Sashe 95
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
* " Hahaha Lallai ta baiwa ke Masifa ce,da sannu zaki ga yadda aikin mu ke ci ke shaida ce Ɗan Baiwa baya aiki kawai dan haka ki ƙara kwantar da hankalin ki wayen nan alamomi ne na cikar aikin mu ".Ya kai ƙarshen zancen yana gaggaɓan dariya.
Inda itama ta fara dariyar kamar wata zararrriya.
" Hankali na ya fara kwanciya Ɗan Baiwa buri na ya kusa cika komai ya kusa dawowa hannu na daga ni sai shi dole mu ƙara zage damtse a ƙara bawa su ɗan duhu jini su ji ƙarfi a jikin su su aiwatar da aiki cikin kuzari,nayi imani da kai ɗan Baiwa na san ba zaka taɓa bani kunya ba ".
Ta ƙara sakin dariya ta na kai ƙarshen maganar.
Cike da rashin imanin ta.
" Hhhhhh ta Baiwa kenan,kibar wuƙa da nama a hannun mu zamu ɗaukar Miki fan sa har da riba dole komai ya koma hannun ki ".
Miƙewa tayi kamar yadda suka saba tana zagin sa yana zagin ta kafin ta yi layar zana ta ɓace ɓatt.
Æacewar ta shima ya É“ace É“att kamar bukkar sa bata taÉ“a zama wajen ba.
" Ummah jiya fa mafarki nayi mara kyau akan LEENA amma na manta wallahi Ummah ina dai tuna kukan ta ne da na ji "
Reena ce ke zancen idanun ta na cika da hawaye.
Idanu Ummah da ke kallon ta zuba mata wadda ke kallon ta bayan fara maganar.
Numfashi Ummah ta sauke cike da ƙaryewar zuciya ta " Ta ce ki yi mata addu'a Allah ya bata lafiya da ke baki ɗaya,amma wane irin mafarki ne kika yi haka " ?
" Na faÉ—a Miki Ummah na manta fa ".
Kai umma ta girgiza kawai zuciyar ta cike da rauni kafin a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana furtawa a fili Allah ya baku lafiya ya ya na.
Amin Reena ta furta tana gyara zaman ta kan doguwar kujeran da take kai wadda take kallon ta Ummah.
Dai dai nan LEENA ta fito tana ya mutsar fuskar ta da ke nuna har yanzu tana jin jiki sai dai akwai alamar sauƙi ya fara samuwa itama.
Zama tayi kusa da Ummah tana shagwaɓe fuska.
" Ya jikin na ki " ?
Ummah ta faɗa tana taɓa wuyan ta.
Jin da zafi sai dai ba sosai ba hakan ya sa ta jan ajiyar zuciya tana ƙara rungume ta jikin ta bayan ta gyaɗa mata kai.
" Aleena ya jikin ki "
Yar hararan Reena tayi jin ta kira ta da complete name na ta kafin ta rufe idanun ta tana ƙara ya mutsar fuskar ta.
" Ummah Leena itama ta fara samun sauƙi ko " ?
Kai Ummah ta gyaɗawa Reena wadda ta ƙara yin tambayar ta kulawa da yar uwar ta.
Dai dai nan Abba ya shigo wanda ya dawo yanzu daga office.
Dan yanzu ya fara samun damar leƙawa kwana biyu ciwon ya yan na sa ya tayar masa da hankali matuƙa.
Ɗauke da murmushi akan fuskar sa ya zauna kusa da Reena yana ƙara ƙawata fuskar sa bayan amsa masa Sallamar sa.
" My babies sun samu lafiya ".
Cike da murmushi Reena ta ce " Eh Abba mun samu lafiya, Leena ce kawai yanzu take ɗan jin ciwon kan ta ,Amma itama Ummah ta taɓa jikin ta temperature na ta ya sauka."
Murmushin Abba ne ya ƙara faɗaɗa cike da jin daɗi ya shafa kan Leena yana furta " Allah ya ƙara muku lafiya ya kare ku daga sharrin maƙiyi da sharrin Aljan da duk wani abun cutarwa da muke gani da wanda bama gani ".
" Amin " Reena da Leena suka haɗa baki wajen faɗa dan suna matuƙar ƙaunar Addu,an Abba haka ma Bilal da ya shigo yanzu ya amsa a hankali yana sakin ɗan murmushi.
A ɓangaren Ummah kuwa ido ta zubawa Abba kafin ta sauke kallon ta daga kan sa tana Amsawa da Amin ganin yadda ya ɗan faɗa wanda sai yanzu ramar ta ƙara fita.
Ajiyar zuciya ta sauke yar ƙarama tana shafa kan Leena.
" Barkan ku da yini,Ummah da Abba "
Cikin sakin fuska Ummah ta amsa masa kafin ta ƙara sakin murmushi na jin yar kunya.Jin Abba na kiran " Momyn Yara yau babu sannu da zuwa ga masoyi sai ta ya yan ki kike yi ".?
'' Ya jikin Leena É—in ".?
Ya ƙara faɗa yana ta sowa daga kujerar da yake kusa da Reena yana komawa zuwa kusa da ita.
