← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 110

Sashe 73

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

" Eh dama ina son maka magana ne akan aikin ƙauyen su yarinyar chan Shatou mutuniyar ka ".
Wani irin kallon ban fahimce ka ba Mahaj yayi masa.
Kan sa ya shafa ganin kamar bai gane ba saboda sunan da ya ji ya ambata,duk da kuma sarai ya san wadda yake magana yana ji a jikin sa ya fahimce sa.Rainin hankali ne kawai.
Idanun sa ya ƙara zuba masa alamar ƙarin bayani.
Dan haka ya furta " Yarinyar da kuka yi faɗa da ita a zuwan mu ƙauyen a wala ".
Idanu Mahaj ya lumshe irin dai yadda kuka san yanayi kafin ya buɗe su tar akan Mubeey ɗan kallon sa yayi na daƙiƙa kafin ya ɗauke kallon sa kan sa yana sauke ajiyar zuciya tare da ƙara shigewa cikin kujerar kamar wani Basarake.
Mubarak kuwa fahimtar cewa ya fahimce sa ne ya sa ya cigaba da magana yana sakin guntun murmushi yadda yake tuno badaƙalar su.
" Aiki ya fara,komai Abbu ya saka hannu an gabatar ranar ma mutuniyar ka wani ya jogano ta ta kai shi ƙara gurin mai gari tana ta kuka ".
Kalaman Mubarak yake saurare da farko ya mayar da hankalin sa kan sa sai dai jin sunan mutuniyar ka da ya maimaita masa ya kuma tabbatar da wadda yake cigaba da alaƙantawa dashi hakan ya sa ya miƙe yana Jefawa Muby wani irin kallo kafin ya ja mugun tsaki yana furta " ka daina alaƙanta ni da wanchan stubborn girl ɗin ".Yayi zancen iya kan laɓɓan sa kamar baya son Mubeey ɗin ya ji shi ko Mubarak sarai ya ji shi dan haka yayi kamar bai ji ba ya ƙara ɗaga murya yana furta " Tayi ta neman ka ".
Chak ya dakata daga tafiyar da ya fara domin lamarin Mubarak ya fara shige masa hanci ya fahimci kamar ya fara wuce masa gona da iri duk da wasu lokutan haka suke saboda sabon da ke tsakanin su.
" Tayi ta auna mini harara,tana É—aga kai ganin inda zata gan ka ".
ÆŠan lumshe idanun sa yayi kafin ya janye daga kan mubeey da ya É—an waiwayo yana kallo.
Shi ko mubeey ganin kamar kallon na sa na neman ƙarin bayani ne hakan ya sa ya cigaba da maganar sa.
Ƙaramin tsaki ya ƙara jaa kafin ya bar wajen cikin ɗan sassarfa.
Mubeey kuwa ƙaramar dariya yayi yana cigaba da kallon sa hankali kwance haka kawai yake son ƙara ganin haɗuwar MAHAJ ɗin da shatou.
Kayan jikin sa ya tuɓe duka kafin ya shige haɗaɗɗen toilet ɗin,tun da ga sama har ƙasa ruwan yake dukan sa bayan tsayuwar sa wajen sabod Shower ɗin irin na'urar nan ce mai amfani da tsayuwar mutun ne kana jayewa kuma zata ɗauke ta kashe kan ta.
Sai da ya ɗauki lokaci a cikin toilet ɗin kafin ya fito mayukan sa masu tsada ya murza ma jikin sa kafin ya sanya wasu kayan mara sa nauyi riga da wando yan Companyn apple rigar armless jacket ya ɗaura kai bayan ya ƙara gyara haɗaɗɗen gashin kan sa da be san adadin abun da yake kashe masa ba.
Turarukan sa masu tsada ya feshe jikin sa da su kafin ya fice daga bedroom É—in yana É—aura p_cap a bisa lallausan gashin sa.
Ƙamshin sa ne ya fara bayyana kafin isowar sa wajen dan haka Mubarak ya zuba ma wajen da zai ɓullo ido shi ɗin ne dai ɗauke da system a hannun sa sai tsadaddiyar wayar sa.
Kunnuwan sa duka biyun maƙale da Bluetooth fari ƙarr kamar kayan da ke jikin sa dan har Wandon irin buɗaɗɗen nan ne kamar pallazo sai dai shi guntu ne yayi kyau matuƙa kyau iya kyau.
ÆŠauke idanun sa yayi da ga kan sa.
Kafin ya miƙe ya zari keys ya bi bayan sa.
Kasancewar ya san bai wuce fita zai yi ba gashi Abbu bai son yana driving a cewar sa bai isa fara driving ba duk da ya san ya iya amma yana tsoron yadda dokokin ƙasashen ƙetare suke su,gashi ko kuskure basu sani ba kar wata rana ƙaddara ta hau kan ɗan gaban goshin sa dan haka ya ce Mubarak ya daina barin shi yana tuƙi duk da kuwa gwanewar da yayi.
Gaba ya shige bayan Mubarak ya buɗe motar wanda ya ke ƙara jinjina hali irin na MAHAJ yana haka i na ga nan gaba ya san maganar kurame zasu komawa yi gaba ɗaya.
