Sashe 78
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yau kwana biyar da samun gocewar ƙashin REENA Kuma har yanzu B bai yiwa LEENA maganar ba kuma ya zuba mata ido da mamaki musamman ganin ta cigaba da harkokin gaban ta,bata nuna wata muguwar damuwa ba akan yanayin yar uwar ta da take fama dan kwanaa biyu Bata ma samun bacci isasshe, sai Ummah ta yi mata addu'oi ta shafa mata akan ƙafar da ke mata zugi haka Sir shima da Dada sai da suka dage da shafa mata addu'a Sannan a hankali ta fara samun sauƙin ƙafar kuma duk wannan yanayi na azaba da Reena take ciki bai taɓa tadawa leena Hankali ba hasalima koda sau ɗaya bata taɓa nuna nadama akan fuskar ta ba,ko damuwa dan haka Ummah da B suka zuba wa sarautar Allah ido.
Yau ta kasance Laraba sun shirya tsaf zuwa gaida kakan su dukkannin su tsohon arziki,su uku suka shirya suka tafi dan BILAL É—in ne ya saka su gaba zuwa wajen Baba Mai Billions É—in da yake É—an fama da jiki.
Har suka isa babu wata sakewa a tsakanin su.Tsitt suke zaune a cikin tangamemen falon na sa Badan komai ba sai dan Yadda Fuskar Bilal take haɗe kamar wani kumurcin maciji dan tun abinda Leena tayi wa Reena ya kasa sakewa da su fuskar sa ta zamo kullum a ɗaure Ummah kullum cikin masa faɗa take Badan komai ba sai dan samun sakewar Reena da take ɗan raɓewa gefe na jinyar da take yi ta ƙafar kafin ta warke gudun abu biyu yayi mata yawa.Sai dai yana bata kulawa Sosai,kamar yadda kowa yake iya ƙokarin sa.
" Ni nayi fushi ace ace sai yau kuke zuwa gaida mai gidan na ku kamar baku son shi "
Farin dattijo ne yake yin zancen yana saukowa daga matattakalar benen fuskar sa ƙawace da murmushi kallo ɗaya zaka masa kasan shine mahaifin Ummah dan babu inda ta baro shi.
Da sauri Reena ta miƙe tana tura ƙafar ta da ta ke ɗan mata ciwo kaɗan ta isa gaban sa tana dariyar farin ciki.
Ba tare da ta tuna gargaÉ—in Bilal ba na natsuwa da yace kowaccen su tayi wanda kuwa ya yi furucin ne ba dan kowa ba sai dan Leena kuma maganar ta shiga kunnen ta dan ta natsu tayi shiru sai satar kallon sa take yi daga gefe har fitowar dattijon da matar sa wadda suke kira Kaka tayi kiran sa dan sun tarar da ita asashen na sa.
Murmushi ƙawace akan fuskar sa yake kallon Reena yana shafa kan ta cike da tausayin ta da wani irin yanayi na kewar abun da yayi masa nisan kiyo.
" So ake na huce da wuri haka ne,ake rungume ni " ?
Yayi maganar cikin dattako yana shafa farin gemun sa da ya ƙawata fuskar sa.
Kai Reena ta gyaÉ—a masa tana kallon fuskar sa.
" Ya jikin B B " Reena ta furta tana Murmushi.
Murmushi yayi mai sanyi ya ƙara shafa kan ta kafin ya furta cike da jin daɗi " Na ji sauƙi mata ta " Sannan ya ƙyafato Leena yana furta " waton ke wannan ja'irar matar ta wa baki yi kewa ta ba "..Ai ko kamar jira take yi ta washe baki ta matsa kusa da shi da ɗan gudu tana dariya tana girgiza masa kai.
Dariya yayi yar ƙarama sannan ya ce " to me zai sa a share ni,sai na yi magana,ga ɗayar mata ta harda mini ya jikin tsufa ".
Ido ta ɗaga ta ɗan saci kallon B Dake zaune yana ɗan taɓa wayar sa fuskar sa kwance da murmushi na ganin dattijon ya samu lafiya dan kwana biyu yana yawan zuwa duba sa kusan kullum sai ya zo duba sa tun da ya dawo musamman ma da ya tarar jikin sa, sai a hankali Ummah ma tana zuwa duba mahaifin na ta duk bayan ɗan lokaci Haka Abba ma da su Dada,Sir suna ɗan leƙawa dan basu yar da Zumuncin ba duk da yar uwar su ta tafiyar ta amma ai Zumuncin su na nan ya riga ya haɗu gasu harda jikokin su jini ɗaya.
