← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 110

Sashe 92

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai ta jinjina tana Murmushi bayan Baffa na yace mayar da idanun to,kar su zube. Bibu kuwa kallon Baffa na yayi da shatou yana share hawaye, Shatou ɗan hararar shi tayi bayan haɗa idon da sukayi,dariya ta ɗan saki kaɗan ganin yana matsar hawaye.Baffa na neh yace " haba kai ko Habibullah maza ba a san su da saurin kuka ba duk ka komawa Inna nin ku kamar Shatou ". Baki shatou ta turo gaba tana furta " Ai ni na girma dan na san na girmi Bature nesa ma shi da yake da girman biredi dan haka na bar wa Bibu kuka ba zan ƙara yin kuka Bama ". Zuba mata ido Baffa na yayi yana kallon ɗan ƙaramin bakin ta dake magana chau chau.Murmushi ne mai faɗi ya samu kan sa da yi yana girgiza kan sa domin kuwa ya san wa take magana kai. " Allah ya sa " Shine abun da Baffa na ya furta kawai yana cigaba da murmushi kan wani al'amari dake shiga zuciyar sa akan lamarin shatoun na yau. '' Ki daina yiwa mutane rashin kunya yanzu Kinga Innar ki ta Hasala dake ". Ganin yadda ta ɓata fuska ne ya sa ya furta. " Zamu cigaba da bata hakuri karki damu shatoun Baffa nan ta ". Ya kai ƙarshen zancen yana shafa kan ta tare da ƙara ƙawata fuskar sa da murmushi. Itama sakin fuskar ta ta tayi tana sakin guntun murmushi. Bibu kuwa zuwa lokacin ya share hawayen sa yana shesshekar kuka. "Adda shatou kiyi haƙuri wallahi ba ƙarar ki na je kawo wa ba,baki na ne ya yayi maganar ban sani ba ". Yar guntuwar harara ta ƙara sakar masa ta wasa tana riƙo hannun sa tace " Ai ban ce ban yafe maka ba da zaka yi irin wannan kuka,kuma baka ga Inna ni bata dake ni ba " Ta kai ƙarshen zancen tana ɗan kallon ƙofar ɗakin Inna ni. Baffa na ne ya ce " kowa ya wuce yayi Sallah kafin ta wuce dan tana hanya " Dan haka suka rabu kowa ya shige ɗakin sa bayan yayi alwallah. Cire kayan jikin ta tayi ta sanya wata yar rigar ta, ta a tampa ta,ta da Sallah. Shiko Baffa na ficewa yayi daga gidan gaba ɗaya. A ɓangaren Inna ni kuwa ta jima zaune bakin ɗan gadon ta tana dafe ƙirji da ƙoƙarin hana tashin hankalin ta bayyana fili.Sai da ta samu natsuwa bayan nanata sunayen Allah sannan ta fito daga ɗakin tana cigaba da ayyukan gaban ta sai dai ta sha al washin ko ranƙwashi ne sai ta yiwa Shatou da ta tayar mata da hankali ko ta rage zafi da raɗaɗin abun da ta ji. Shatou na gama sallah bayan ta yi addu'a ta cire rigar jikin ta ta ɗauro zanen ta na wanka sannan ta fito tana sakin yar doguwar Hamma ta yunwar dake naniƙar cikin ta. Tsaye tayi ganin Inna ni zaune sai kuma ta fara susar kai tana furta " Inna ta ina Yini " Ɗan ɗagowa Inna ni tayi ta Kalle ta ta ɗauke kai. Ɓata fuska shatou tayi kafin ta matsa kusa da ita cikin ɗar ɗar cikin yin ƙasa da kai ta ce " Na fa daina wannan ma saboda sun taɓa yi muna wulaƙanci ne, saboda ina da Haushin su shi ya sa na musu rashin kunya,kuma kar ta san kar ni da su babu abinda zasu iya mini dan ogan na su ma girman biredi ne " . Ta kai ƙarshen zancen tana dariya harda ƙyalƙyatawa.Inna Ni dake sauraren ta sai yanzu ta ɗaga kai ta kalle ta kafin ta saki guntun murmushi tana girgiza kan ta a cikin zuciyar ta kuwa faɗi take mai hali baya fasa halin sa yanzu a wannan yanayin har ta samu damar dariya irin haka. Ganin murmushin Inna ni ya sa shatou ƙara gyara zama tana cewa " Kuma fa Inna ni baki san abinda suka mini ba kwata fa suka watsa wa su Amina " Ɗan shiru tayi ganin Inna ni ta kalle ta sai ta ƙara furta " Ai har da ni,Ni kuma shine yanzu na rama ". Kai Inna ni ta girgiza bayan gama zancen Shatou wadda ta yi shiru tana ɗan leƙen fuskar Inna ni da ta juyar da kan ta dan ganin ko ta saki fuskar gaba ɗaya. Dai dai nan kuma Bibu da ya gama ta sa Sallah ya fito yana furta " Inna ni yun wa nake ji,Ina abincin mu ". Kallon sa Inna ni tayi da murmushi kafin ta ce " Habibullah kamar dai yau ka sauka gidan nan ". Shima dariya yayi dan sun san inda take ajiye musu abincin su. Amma yau shine da tambaya duk da wata rana ita ke zuba musu ta kawo musu. " To ai Inna ni kin fi saba mana da ki kawo mana da kan ki ". Shatou tayi zancen. A wannan karon Inna ni Murmushi ta yi wa shatou kafin ta ce " To yanzu sai ku je ɗaya ya zuba muku sai kuci tare ,dan tuwo