafin ta ce " Ummah ai na faɗa Miki na ci chocolate fa,kuma na ƙoshi,Dubi fa ciki na "
Ta kai ƙarshen zancen tana buɗe shaffafen cikin ta.
Bilal dake kallon su ne ya janye idanun sa da sauri yana kallon shayin dake ta tururi.
ÆŠan fara feta shi yayi da spoon yadda zata ji saukin shan sa.
Ummah kuwa rarrashin ta ta fara kafin tace " Ni dai yanzu ke da ya yan ku bari na je na É—auko waya na,kafin Abban ku ya fito ".
Miƙewa tayi ta haye steps tana jin yadda Leena ke ta ƙoƙarin sakin kuka.
Ita kuwa Reena kallon ta kawai take yi.
" Ya B ka rarrrashe ta,ko Ni na sha shayin makon ta ".
Ɗan murmushi yayi yana jan table ya zauna ya miƙa wa Leena ɗin tea ɗin yana haɗe kyakkyawar fuskar sa.
Ɓata fuskar ta tayi kafin ta karɓi cup ɗin da ya dungura mata.
A hankali ta fara sha ganin tana sha da wasa hakan ne ya sa ya karɓa ya fara bata da kan sa haka take karɓan tea ɗin kamar ɗaci duk da ta ji daɗin saukar sa a cikin hanzayen ta.
Motsin Abba ne ya sa shi É—an kallon steps din.
Abba ne kuwa ke saukowa fuskar shi cike da murmushi yana kallon su wani irin farin ciki na mamaye sa kulawar da Bilal yake bawa yan uwan sa na sanyaya masa zuciya ya san cewa ko ba sa duniya Indai har yana raye zasu samu kulawa bayan ta kakannin su.
" Ai dole sai da hakan dan tun da na shigo na ga alamar bata ci wani abun kirki ba ".
" Ka kyau ta Allah yayi muku albarka ".
" Amin Abba ".
" Yawwa Ina Umman ku ".
Dai dai nan kuma ummah ta fito riƙe da wayar ta a hannun ta fuskar ta ƙawace da murmushi.
Yau Abba Dinning Abba ya wuce bayan hango an jera komai a chan.
Bayan sa Ummah ta bi bayan ta yiwa BILAL kallo É—aya da Leena.
Reena kuwa hankalin ta ta mayar kan Tv tana cigaba da kallon ta shar toon.

***

" Ba zai yuyu ba gaskiya Boka gangaro ya kamata dai ka ƙara duba mini lamarin nan babu yadda za,a ce komai yana faruwa haka ba tare da kasan wayen da ke wannan aikin ba ".
" Hmmm ba zaki gane bane ai shi rame da ƙarami yake farawa kafin ya yi girma na sha faɗa Miki ki fitar da hannun ki cikin wannan rigimar wannan abun daɗaɗɗen aiki ne yanzu ya fara ci,bana son Ni dake mu shiga Masifar da zata yi muna wahalar fita,Masu wannan aikin ba ƙananan Azzalumai bane suna aiwatar da shi ne cikin kuzari domin kuwa su ɗan duhu kowa ya Sani ba su san inda imani ya shiga ba,ba wani sanin su ne ban yi ba,a wancan karon na ji tsoron su ne hakan ya sa na ɓoye mikisaboda yadda na tsorata da abun da na gani,na dai shaida Miki ki fita wannan sabgar aikin ki ɗaya kuma yana kan ci,muna aiwatar da shi,duk da an riga ki aiwatar da shi amma zamu iya loda na mu koda ace wanchan ya sauka ".
" Hakan shine zai kawo mana salama Ni dake ".

Ƙaramin tsaki matar dake zaune itama cikin shigar ta ta alfarma sai dai fuskar ta rufe ruff da wani irin liƙab irin na zamani wanda sai kayi da kyau zaka iya hango idanun ta domin rufe yake ruff.

" Naji yanzu ga wannan Ni dai a yi mai yuyuwa kuma zan yi ƙokarin kwantar da hankali na,tun da haka kake so,amma muddin na ga cigaban da na gani ya tsaya zan dawo kayi aikin nan ko na chan za waje ".
" Ba sai an kai chan ba shegiya yanzu dai zube muna kuÉ—in mu kiyi gaba ".
Itama tsaki ta ja dan ta tsani zafin ga da yake mata wasu lokuttan duk da kasancewar sa boka ji take kamar ta kai masa bugu sai dai tana da tsoro dan tana mugun tsoron aljanu dan haka take raga masa kar ta kai kan ta ta baro.
Kuɗaɗe ne ta Fiddo da su masu yawa ta a ajiye masa aiko ya kwashi abun sa yana gaɓɓatan dariya kamar wani zararre.
Miƙewa tayi ta fice da baya baya tana zagin sa yana Amsawa,sannan ya na ramawa.
Haka tayi ta ta fiya da baya baya har sai da tayi masa Nisa kamar kullum sannan ta juya tana cigaba da tafiyar ta hankali kwance.
Fitowar ta bakin titi ne inda ta parker motar ta ta shige tana tada ita sai dai tunda ta shiga motar take jan tsaki ita kaÉ—ai....
Chapter 96 · 0% Book details