← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 110

Sashe 10

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shiru Inna ni tayi kamar ruwa ya cita kan ta ya rufe ɗiff sai kuma cikin ɗan murmushin da ta ƙaƙalo ta furta " Ai Ni shatou na tsufa baki ga harda furfura ba a kaina,kuma kin san tsofaffi basa haihuwa ".

" Laaaah Dagaske Inna ni ai Ni ban taɓa ganin ta ba,Inna ni kan ki fa baƙi wulik yake ai ina buɗe shi na taɓa wata rana idan kina bacci saboda daɗin taɓa sa nake ji taushin sa kamar kayi ta bacci ".

Waro idanu Inna ni tayi tana sauke ajiyar zuciya da firar ta su ta sauya.
Kafin ta furta " Ohh ni Indo gashin nawa ke saka bacci kuma Shatou,ai ga naki nan da baki son a taɓa sai ki riƙa taɓa shi dan naki yafi nawa taushi nesa ba kusa ba kawai na wa kika zuba ma ido ko,zan ma aske shi saboda ke ".

" Wallahi Inna ni ba zaki aske shi ba ki saka naji kunya har fa labarin shi na ke bawa su Amina ko ".

Kai su Amina suka gyaɗa suna murmushi dan suna shan labarin jin yadda gashin Inna ni yake da silɓi wanda suko suke ganin bai kai na Shatou ba saboda akwai ranar da ɗan kwallin ta ya cire bayan sun yi dambe da wata yar aji biyar ta yaga mata hijabi har ɗan kwalin ta ya cire wajen Masifa daga nan suka san shatou ma nada gashi dan bata son ana ko taɓa kan na ta bare a ga abun da ke cikin sa kitso daƙyar inna ni take ma ta shi kuma bai wuce kalaba itace kawai ta iya.

Dariya Inna ni tayi wadda ta ƙara bayyanar da kamar ta da shatou har yar wushiryar su ma iri ɗaya ce.

Itama shatou murmushi tayi mai haÉ—e da dariya ganin dariyar Inna ni wadda ba kullum take yin ta ba.

" Inna Dan Allah a bar maganar wasa kar ki aske shi wallahi kika aske shi ba zan ƙara fita ƙauyen nan ba dan gori za,a mini ace Inna ta Tal kwabo gare ta ".

A wannan karon Inna ni daƙuwa ta jefa wa Shatou tana dariya.
Itama shatou dariya tayi tana chafke daƙuwar tana shigewa cikin su Amina da suke ta dariya suma gwanin burgewa ganin yadda shatou ke wasa da mahaifiyar ta.

" Allah ya shirye ki Shatou ya baki hankali "

Inna ni ta furta tana girgiza kan ta Dan ta fahimci idan ta biye wa shatou haka zata lalace wajen.
Shigowar Bibu ce ɗauke da Sallama a bakin sa ya dakatar da su da dariyar da suke yi.Zama yayi cikin su cikin farin ciki yana furta " Adda shatou kin ji sauƙi sosai naga kina farin ciki sosai,Naji daɗi ".

Dariya tayi tana furta " Naji sauƙi sosai Bibu baka ga har ƙiba na ƙara da girma ba " .

Dariya yayi sannan ya ce " Wallahi Adda SHATOU ba wata ƙiba kin ga yadda kika rame,girma kuma ai kince bakya son ki girma,dan Baffa na ya ce kar na miki addu,a da sai na Miki Addu,a ki zama Saratu Wada ".

Ai ko su Amina me zasu yi in ba dariya ba ganin yadda ta bata fuska saboda sun san yadda ta tsani sunan.Bibu kuwa shima dariyar yayi yana tserewa bayan Inna ni yana furta Inna Barka da aiki ".
Amsa masa tayi tana furta" Sarkin jan magana ko Allon an kasa ajiyewa sai tsokana na san da ba kai bane da wani ne yake haɗa wacchan rigimammar da saratu da tuni wani zancen ake yi ba wannan ba" ta kai ƙarshen zancen tana kallon shatou dake Hararar Bibu kamar idanun ta zasu faɗo.

Dariya yayi tare da tsalle yana furta " Sai ni na Adda SHATOU guntuwa ".

Yana gama furucin ya shige É—akin sa da gudu yana dariya.
Har ta miƙe,kuma ganin cewa in ta biye masa haka zai ta ƙara kiran ta ya sa ta dawo ta zauna tana dariya tana furta " Ai in ba tsoro ba mutun ya zo ya faɗi gaba na ".

Inna ni ce ta karɓe zancen tana furta " Ai maza ba sa tsoro,bare Habibullah na ai jarumi ne ".

Baki Shatou ta turo gaba bata ce komai ba.
Inna ni kuwa murmushi tayi kawai tana cigaba da yin aikin ta.Tana jiyo dariyar Bibu daga ciki.Sai taji sanyi dan hankalin sa tashe ya bar gida sai gashi daga shigowar sa ya samu nishaÉ—i.