ne ma na dawa yau muka yi gidan ". Ai ko rufe baki bata yi ba shatou ta fashe da kuka tana furta " Allah Ni ba zan ci tuwo ba haba,jiya ma fa shi muka ci,yau ko yar murjin nan Ace ba,a dafa mana ba " Ta ƙara ɓarkewa da kuka " Shikenan sai mutun ya dafe shima,ai in mutun na cin tuwon dawa kullum baƙi yake yi dan haka Ni dai ba zan ci ba Allah kuwa sai dai na zauna da yunwa na idan Baffa na y zo ya siyo mini tsiren Sharehu " Ta kai ƙarshen zancen tana shesshekar kuka tare da ƙara taɓe baki na sangar ta. Ƙala Inna ni bata ce mata ba sai da ta gama har ta fara share hawayen ƙaharun sannan ta ce " Habibullah shiga ka ɗauko mini Bulalar nan da nake ta ajiya ƙasan gado na,dama ta tsuma sosai jini kawai take jira ta ɗiba,sauri zaro mini ita". Aiko shima Bibu baki ture ya kama hanyar ɗakin yana kallon Shatou da ta ke ƙoƙarin maƙalkale Inna ni aiko yana shigewa ta shige jikin Inna ni kamar zata koma ciki tana furta " Ai na ce na daina kuka fa yanzu ma baki ga dariya nake yi ba " Ta fara ɓallan dariya ga hawaye na Silalo mata dake nuna dariyar ƙarfin hali ce kawai da Shegen tsoron ta tunda ta san Baffa na baya kusa dan haka ta yiwa kan ta wannan dubaran dan fidda kai. Inna ni kuwa ikon Allah take kallo tana son tayi dariya amma ta haɗe ran ta. Sai dai cikin zuciyar ta sai da ta dara musamman da ta kalli fuskar shatoun ta da hawaye keta silalowa tana gogewa tana ƙara cewa " Dube ni fa na daina kukan nan ai haka na cewa Baffa na ko Bibu " Ta kai ƙarshen zancen tana kallon Bibu dake tsaye bakin ƙofar ɗakin Inna ni Hannayen sa ɓoye a bayan sa. " Kawon bulalan ". Inna ni ta furta wa Bibu bayan ta ƙare masa kallo daga tsayen da yake. Kuka shatou ta ƙara fashewa da shi kafin ta ce "Na fa daina wallahi Na tuba Inna ni ki mini afuwa ina son shiga aljanna zan dinga jin maganar ki ". Jin Inna ni na furta kin shigo hannu mai kunnen ƙashi bayan gama furucin ta na farko.Kuka kasharɓan shatou take yi wanda ya sanyaya jikin Inna ni da ta haɗe mata hannaye waje ɗaya,alamar Dagaske dakan ta zata yi kamar yadda shatou take zato da Bibu da idanun sa suka cika da hawaye. " Bani bulalan,ko sai na zo gurin " Inna ni ta ƙara furtawa zuciyar ta ƙuntace domin kuwa wata irin damuwa take tsintar kan ta a duk lokacin da shatou take cikin yanayi mara daɗi tunanikan baya ke dawo mata marasa daɗi da masu daɗi da wayen da ya kamata su zauna mata akai da wayen da basu kama ta ba. " Dan Allah ki yafe mini Inna ni ina son shiga Aljanna zan dinga jin maganar ki,kuma idan nayi kuɗi zan kai ki Umrah da hajji ke da Baffa na ".inda ta kai ƙarshen zancen tana ƙokarin ƙara fashewa da kuka. Wani irin rauni ne ya bayyana gare ta ƙarara sai da idanun ta suka cika da hawaye sai ta shanye abun ta gudun kar yaran su gani duk da ba lallai su fahimta ba. " Nace ka bani bulalan fa " Inna ni ta ƙara furtawa tana ɓoye murmushin ta da ya fi kuka ciwo.Duk da ta san cewa Bibu bai ɗauko komai ba hasalima bata da wata bulala dan ta samu ta rage fitinar Shatou ne da ita kan ta ba son bugun ta take yi ba. " Inna ni idan ba kya sona zan bar gidan nan kawai ni nama yarda a mini Aure kawai ". Cike da sakin fuska Inna tace " Dagaske ". Kai shatou ta gyaɗa mata tana sharar hawaye. Yar ƙaramar dariya Inna ni tayi kafin ta ce " kai Masha ALLAH,to waye mijin dan mu kai ƙarshe kafin zuwan Baffan ku ". " Ni kawai Zan Auri iro tun da yana sona idan na zama yar sanda zan je da shi birni ya riƙa wanke bakin sa,Idan na zama Babba kuma sai na sake shi ya dawo ƙauye yayi sabon Aure " Wannan karon dariya Inna ni tayi da ta bayyanar da wushiryar ta irin ta Shatou mai kyau kafin tace " Kai masha Allah wannam abun alkhairi ne Bari Baffa nan ku ya zo sai aje neman Aure da wuri da kan mu ma zamu je na dangin mijin zasu zo ba sai a fara daga yar mafarauci ". Shiru Inna ni tayi bayan fitowar wannan furuci da ta ji ya mata wani iri a baki kafin ta ɓatar da yanayin da zuciyar ta ke hauhawa tana ƙara sakin dariya. Ita kuwa Shatou baki ta tura gaba tana sauke ajiyar zuciya. " Ai na yafe Miki shatoun Baffan ta ". Hawayen ta,ta ida sharewa tana sauka daga jikin Inna ni. Bibu kuwa yar ƙaramar dariya ya fara yi tun bayan fara maganar ta Aure. Ɗauko muku abincin ku yau faten dankali
Chapter 92 · 0% Book details