Sashe 89
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri wannan mopol ɗin ya matso yana jin sanyi a ran sa na damar da yake shirin samu ya yiwa yar ƙaramar yarinyar da bata wuce gwiuwan sa ba hankali. MAHAJ kuwa gyara zaman rado ɗin sa yayi yana ƙara tsuke fuskar sa. Muby ne cike da sakin fuska ganin yadda mopol ɗin nan ke ta ƙara haɗiye rai haka ma uban gidan na sa duk da ya san ba lallai ya aikata abin da ya faɗa ba. " Haba Malama Shatou dan Allah ki matsa mu wuce mai gida na baya son rana tana saka shi zazzaɓi yanzu haka in kin lura ya mutsar fuska yake yi ki taimaka mana ba sai an kai yadda ba,a so ba kar jama'a su tarar mana nan " Ya kai ƙarshen zancen yana haɗiye dariyar dake neman kubce masa ganin yadda take ta hurar hanci da girgiza ƙirji da Harare kamar zata zubar da idanun ta kuma duka akan sa ne kafin ta koma kan Mahaj dake tsaye hannayen sa maƙale a cikin aljihun sa.Ba zaka iya tantance ainahin yanayin da yake ciki ba sai dai fuskar nan a haɗe take dan ya gaji da lamarin shatou.A ɓangaren Bibu kuwa ganin bata saurare sa ba dan fisge hannun ta tayi tana ce masa barni ka tafiyar ka sai na ga karshen rainin hankali, hakan ya sa ya bar wajen da sauri yana haɗawa da gudu wanda da alama wani zai kira ya raba wannan rigimar. " Wannan ne uban gidan naka,wannan ɗan Yaron ko ni fa na girme sa kawai dan bana girma ne shi ya sa yafi ni zama ƙato,kuma ma na tuna Bature ance dama haka suke girma kamar biredi hhh " ta kai ƙarshen zancen tana nuna Mahaj tare da ƙara sakin wata yar dariya ta yarinta da rainin wayau da sakarci. Baki sake Mopol ɗin da ke jiran izini yake kallon ta haka ma Muby sai da ya ƙwalalo idanun sa yana kallon ta tare da furta anya wannan ba aljanna bace a ran sa ga dariyar dake ƙara ta so masa ji yake ina ma a ce Abbu yana kusa ya sha kallon wannan dramar ta su. Ɗan satar kallon MAHAJ yayi da yake tsaye kamar bai san abinda ake yi ba dan ya ma juyar da kan sa gefe ya san cewa ran sa ya fara ɓaci ne sai dai yana ƙoƙarin shanye wa dan shi mutun ne mai shanye komai ba kasafai kake gane yanayin sa ba musamman ma yanzu da shatou ta zamo mace babu yadda zasu yi da ita dan shi kawai yake lallaɓa ta. " Kai dube ka garjejen ƙato da kai kake kiran wannan abun mai gidan ka chab " Ta yi zancen irin bani da damuwa da kuma mamaki. Wannan karon muby murmushi ya saki wanda ya fi na ko yaushe sannan ya ce " Ba wannan ba dan Allah ki yi Haƙuri ki jaye gefe mu wuce ". Ƙugu ta ƙara dafewa tana hararan Mahaj. Musamman ganin yadda ya ɗan saka hannun sa akan sa ya cire p cap ɗin sa. Sai kuma ya taka gaban ta a hankali wanda ya zamo ɗan tazarar dake tsakanin su dan kaɗan ne. Sai da ya ɗan mula hannun sa ɗaya a aljihu.Ya ɗauki mintuna biyu tsaye gaban ta.Ita kuwa shatou baya ta ɗan ja kafin ta furta " Wallahi Ni ba yar iska bace dan haka ka matsa,ko in fasa maka kai da dutse " ta duƙa ta ɗauki dutsen. Ƙara takawa yayi inda take dan ganin ƙarshen iskan cin na ta. Baki ta tura gaba bayan ta zuba masa ido Ganin kammanin Abbu Mutumin kirki ƙiriƙiri a gare sa dan tun ɗazu ta ke hango su wanda sai yanzu ta ƙara ganin su bayyane saboda kusan cin da suka samu,kuma ta tabbatar lallai ya yan sa ne dan shima fatar ta su ɗaya ce sai dai a yanzu ta mahaj tafi ɗaukar ido,ɗauke idanun ta daga kan sa tare da hararar sa ganin sa gaban ta a karo na biyu kafin ta ankara wanda sai da ya ɗan razanar da ita sai dai ta haɗiye dan a cewar ta bata tsoron girman biredi,Cikin zuciyar ta,tayi zancen sai dai bata san cewa ta fito fili ba sak haka maganar ta shiga kunnen sa " Ni bana tsoron Girman biredi ". Kafe ta yayi da idanun sa ta cikin glass ɗin sa kafin ya ja ƙaramin tsaki da ya sauka kan kunnen Shatou.Wanda ya sa ta ƙara maka hararan da tafi sauran. " Ai watar da abun da kike shirin yi " Haka zancen sa ya shiga kunnen ta cike da wani irin isa da kaushin dake nuna ya fara gundura da tsayuwar ta su. " Zan jefa ka ". Ta faɗa tana hararan sa tare da turo baki gaba. Glass ɗin sa ya zare a hankali tare da mayar da hulan sa a kan sa yana zuba mata idanun sa wayen da ya kafe mata har tsakiyar kai yana ƙare mata kallo a fakaice. " Zan jefe ka fa,ka matsa kafin na ƙirga goma " Ta kai ƙarshen zancen tana rufe idanun