" Sannu da dawowa,Abban su,Leena ta samu lafiya itama ".
" Murmushi yayi ganin yadda Ummah ke soke kai kafin ya shafa kan Leena yana dawo da ita jikin sa fuskar ta ya shafa a hankali yana ƙara jin Tausayin ta na ƙara mamaye sa musamman da ya ji ɗan zafi a jikin ta sai dai bai kamar na ɗazu ba da safe.
Idanu Leena ta ɗan Lumshe kamar mage tana ƙara shigewa jikin Abba kafin ta ce a hankali " Abba sannu da zuwa ".
" Yawwa ya jikin,?kin samu lafiya ko "?
Kai ta gyaÉ—a masa tana sakin gun tun sanyayyen murmushi.
Kan ta Abba ya ƙara shafawa kafin ya sakar mata kiss a goshi.
Yana cewa." Allah ya baku lafiya ".
Amin suka haÉ—a baki wajen faÉ—a.
Miƙewa yayi ya haye Sama bayan ya gaisa da Bilal ɗin da sai yanzu suka haɗu shima dan da wuri ya fita shima ya fita wajen motsa jiki.
" Babu komai a tattare da su kamar yadda na faɗa maka,amma dai abun da kawai zan ce maka shine ku ƙara da gewa da Addu,a akan su nima a ta gefe na zan dage sosai dare da rana zan taya ku nema musu kariya wajen Ubangiji,yanzu ƙuruciya kawai ke damun su ".
" Ungo wannan ka ba su,su sha sannan kuma ka tabbatar ka shafa wa kowaccen su a kai da ƙafafu ".
" Kar ka yarda da kowa yayi wannan aikin ka tabbatar kayi shi da kan ka "
Sallamar Ummah ce É—auke da jakar sa a hannu ya sa shi dawowa daga duniyar tunanin da ya shiga na zantukan malam Hambali dan yanzu daga wajen su yake daga office ya wuce chan har yanzu kalaman malam suna masa shawagi "Babu komai a tattare da su ....."
Shin me hakan ke nufi kenan akwai wani abu a ƙasa sannan me zai saka malam yin wayen nan zantukan " Ka tabbatar kayi shi da kan ka ....."
Numfashi ya sauke da ajiyar zuciya bayan zaman Ummah É—an kusa da shi kaÉ—an.
Zuba masa ido Ummah tayi ganin yadda ya yi shiru kamar ya ƙara komawa duniyar tunanin da ta same sa.
Numfashi ta sauke kafin a Hankali cike da yar damuwa ta ce " me yake damun ka Abban yara ".
Murmushi Abba ya ƙaƙalo kafin ya ce
" Babu komai Barry kawai dai ciwon yaran chan ne yake damu na,ina tsoron wani abu ya same su ".
Hawaye ne ya wanke fuskar Ummah cike da wani irin raunin ta dake bayyane ta ce " Abban su,ka cire damuwa komai zai wuce,zasu samu lafiya,sannan duk wasu rigimar su zasu daina ".
" Kune ƙwarin gwuwaita Abban su dan Allah ku daina sage mini gwiwa ".
Ajiyar zuciya Abba ya sauke yana ɗan samun sanyi a ran sa,ko ba komai ya samu ƙwarin gwiwar da ya ke jin yana neman rasawa.
" Kar ki damu Barry,amma akwai wani hanzari wai Ni kaÉ—ai nake hasashen yaran nan kamar akwai sihiri a jikin su ".
" Tunani ne ke faɗa mini hakan Barry na kan ka sa yardar wa kai na babu wanda ya ke bi mini ya ya da bita da ƙulli ".
Wata irin faɗuwar gaba ce ta saukar wa Ummah cike da tsoro ta ce " Abban su Sihiri me za,a tsinta a jikin ya yana,me suka yi wa wani babu abun da suka sani fa,bamu da wani maƙiyi Abban su,kai gaskiya Abban su Wannan hasashe ne kawai Dan Allah Abban su ka daina irin wannan maganar wallahi ka tayar mini da hankali innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un "
Ta kai ƙarshen zancen tana fashe masa da kuka.
Jikin Abba ne ya ƙara yin sanyi ya ji dama bai yi maganar ba a hankali ya ɗan rungumo Ummah jikin sa ya fara rarrashin ta.
"Ba cewa nayi Dagaske ba hasashe na ne kawai,kuma sai yanzu na tabbatar da hasashe na ba gaskiya bane domin kuwa bamu da wani maƙiyi bare su na fili da na ɓoye duk abinda kika faɗa ba gaskiya ne".
" Allah ya basu lafiya,ya sa komai ya zamo muna tarihi mu da su,ya dawwamar da mu cikin farin ciki ".
Amin Ummah ta faÉ—a a hankali bayan tsaida kukan na ta.
Tana share hawayen ta tare da sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
" Zamu kai kukan mu ga ubangiji a koda yaushe mu masu miƙa wuya ne,dan haka Abban su ka ɗauka jarabawar mu ce wannan mu da su,Amma bana son ka raunata imanin ka ta hanyar yin wannan hasashen Abban su,Shekaran jiya ma na saka anyi musu saukan Alqur'ani,yanzu ma zan bada kuɗi a ƙara musu wata ".