Fahimtar cewa BILAL ya gargaɗe su ne ya sa Baba mai Billions bai ƙara cewa komai ba sai ma shafa kan ta da yayi yana murmushi yana tofa musu addu'oi na kariya ba ta re da sanin su ba sai da ya gama sannan ya samu waje ya zauna tare da kowaccen su a gefen sa.
" Ya Mahaifiyar ta ku,tana lafiya ko ".??
Ya tambaya bayan Bilal ya gayar da shi da jiki cikin girmamawa duk da wasan jika da kaka da suke yi hakan bai hana sa bashi girman sa ba da daraja sa kamar yadda yake bawa sauran manyan mutanen da bai san su ba.
" Ai jiya Abban na ku yazo ya jima nan bayan fitar ka ".
Murmushi BILAL yayi yana jin daÉ—i har cikin ran sa.
" Ke yar gurguwa ya ƙafar da sauƙi ko ?"
Ya faɗa yana kallon REENA da take ta murmushi dan indan kewar sa sunyi kewar sa dan tun da ta kwanta ciwon ƙafa basu leƙo shi ba gaba ɗayan su Bilal shi kaɗai yake tahowar sa.
Baki ta tura gaba fahimtar da ita yake
Kafin hawaye suka cika idon ta tuno azabar da ta sha kafin ƙafar ta samu sauƙi
" Ya isa haka Allah ya tsare gaba a ƙara kulawa da hanya "
Ya furta yana wanzar da guntun murmushin sa kasancewar ya san komai duk da Bilal ya ɓoye masa amma ya ji komai gurin Samira jiya da ta zo gai she da shi itama gurin Hamida ta ji komai dan ta je gidan wayewar safiyar da abun ya faru ne ta ji komai bakin Ummah.
" Yaushe zaka koma aiki na san hutun na ka ba mai yawa bane ko " ?
Yayi maganar yana kallon Bilal da ya ajiye wayà r ta sa yana kallon kakan na sa.
" In sha Allah zuwa farkon azumi zan koma,duk da hutun ba mai yawa bane dama na É—auko ".
Kai Baba Mai Billions ya gyaÉ—a yana murmushi kafin ya kalli Leena ya ce " Matas shirun dai yau babu magana "
Murmushi tayi kafin ta ce " Akwai magana man mun kusa zama manya daga wannan shekarar sai wata zamu je senior section "
Ta kai ƙarshen zancen tana Murmushi.
Reena kuwa dariya ta yi itama mai haɗe da murmushi tana furta " Muma mun kusa zama irin su Anty Hamida da Samira mu riƙa fita mu kaɗai ba tare da kowa ba ".
Dariya mai nuna jin daÉ—i Baba mai Billions yayi yana kallon su.
" Ashe amare na sun kusa tare wa, na ku sa zama Sabon Ango na yar da Kaka tsohuwa "
Shigowar Kaka dai dai tsakiyar falon ne da ta shige Bedroom ɗin ta bada jimawa ba ya kai ƙarshen maganar yana sakin murmushi.
Murmushi Kaka tayi tana É—an hararar Baba mai Billions cike da murmushi ta furta " ai mu tsohuwar zuma ce,sai dai ayi da mu a bar mu,idan muma aka matsa mana sai muyi sabon Aure,ga ango na nan a hannu ",ta nuna Bilal dake zaune yana murmushi fuskar sa sai sa.
Dariya Baba mai Billions yayi yana furta " Tsohuwar zuma sai da wuta".Dariya Kaka tayi tana zama kusa da Leena.
" Ni ba zan iya Auren Tsohuwa ba,na bar wa Baba mai Billions yayi ta kaya mu sai masu jini a jika ".
Hararar shi tayi haka ma Baba mai Billions dariya ya saki yana kallon su.
Kafin ya furta " Ko dambe aka haɗa mu sai mun chanye ka Indai gasa ce,dan mu rainon tuwon dawa ne bana ice cream da indomie ba " Dariya Bilal yayi haka ma Reena ganin yadda B B yayi da hannun sa alamar yana da ƙarfi irin mugun ƙarfin nan.Ita ko Leena kallon su kawai take yi dan ta kasa sakewa.
Haka suka cigaba da ta ɓa fira cike da barkwanci da sakewar su har Hamida ta shigo aka cika taro da ita tare da Samira wadda ke ta rawar ƙafa tana bawa BILAL kulawa yana share ta ko kunyar su Kaka bata ji.Sun daɗe a wajen sa kafin suka shiga suka gayar da Mahaifiyar su Samira da sauran jama'ar gidan sannan suka yi Musu Sallama.