← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 110

Sashe 105

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Rarrashin ta matar ke yi cike da tausayin ta.
Sai da tayi shiru ne sannan ta sake ta ta juya ta ɗauko mata ruwa mai sanyi a cikin wani ƙaramin fridge dake a cikin bedroom ɗin ta ba buɗe mata.
Ruwan ta miƙa mata babu musu kuwa ta kafa kan ta a hankali ta sha dan su ta fi buƙata a yanzu,a hankali ta sauke a jiyar zuciya da numfashi a tare tana sauke goran a bakin ta jin sun ratsa ta ta ko ina.
Lumshe idanun ta tayi tana buÉ—e su.
Yaron da ke gaban ta da ya dunƙule waje ɗaya ta kalla wanda a ƙalla zai kusa kai shekara biyar a duniya.
Baccin sa yake sha hankali kwance kusa da ita dan ajikin ta ma rabin jikin sa yake.
Itama matar shi ta kalla kafin ta ce " Sannu mafarkin ne ? ".
Kai Budurwar da aka kira Alishat ta ɗaga kafin ta ce cikin natsatsiyar Muryar ta mai sanyi da taushi " Mamma me ya sa wannan mumman tarihi ya kasa barin idanu na da tunani na,me ya sa zan dinga mafarkin sa haka? ". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta yi shiru tana sauke numfashi jin wasu Sahabban hawaye na neman sauko wa tare da wani sabon kukan da ke bayyanar da ƙunar da zuciyar ta ke yi.
" Ki cigaba da Addu'a In Sha ALLAH daga wannan ba zaki ƙara yin sa ba da yardan Ubangiji,kuma hakan ba komai bane sai yadda tsoron yanayin ya shige ki,kuma ki yi ƙoƙari ki daina tunawa kar ki haifar wa kan ki wani sabon ciwo kin san dai yadda kike fama idan ciwon ya tashi ".
Matar da aka kira Mamma tayi furucin.
Ajiyar zuciya Alishat ta sauke kafin ta É—an shafa kan yaron da ya fara motsawa kasancewar lokacin sallar Asuba yayi ta zo ta tada yaron su wuce masallaci shida mai gidan na ta.Alhaji Sama'ila da suke kira Abbi wanda kuwa Ba kowa ta ya raÉ—a masa shi ba sai Wannan yaron.
" Asad ! Asad ! "
A hankali kuwa ya fara washe manyan idanun sa dake cike da bacci kasancewar jiya bai kwanta da wuri ba sai da ya yi ta rigimar da ya saba wadda har yanzu sun kasa samo masa mafitar ta.Dan haka wasu lokutan tare suke shan kukan su ita dashi abun tausayi dan ita kan ta da take mahaifiyar sa ba zata iya yi masa abun da ya ke nema ba hasalima ba ta san inda ta dosa a abin da yake buƙata.
Zuba wa Alishat ido yayi yana kallon ta wadda ko makaho ya shafa ya san ɗan ta ne amma ba zaka taɓa cewa ita ce ta haife sa ba.
Kiran sunan sa da ta ƙara yi ne cikin murya mai taushi ya sanya shi ɗan Lumshe idanun sa masu cike da bacci kafin ya ɓata fuskar sa ganin tana Murmushi tana nuna masa Mamma dake tsaye tana murmushi itama tana kallon sa.
Da sauri ko ya ja tattausan duvet dake kan gadon ya rufe fuskar sa.
Aiko da sauri itama ta riƙe duvet ɗin tana Murmushi mai bayyanar da side dimples ɗin ta.
Jan sa ta yi baya tana furta wa a hankali cike da Rarrashi " Come on my baby wake up pls ".

" Ummieeey ".

Ya furta kamar ya fashe da kuka É—aga shi tayi tana Murmushi.
Mamma ce ta ce " Asad Abbi na jiran ka fa kaga an fara Salloli ".
" Mamma Basshi ".
Ya bata amsa kamar zai saki kuka.
Yar dariya tayi ganin ya tsayu kan ƙafafun sa da taimakon mahaifiyar sa.
Chapter 105 · 0% Book details