Murmushin Abba ne ya fito da wani irin farin ciki ya washe fuskar sa daga damuwa.
Hannun ta ya riƙo a hankali yana fuskan tar ta kafin ya ce " Allah yayi Miki albarka Barry,Allah ya saka Miki da Alkhairi ya ƙara Miki ƙarfin renon ya yan mu da basu tarbiyya ".
" Amin " Ummah ta amsa tana sakin murmushi.
Jakar ta sa ya amsa bayan ya miƙe daga zaunen ya saka ta inda yake ajiye jakar sa.
Tuno da abun da malam yace masa dan haka ya tura jakar cikin lockern sa kamar yadda Ummah ta saba yi masa.
Kallon sa ta dinga yi ganin yau da kan sa yake ƙokarin ajiye jakar ta sa.
Kafin ya ta ce " Abban su Yau ko kayi mantuwa wannan ba aikin ka ba ne ".
Murmushi Abba yayi yana juyowa kafin ya ce " kar ki damu na ga kina gajiye ne ga kula da marasa lafiya shi ya sa na ke ƙokarin yin komai da kaina ina son ki huta ne ".
Murmushi ta ƙara saki na jin daɗi.
Wanka ya faÉ—a yana furta" bari na shiga na sake jikin nan nawa".
Kai Umma ta gyaɗa kafin ta miƙe ta fice kasa wajen haɗa masa abincin sa,ta san Abba baya wa sa da cikin sa.
A ɓangaren Abba kuwa bai daɗe ba ya fito daga cikin toilet ɗin tsaf ya kimtsa cikin kaya mara sa nauyi na zaman gida.
Jakar sa ya janyo kafin ya Fiddo da yan gorunan ruwan addu,an da malam Hambali ya ba shi.
Zuba masu idanu yayi gora biyu ce ciff yanda malam yace a ba su na kwana biyu.
Har ya É—auki É—aya ya fita da ita sai ya tuna maganar malam hakan ya sa ya mayar da ita cikin jakar yana ficewa daga É—akin.
A ɓangaren Bilal kuwa bayan wucewar su Ummah cike da yar kulawa ya dubi Leena.
Yace " Y jikin na ki ".Naji sauƙi. Ta bashi amsa.
Daga haka bata ƙara cewa komai ba sai shigewa cikin kujera ta ƙara lafewa lafe.
Ita kuwa Reena jikin shi ta shige tana cewa " Ni ya ya B baka mun ya jiki ba ".
Ɗan guntun murmushi ya saki yana kallon fuskar ta da tayi fayau kafin ya ce '' Na ga ba kya buƙatar tambaya ne Reena,gashi kina da ƙarfin jikin ki har kin samu damar surutu ".
Ya kai ƙarshen zancen yana shafa kan ta.
Yar dariya tayi tana cewa " eh na ji sauƙi y B "
A wannan karon murmushin ya ƙara saki kafin ya ce " Ta ci abinci ".
Fahimtar wadda yake magana hakan ya sa ta ce " Eh ta ci chocolate,kuma tace ta ƙoshi haka ta cewa Ummah ".
Kai ya gyaÉ—a kafin ya ce " Je ki Kice wa Inna Rabi ta haÉ—o mini tea mai kauri ".
Miƙewa Reena tayi jikin ta sanyaye dan har yanzu da Sauran rashin ƙarfi a jikin ta itama.
Dai dai fitowar ta dai dai lokacin da Ummah ta ke saukowa daga step steps fuskar ta babu yabo babu fallasa.....
Sai dai fuskar ta kamar da danshin ruwa da alama sai da ta shiga bedroom É—in ta,ta wanko fuskar ta.
Kallon B tayi dake zaune ya zuba wa Leena idanu yana kallon ta wadda idanun ta ke rufe da alama bacci ya fara kwasar ta.
Ɗan jimm tayi kafin ta karasa saukowa tana giftawa ta gaban sa hakan ya sa ya ɗauke idanun sa kan ta yana jin wani mugun tausayin Ƙannen na sa na sukar zuciyar sa.
Zama Ummah tayi kafin ta shafa kan Leena ta ce " Baiwar Allah ta fara samun barci ".
Kai B ya gyaÉ—a kafin ya ce " Ashe bata ci abinci ba ".
" Eh wai ta ci chocolate ta ƙoshi ".
Ummah ta bashi amsa.
" Ummah Chocolate ai ba zai yi ba shi ya sa jikin na ta ya ƙi yin ƙarfi ".
" To ya za,ayi Soja basa jin dadin komai ne itama Reena da ƙyar ta yarda ta ci coslow ko shi kaɗan ".
Reena dake zaune ce ta ce " Ummah ai na ƙoshi ".
Kai Ummah ta gyaɗa mata tana Murmushi kafin ta ce wani abu sai ga Inna Rabi ɗauke da cup a kan ɗan ƙaramin ti re mai kyau.