← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 110

Sashe 76

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Rarrashin ta ya dinga yi tare da Bibu da ya faki idon Inna ni da ta shige ɗaki ya ƙi fita daga hanyar da ya nufa.
" Baffa na kalli hannun ta fa Wallahi Adda shatou kin daku,Kuma bamu yafe wa Malam Abu ba.".
Cewar Bibu.
Kallon hannun ta,ta yi inda shatin bulala ya kwanta kan lafiyayyar fatar ta.
Cike da sangarta ta ƙara ɓare ƙaramin bakin ta.
Tana yi tana kallon gurin tana sake fashewa da kuka.
Baffa na hankalin sa duk ya tashi dan haka ya cigaba da rarrashin ta.
Sai da suka tabbatar ta yi shiru sannan Baffa na ya furta a hankali " Karki ƙara yiwa malamin ki Allah ya isa kinji shatou malamai sune magada annabawa kinji,haka kaima Bibu kar na ƙara jin haka ".
Kai suka É—aga masa ganin babu alamar wasa kan fuskar sa.
Miƙar da Shatoun zaune yayi kafin ya ce " Ki riƙa zuwa makaranta kinji ko,bana son ana dukan ki,gashi ma Makarantar boko sai karar ki ake kawo wa dan Allah ki daina kin ji , Mahaifiyar ki bata jin daɗin haka bare ni,Ki mayar da hankalin ki kamar yadda Bibu ke son zama ba kin ce Yar sanda kike son zama ba " ?
Kai ta gyaÉ—a masa.Cikin tabbatar wa.
Murmushi yayi kafin ya ce " Yawwa sai kin dage dan karatu shine gaba su ma ba haka Kawai suka saka kayan Yan sanda ba ".
Dan Shatou tunda Abbu ya zo tare da masu kayan yan sanda taga harda mace cikin to tunda ta ƙyalla ido ta sha wa Baffa na kai irin wacchan matar da ta gani ga wannan mutumin mai kyau take son ta zama nan ya ce mata yan sanda ne ta ce ta ji har da aikin su ya faɗa mata ta ce ta ji ta gani.Da farko dariya abun ya bashi sai da yaga dagiyar tayi yawa da nacin tambaya hakan ya sa ya gane da gaske take yi.Shi ya sa yake biye mata a je hakan kawai shi ya san babu wani yar sanda da zata zama suna sake ko suna ɗaure,ai Bama nan gizo ke saƙa ba.Hmm
Numfashi ya sauke yana ƙara ƙawata fuskar sa da murmushi kafin ya ce " dan haka ki dage kin ji,Allah ya baku sa,a gaba ɗaya,shi Bibu ya ce mai Shari'a yake son zama kamar yadda mai gari yake yi ".
Dariya ta saki kaɗan jin wai bibu mai Shari'a yake son zama kamar Mai gari yana nufin irin yadda idan an kai wa mai gari ƙara yayi sulhu ya bawa mai gaskiya gaskiyar sa.Chab lallai ita kam yar sanda take son zama sai ta saka wayen nan uniform ɗin ko dan ta kama irin su MAHAJ masu rainawa talakawa suna musu yadda suka so.
Sunan MAHAJ da ya shigo cikin zancen zucin ta ne ya sa ta jan guntun tsaki.
Har sai da Baffa na ya Kalle ta ganin ta haÉ—e rai tare da sakin tsakin.
" Lafiya dai ko ".?
Ya tambaye ta yana kallon ta.
Ƙara taɓe fuska tayi tana turo baki gaba ta gyaɗawa Baffa na kai kawai.
Murmushi yayi kawai tare da girgiza kan sa.Yana mamakin halin shatou wasu lokuttan tayi ta abu kamar mai tashin iska.
A ɓangaren Iro kuwa abun duniya ya sha masa kai dan gargaɗin mahaifin sa yake tunowa sai dai har yanzu bai jin ya bar zancen dan haka yau ɗin nan ya shirya tare shatou idan Allah ya Fiddo da ita dandali dan yanzu ba kullum take fita ba sai tayi sati bata fita ba.Kuma hakan mugun yiwa Inna ni daɗi yake yi dan haka yanzu bata wani mata faɗan fitar saboda ko ta fitan tana dawowa da wuri kuma tare da Bibu suke tafiya dan gaba take saka shi.Sai dai Kullum Inna ni cikin Bin ta da Addu,a take ta kariya daga shaiɗan da aljan,da mutun.