ta. " Ɗaya,Biyu,uku,huɗu Biyar..." Ɗan buɗe idon ta ɗaya tayi ganin ko ya matsa sai dai yana nan tsaye kamar dutse ya zuba mata idanun na sa. Haɗa idon da suka yi ne ya sanya ta ƙara tura bakin ta gaba tana buɗe idanun na ta gaba ɗaya, hannun ta ta ɗaga kamar zata jefa masa dutsen. Sai kuma ta saki ɗan guntun murmushi wanda ya bayyanar da yar ƙaramar wushiryar ta, murmushin kai da gani ka san akwai Zallar ƙuruciya kan ta babu Damuwar komai a kan ta kamar ma ta mayar da komai shirmen ta. Ɗauke kallon sa yayi daga kan ta a hankali yana lumshe idanun sa kafin ya ware su Dai dai nan kuma Baffa na ya ƙaraso wajen wanda ke cike da tashin hankalin labarin da Bibu ya kai masa yana kuka kashirɓan ga Addan sa chan zata yi faɗa da mutanen birni zasu kashe ta. Sai dai yana ƙarasowa wajen ganin Muby sai ya ɗan yi jimm yana kallon sa dan ya gane sa tun da tare suka zo kwanan baya da Abbu, kafin ya mayar da idanun sa kan MAHAJ dake tsaye yana kallon ƙasa kamar mai nazari. Yan ƙafafun Shatou yake kallo yan ƙanana da su da suke da ɗan datti a cikin silifass ɗin ta,Wani murmushi ne ya nemi suɓuce masa sai dai ya hanawa kan sa hakan. Ita kuwa shatou dutsen ta yar ƙasa bayan ɗan juyawan da tayi ta kalli Baffa na dake tsaye yana kallon MAHAJ bayan sun haɗa ido da ita. " Ka ci sa,a Baffa na ya zo wajen nan,Sannan da kuma kaci sa,ar ya yan ka mai mutunci da kamar da kuke yi da sai na fasa maka kai gobe ba zaka ƙara raina ni ba ka zata na manta abun da ya faru ko wai har ni zaka kalla kace mini yarinya,kuma kai da ke bilicin Ni zaka cewa nake yin bilicin ai da ganin ka an san farin bilicin ko ka zata ban san yan bunni na bilicin ba ai Baffa na ya bani labari akwai masu farin mai kuma kaima shi kake shafawa ji fa fatar ka kamar ƙosan iya " Ta kai ƙarshen zancen tana ƙyaƙyata dariya. Idan ba kuskure yayi ba ya ga alamar murmushi akan fuskar sa wanda sai idan ko lura sosai ne zaka iya fahimtar hakan. Dan haka ya zuba ma Uban gidan na sa ɗan uwan sa ido. Ga mamakin furucin Shatou wanda ya tabbatar ba kowa take nufi ba face Abbu shi take kira da ya yan sa.Lallai wannan yarinya Boss ce ya furta a cikin zuciyar sa yana sakin murmushi. Numfashi ya ɗan sauke Da ke nuna gajiyar sa dake bayyane kafin ya ɗan ja baya kaɗan bayan ya samu haɗa ido da Baffa na da ya zuba masa ido yana Kallon sa kamar ya samu tv.Ga shirmen Shatou da shiga kunnen sa wanda ya ji kamar ya kame bakin ta ya hana ta yin furucin wanda har nauyi tasa ya ji bayan wanzuwar sa wajen. Kan sa ya ɗauke daga kallon kowa kafin ya kalli wannan Mopol ɗin ya furta masa " is Okey let her be ". Cije baki mopol ɗin nan yayi wanda kafin yanzu ya yardan wa kan sa shatou bata da lafiyan ƙwaƙwalwa daga yanayin yadda take abubuwan ta. Dan haka sai lamarin na ta ya so ba shi dariya dan har wani kaso daga Haushin ta ya ragu ganin wanda yake yi dan sa ko ajikinnsa kamar ma yana biye mata su yi ta ƙuruciyar tun da duk kamar sune. Mota ya koma tare da sauran da suka zagaye su jira kawai suke yi a basu dama su yi wani abu akan Shatou. Juyawa tayi ta kalli Baffa na ta yi Murmushi tana barin wajen tana komawa gefen Baffa na ɗin. Ajiyar zuciya MAHAJ ya sauke tare da ɗan shanye narkakkun idanun sa yana kallon Shatou da take ta ya mutsar gashin Bibu tana dariya kamar har ta manta da rigimar da ta gama Badan komai take yi masa haka ba sai dan ganin yadda yake cikin tsoro kamar zai yi wani kuka har yanzu a tsorace yake yana zaton wani abu zai same ta ne kafin su iso. Kallo ɗaya yayi musu ya ɗauke idanun sa kan su. Juyawa yayi a hankali ya fara tafiyar sa cikin ƙasaitar sa da natsuwa sai dai ko tako biyar bai yi ba ya juyo a hankali ya ɗan saci kallon Baffa na kafin kuma ya juya ya cigaba da tafiyar sa ko kafin ya isa bakin motar wani ya buɗe masa da sauri. Shigewa yayi suka rufe sa.Jingina bayan sa yayi da seat ɗin yana sauke Jerarrun Ajiyar zuciya tare da numfashi kan sa ne ya ɗan sara masa na gajiyar magana da tsayuwa cikin ranar da yayi.Wani madanni ya danna a hankali inda ya buɗe wata yar ƙofa sai ga drinks ɗin sa wayen da suke favorite na sa a ciki sun ɗauki sanyi mai yawa.Dan wajen kamar fridge ne. Ɗaya ya ciro kafin ya zuba masa ido kamar mai karantar wani abu a cikin sa,Har ya