Sashe 107
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
" Yanzu me ye abun yi Anty ruƙy ".?
" Abun yi kawai shine kema ki bi hanyar da na bi ki jaye shi wajen ta kafin ki rasa shi ".
Numfashi Hajiya makiyya ta sauke kafin ta ce " An jima zan zo gidan ki Anty ruƙy wallahi yau ba zan iya barci ba sai na san abin yi dan ba zan yarda ina ji ina gani wata shegiya ta jaye mini miji ba a bariki ba, ko ta karɓe mini shi ".
Sallama suka yi tana a jiye wayar tare da jan tsaki tana haɗiyar wani baƙin ciki bayan tuno da saƙon da ta gani wanda mijin ta ya rubuta shi da kan sa cikin salon roƙo,gashi sai ja masa aji ake yi.
Tsinewa Leesha ta dinga yi kamar ta cire bakin ta.
Kafin ta miƙe ta haɗiye komai ta fito ta cigaba zaman jiran fitowar Alhaji Mamman ɗin wajen breakfast saboda yana fita da wuri majalisa yau,tare burin aiwatar da maganar Anty ruƙy da tace kar ta yadda ta nuna masa ta ga wani abu a wayar sa.
A ɓangaren Mamma kuwa shayi kawai ta haɗawa Asad mai kauri ta bashi ya sha.
Sannan ta ƙara masa wani sabon wanka ta shirya sa tsaf cikin shigar sa ta uniform dark blue masu kyau da necktie ɗin su.Kayan sun masa mugun kyau kamar koda yaushe yau ma Mamma sai da ta zuba masa idanu tana kallon sa dan koda yaushe wani kyau yake ƙarawa a idanun su.Turarukan sa dake shaƙe akan madubin sa ta fesa masa tare da gyara masa kan sa dake shan kayan gyara kafin suka fito daga bedroom ɗin na sa dake kusa da na Alishat ɗin sai dai na shi ta ko ina kayan wasan yara ne masu tsada da kyau.
Da sallama Mamma ta shiga bedroom ɗin na ta tare da Asad riƙe a hannun ta yana kumbure kumbure.
" Ummieey,Mamma wai ba jata bani ice cream ba na sha ".
Maganar sa da ta shiga kunnen ta cikin barcin da ya fara fisgar ta ne hakan ya sa ta buÉ—e manyan idanun ta a hankali a kan sa tana É—an Lumshe su tare da sakin guntun murmushi wanda daga shi sai Mamma da Abbi ke samun sa.
" Asad yau an tashi da sanyi ka bari sai anjima idan ka dawo school ".
Jin wannan magana ta sanya shi fashewa da kuka take dukkanin su hankalin su ya mugun tashi idanu Alisha ta zuba masa kamar ta saka kukan itama,saukowa daga kan gadon tayi a hankali ta janyo shi jikin ta,ta rungume ta fara rarrashin sa.ƙin shiru yayi sai da ta ɗaga shi sama ta fara juyawa dashi tana masa chakulkuli take kuwa ya sake ya fara ƙyalƙyata dariya kamar ba shi ba itama kan ta dariyar take yi cike da jin daɗi da farin cikin da take samu a gurin ɗan na ta.
Mamma kuwa kallon su kawai take yi cike da tausayin su.
Bakin wata locker ta je dashi rungume akan kafaɗun ta wata jaka ta janyo ta saka hannun ta ciki sai gata da chocolate guda uku masu tsada jakar sa dake kan wata yar hanger mai kyau ta buɗe ta zuba masa su a ciki dan ta san halin sa da shan chocolate kamar dan shi aka yi su bakin sa ya san kwaɗayi kwarai da gaske,haƙorin sa ɗaya har zaƙi (cin Zuma)ya fara kama sa sai fira (giɓi)Ya cire sa.Bakin sa washe yana murmushi yake kallon mahaifiyar ta sa cike da ƙauna kafin ya sakar mata kiss gefen kumatun ta ya ce " thanks you Ummmiey " cikin yar Muryar sa ta yara.
Murmushi ta saki mai sanyi kafin ta sakar masa kiss a goshi itama sannan ta sauke sa ƙasa.Tare suka fito falo har da ita bayan ta ɗauro wata doguwar hijab akan rigar baccin jikin ta,da ta a za rafa akan sa.Tare da keys a hannun ta,dan ita ke Kai sa ta ɗauko sa.
Mamma ce ta Kalle ta kafin ta ce " Lafiya hala baki fita yau ".?