Kamar kuwa ya sani yau Allah ya fitar da Shatou tun daga nesa ya hango ta tana yankar gudu dan haka bakin shi washe ya tare ta yana zuba mata idanun sa.
Turus ta ja ta tsaya ganin sa.
Ɗan zuba masa idanu tayi na ɗan lokaci kafin ta ɗauke idanun ta daga kallon sa tana taɓe bakin ta ganin duk yayi duhu ya faɗa kamar wani mai aikin wahala,bayan kuma A iya sanin ta mai gari bai barin sa ko noma ne saboda gata.
" Haba Shatou idan babu yaƙi me ya kawo gaba " ?
Harara ta sakar masa kafin ta ja ƙaramin tsaki sannan ta ce " Yaƙi kuwa tsakani na da kai ai baya ƙarewa tunda haka kake so yanzu me ye na tare mini hanya ta idan ba neman faɗa ba ".
Ta faɗa tana hura hanci irin an dame ta ga cikakkiyar budurwa dan hannuwan nan zaune suke dam a gefen ƙugu.
Shidai Iro kamar Gaula haka ya zuba mata ido dan shi duk wani abu da shatou zata yi yanzu burge sa yake yi Kamar kar mahaifin sa yayi masa kashedi da ita ya ji duk duniya babu wanda ya isa ya raba shi da Shatou sai Allah.
Ya sha shan alwashi iri iri akan ta tun bayan da ya fara son ta har izuwa yanzu haka yake dan ya sawa ran sa idan har ba shine mijin shatou ba kuwa sai dai yayi mai hisshe sa wadda zata saka dole a duba masa ko ba,a so.Dole na so ki yar Abar nan ga Shegen kyau kamar hindiya.
Numfashi ya sauke yana ajiye maganar zucin sa,yana murmushi da yake bayyana haƙoranta sa da suka fara yin jaa saboda rashin wanke bakin.

" So ne fa ba komai ba ya kamata Babies ki gane ".

Wata uwar Harara ta ƙara sauke masa tana ƙara hura hancin ta musamman jin sunan Babies da ya kira ta dashi dan ya mata daɗi amma bata yarda ta nuna masa ba kar ya ga damar ta ko ya zaci wani abun.

Shiko Iro cike da iyayi yake ta ƙara Nana ta haba Babies.

Wai tsaya 🤔🤭ko dai yan matan da yawa suke gaban iro bamu sani ba.Koda yake degree ce ga Manya🤣

Gaba tayi aiko Sarkin nacin ya ƙara cin gaban ta.

Cike da tsiwa ta fara sauke masa Masifa sai dai abun haushi har ta gama murmushi ne yake saki.
Abun da ya fara sage mata gwuiwa kenan domin babu rashin mutuncin da bata juye masa ba a wannan lokacin mai gari ne kawai bata zaga ba har sunan dabba ta kira sa dashi amma sai dai fuskar sa babu alamar damuwa.
Tsaye tayi tana kumbure fuska cike da haushin masifar da ta gama.Ji take kamar ta tsinka masa mari ko ta yanke kan sa yadda ba zai ƙara ganin ta ba.
Ganin dai bazata taɓa rabuwa da shi ba ta hakan ba ya sa a hankali wata dabara ta faɗo mata ta sauke kan ta ƙasa tana ɗan sakin fuskar ta kafin ta ce.

" Yanzu dai muje dandalin ".

Tayi gaba tana haÉ—e rai tare da hararar shi ta gefen ido.
Chapter 76 · 0% Book details