Su shatou kuwa firar su suka cigaba da yi kamar babu abinda ya shiga tsakanin su.

Daga ƙarshe ma Inna ni aka tashi aka ƙara ƙalƙalewa gida.Ita kuwa sai kallon su take yi tana murmushi cike da wasu irin tunani ka iri iri.

***GTR👑👑👑

Kafin fitowar ta su wajen lunch ɗin sai da aka kusa yin dambe saboda LINA bayan gama yin wankan ta ƙin fitowa tayi daga toilet ɗin saboda dama tana shiga chan ta yi tsinke,Jin shiru ya san ya REENA buɗe toilet ɗin kai tsaye dan babu motsin ruwa.
Zaune ta isko LINA gaban madubin toilet ta na ta kallon kan ta tana Murmushi tare da jan dogon gashin ta da ta jabga ma ruwa yanzu.
Cike da haushi ganin jikin ta ya ma bushe tana É—aure da towel tayi zaman ta gashi Ummah tace su fi to da wuri saboda ya'yan su,amma ita har ta zama ta bata kamar ba É—azu a school ta gama faÉ—ar yunwa take ji ba bayan ta gamo faÉ—ace faÉ—acen ta.

" Mutun ba wani kyau ba sai iyayi ".
Tayi furucin tana nufar inda set na towel ɗin su suke jere gwanin burgewa.Ko ina tsafff ba zaka taɓa cewa ƙananan yara ke aiki dashi ba,saboda yadda ake kula da tsaftar su.Komai na su tsaf dashi.

" Damar abun kamar mu É—aya idan ma rashin kyau ne Kinga har ke baki da shi ".

LINA tayi furucin tana wani juya ido gaban madubi tana mayar da gashin ta baya kamar wata ba indiya.
Sai kuma chan kamar an dawo da sense nata ta ta so da sauri tana yowa kan REENA tana furta " Uban wa ne mai iyayi " .

" Wallahi da ba Abba zan zaga ba da sai nace uban ki ".

" Hehehe " tayi wata irin dariya ta na yaƙunar fuska sannan ta ƙara furta " wallahi kin zagan kuma Abba ya dawo sai na faɗa masa,Wawuya kawai ".

Take idanun REENA suka cika da hawaye baƙin cikin ta ɗaya kalmar Wawuya da LINA ke yawan kira mata bata son ta ko kaɗan Dan bata ga inda take wawanci ba amma abu kaɗan sai LINA ta kira mata wawuya abun na ƙona mata rai dan tun bata san ma, anar kalmar ba har ta gane ba mai daɗi bace.

" Wallahi ma rufa Miki da nayi sai na faÉ—a ma Yaya Kin tafi yawo bayan an tashi breakfast,har sai da aka kusa tashi kika dawo ".

Zaro idanu LINA tayi kafin ta zo da sauri tana marairaice wa kamar ta duƙa ma REENA tana furta " Ki rufa mini asiri ba zan ƙara ce Miki Wawuya ba REENA "

Murmushi REENA tayi abun ka ga zuciya mai sauƙi take ta ce " ai ba zan faɗa masa ba na rufa Miki,da zan gaya masa tun ɗazu ai da na faɗa masa ma ".
Numfashi LINA ta sauke har da dafe ƙirji
Dan wasu maza tayi dambe dasu su uku bayan school kawai dan sun yi Gulmar ta maganar ta dawo kunnen ta shine ta aika musu da saƙon su haɗu lungun kaci uwa ka idan basu tsoron ta wanda da ƙyar wani security na su ya raba faɗan har suka bashi cin hanci ganin Dagske zai kai report wa school a hukunta su sannan a kira iyayen su.

Gaba tayi zuciyar ta na yin sanyi tana fatan kar wata rana Surutun REENA ya tashi ta faɗa ta san ranar sai ya kakkarya ta tayi faɗa da maza ko matan ya ta ƙare in zancen ya zo kunnen sa.

" Ummah ta ce mu fito da wuri muyi lunch tace har ke ki fito kuma ".

Tana gama sauraren zancen na REENA ta fice daga toilet ɗin tana yatsinar fuska ganin kamar an takura mata dan bata so fita ba, ta so akawo mata abun ta nan hankalin ta kwance amma yanzu da ta haɗa ido da Ya B. Ta san Harara ce zata ƙosar da ita.

Ta shirya da wuri amma itace last fitowa dan zaman ta tayi sai da tayi ta tunanin zaman dinning saboda ta san haushe yake da ita tunda gaban shi ta daki yar gaban goshin sa, gashi bata da gaskiya ganin take ko wane irin lokaci asirin ta zai iya tonuwa dan ta san REENA gaɓa ce wata rana tsafff zata iya kawo zancen idan fira tayi daɗi.
Chapter 10 · 0% Book details