" Zan fita amma sai zuwa 10 ko 11 Mamma ".
Kai Mamma ta jinjina kafin ta miƙa ma Alishat lunch box na Asad ɗin.Kasancewar baya breakfast mai nauyi tun da safe.
Abbi ne ya fito cikin shirin sa na karya wa yana gamawa ya fice daga nan.
Har ƙasa Alisha ta gayar da shi.
Shiko Asad da sauri ya faÉ—a jikin sa yana dariya É—auke sa sama Abbi yayi kafin ya ce " yoo my boy,Yau ka yi missing lada mai yawa,kar ka bari gobe ka rasa ka ji,ina son mu shiga aljanna tare ".
" Abbi zamu sha Ice cream ko mai yawa ko ".
Kai Abbi ya gyaÉ—awa Asad cike da murmushi.
Dukkanin su murmushi suka yi kaÉ—an sun san inda ya dosa.
Dariya yayi mai kyau da take fitar da haƙoran sa dake a ware wasu duk sun fita ma saboda firan sa da yake kai yanzu.
Mamma ce ta ce " ÆŠan nema ice cream É—in nan dai ba zai fita bakin ka ba ".
Dariya yayi bai ce mata komai ba sai faman shafa chocolate da Abbi ya basa yake yi yana jin daÉ—i dan Indai chocolates ne babu wanda ke masa shamaki da su Amma abun da ya shafi su Ice cream sune ake hana masa saboda yanayin ciwon sa.
Sai da ya gama firan sa da Asad sannan ya ce " Yau ba da wuri za,a fita ba kenan " ?
Ya furta wa Alisha wadda ya karɓa gaisuwar ta kafin ɗaukar Asad.
Kai ta É—aga masa kafin ta ce a hankali " Sai zuwa 10 haka ".
" Allah ya taimaka ".Cewar Abbi.
" Amin " Suka amsa har Asad.
Miƙa mata shi Mamma tayi bayan saukar sa jikin Abbi.
Bye bye yake musu har suka fice shi daga gidan Alishat dai sai ɗan murmushi take saki a hankali tana kallon Asad ɗin da ta tashi da mugun tausayin sa da ta kwana da shi,wanda yake maƙale ƙasan zuciyar ta koda yaushe.
Suna fita tsakiyar compound É—in wata lafiyayyar mota suka nufa ta buÉ—e,ta saka lunch box da school bags da ta fito da ita,bayan ta sanya su ta buÉ—e ma Asad extra sit sannan ta rufe ta koma mazaunin driver ta shiga.
Kunna motar tayi kafin ta bata wuta suka fice gidan bayan wangale musu gate da aka yi na gidan...
Gudu take a hankali na zallar kwarewar ta akan kwaltar.karatun Qura'ani ta kunna musu,ƙira'ar Sheikh Afif inda take bita wa a hankali,sai Asad da ke ta tsalle tsalle kan sit yana bitar dan inda ya iya ne ta kunna masa,wanda har ta gaji da furta ya zauna ya ƙi.
Suna isowa dai dai makarantar ta su dake É—auke da tambarin S&A Staff school Abuja.
Ta dakata ta juyo tana kallon Asad da ya hargitse gashin kan sa da ya sha gyara.
Ɗan zuba masa idanun ta tayi tana jin wata irin kasala na saukar mata domin a duk lokacin da zata yiwa Asad kallo na ƙwas dan ganin ainahin kamannin ta da shi da kuma tantance irin ta sa kamar da zubin da har yanzu take mamakin yadda hakan ya kasance.Sai ƙirjin ta yayi ta bugawa har ta ji Numfashin ta na neman barin gangar jikin ta.
Yanzu ma hakan ce ta kasance sa ita dan haka da sauri ta janyo ruwa kusa da ita ta sha sannan ta rufe idanun ta jingina da sit tana sauke numfashi.
" ummieey mun iso fa ".
Muryan Asad ta sauka cikin kunnen ta yana furucin.
Yana kallon gate É—in na su da ake ta wuce wa da yara cikin sa dan an buÉ—e sa sosai.
" Yes maa boy I know,I just want you to have a good small rest ".
Dariya yayi mata yana furta " Yes Ummieeey na "Murmushi tayi tana shafa kan sa.
Sai da suka É—auki mintuna biyu kafin ta ce a hankali cikin Rarrashi " Asad don't fight anyone pls,Ka kula da kan ka,kayi karatu sosai idan ka dawo ka koya mini ".