" School Auditorium zamu je "Ya furta cikin muryan sa mai nuna yanayin sanyin sa.
Kai tsaye Mubarak ya fahimci inda yake nufi dan haka ya ja motar suna ficewa bayan wangale musu katon gate da aka yi.
Sunyi yar tafiya mai ɗan nisa kafin suka isa haɗaɗɗiyar makarantar ta su.SHINHWA University Babbar makaranta ce da take da manya manyan sassa kama daga primary secondary har zuwa tertiary,sannan makarantar biyu ce akwai ɗaya a Korea komai ɗaya da wannan bayan haka suna da sassan su a cikin zagayen Beijing da sauran garuruwan Ƙasar.
Makaranta ce ta masu kuɗi da mulki domin duk wani mai maiƙo yana cikin wannan makaranta.
Bakin Wani ƙaton Hall yayi parking.
Shi ya buÉ—e da kan sa kasancewar shi kaÉ—ai suke jira dan bai so zuwa ba ma amma saboda jin wani yanayi a jikin sa kamar kasala ya sa ya yanke shawarar zuwa wajen ko dan ya wartsake.
Shigar su wajen ne ya ƙara bayyanar mini da girman da wajen yake da shi waje ne mai Shegen kyau ya Tsaru iya tsaruwa komai na sa red kama da kujeru har zuwa curtein komai ya yi kyau ga wasu irin haɗaɗdun kujeru masu kyau,kai daga nin yadda komai yake tsare kasan makaranta ce ta manya board ɗin su ma abun kallo ne.
Tun da suka shiga ka fara jin shin shin na tashi a tsakanin su musamman Mubarak da ya fi sakewa.Abun ka da Chinese.Shi ko iya ka ya gyaɗa kan sa da ɗaga hannu ga wayen da ke ta faman furta masa nî háo?.(how are you)
A chan ƙasan maƙoshi kawai yake amsa wa da fine yana zama fuskar nan dai sai sa sai sa.
Haka suka fara gudanar da Rehersal Presentation É—in su saboda sun gayyace shi ne ko zai taimaka musu da wani abun duk da gobe ne za,a yi.
Mutun uku yayi yan China kafin ya miƙe kamar an masa dole yayi ya yi musu yan gyare gyare sannan ya rufe da xié xíe (Thanks you)
Dukkanin su tafa masa suka yi.
Godiya suka masa kafin suka watse taron cike da jin daɗi dan yana cikin ɗalibai masu ƙwazo sun san zai tallafa musu sosai duk da suma ba baya ba.
Wajen wani gidan shaƙatawa suka nufa bayan ya sanar ma Mubarak ɗin dake ta murmushin jin daɗi dan baiwa irin ta Mahaj na burge sa.
Ya san dole gobe ya burge manyan professors.
Sun jima wajen kafin ya gama hutawar sa sannan ya fito ya samu Mubarak da yayi zaman sa cikin mota ya ɗan kwantar da seat ya kunna ƙira,a yana saurare tare da bin babbar hanyar titin da kallo mai cike da tsari mai kyau kowa sai harkar gaban sa yake yi.
Yana shiga ya rufe motar hakan ya sa Mubarak sanin shigowar sa.
Babu wata magana yaja motar dan ba yau ya saba da halin sa ba.
Gida suka wuce direct koda suka isa ana kiran Salloli kasancewar dukkanin su da alwallan su ya sa kai tsaye suka shige masallaci ana gamawa kuma kowanne su ya fito dan mahaj ya riga fita ma kafin Mubarak..
Yau ko zaman falon bai yi ba ya zarce war sa sama.
Wayar sa ya zuba ma ido yana kallon ñumban Ayya da yayi kewar ta sai dai ya san ko ya kira magana ce mara daɗi zai samu kamar koda yaushe.
Numfashi ya sauke mai ɗan fita da hayaƙi na yanayin weather ɗin garin kafin ya danna mata kira.
Saboda Allah ya saka masa ƙalahucin Ayya Saboda ita ya buɗe ido ya gani uwa duk da rashin mutuncin da take masa yakan ji kewar ta,kuma bai cika ganin baƙin ta ba kan hakan dan ya san tana da dalilin ta wanda ya rasa gane dalilin da ya sa har yanzu da ya girma fentin bata goge masa shi ba,yana jin tana yawan saka mahaifiyar sa cikin zancen kuma ya san wata rana dole zai san inda Ayya ta dosa.
Laifin me kuma mahaifiyar sa ta yi da ta chanchanci yaɓin magana a gurin Ayya duk da cewa ta na ƙasa kwance.Idanun sa ne suka sauya sako wannan tunanin da yayi.Iska ya ɗan furzar kafin ya maƙala Bluetooth ɗin sa a kunnen sa.
Ringing daya ba,a É—aya ba sai ana biyu aka É—aga.
Shiru aka yi ta ɓangaren Ayyah kafin a hankali cikin Muryan sa mai sanyi ya furta " Ayyah Barka da dare ".
" Barka "
Ayyah ta amsa kamar an mata dole.

" Kin wuni lafiya " ?
Chapter 73 · 0% Book details