← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 110

Sashe 70

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kwance ya tarar da ita kamar koda yaushe dan bai fi sau Biyar ba ne yake samun ta ido biyu saboda yanayin ta da yake son hutu hakan ya sa likitotan suke bata Alluran barci wadda bata cutarwa dan haka ta ƙara samun Hutu tayi wani irin kyau fatar ta sai sheƙi take yi dan ko abinci suna bata shi a cikin drip abun da zai hana ta saurin jin yunwa da ciko mata cikin ta kafin ta farka ta saka wani abu a cikin ta,kuma gwargwado idan ta farka tana shan madara da fruit ɗin suma da ƙyar kafin a gama ta ɓata jikin ta gaba ɗaya dan zuwan su Canada ma ta rage duk wani haukar irin ɓatattar nan so ɗaya ta yi ta wan sahaken da suka zo ta farka cikin na'urar da ke Binciken ƙwaƙwalwa gashi ko ina tar take ta hargitse musu kasancewa su ƙwararru cikin yan daƙiƙu suka mayar da ita yanayin natsuwa dan haka ta koma sai yadda suka yi da ita idanun ta ƙwar akan su ga hasken da take ji har tsakiyar kwanyar ta,ga abubuwan da take gani a cikin hasken kamar an ƙara musu yawa dan haka hawaye suka yi ta silalar mata a gefen ido koda aka dawo wa Suhaila da ita kuka ta zauna ta darza tana kallon Ishaa a wannan yanayi gashi da haske amma ta kasa ko motsi sai hawaye da take yi ta kafe Suhaila da ido.
A bu ɗaya ne matsalar hasken nan da bata so likitota suka matsa da kullum Abar hasken ɗakin kunne.A hakan har ta fara rashin damuwa da shi sannan duk wata rigima ta rage ta, zata yi shiru dai ta zuba ma waje ɗaya ido kafin kaga kuma ta ɗauke kallon ta wajen,Sai kuma hawaye,chan sai kaga tayi dariya ko surutai mara sa kan gado kamar wani yare daban wanda Suhaila bata taɓa sanin akwai shi duniya ba.Kuma yanayin ta hakan yana sanya su Farin ciki ganin kamar wata nasara ce ko wannan maganar tata da take yi cikin Muryan ta ƙarama.Wannan kenan.

Idanun sa ya rintse da ƙarfi yana buɗewa kafin ya ja ajiyar zuciya yana barin ɗakin bayan ya sanar da Suhaila su shirya yau zasu bar ƙasar da dare.
Kai kawai Suhaila ta gyaÉ—a masa tana haÉ—iye wani sabon kukan da ya ta so mata bayan wanda ta gama yanzu,dan ta san tun da bai ce mata komai ba babu wata nasara.
Sai da ta darji kuka sannan ta haÉ—a musu komai na su dama a haÉ—e komai yake.
Da taimakon Nurse suka chanza mata kayan jikin ta daga rigar asibitin...

Ƙarfe takwas dai dai na dare suka hawo jirgi sai Nigeria kafin suka sauka ƙarfe bakwai na safe.Driver ne yaje kwaso su tare Amoh har da Dady da Rayyan a mota ɗaya.
Su ne suka fara fitowa fitowa tare da ma'aikatan jirgin guda biyu da suka tuƙo gadon da Ishaa take kai.
Hawaye ne suka Silalo ma Dady na tausayin Ishaaa, A hankali ya shafe kar amoh ta gani,ita kan Amoh ba,a ma maganar ta.Dan kuka ne ya ƙwace mata ji take kamar ta dawo da yanayin Ishaa akan ta.
Driver motar da Rayyan yake ciki ya buÉ—e wa Suhail ya sanya Ishaa ciki a baya sannan shi ya shige gaban motar.
Ita kuwa Suhaila Gaban motar su Dady ta shiga da driver ya tuƙo su.
Duk yadda Amoh ke son cigaba da daurewa kamar yadda Suhail ya rarrrashe ta, ta kasa haƙuri dan ko yanzu suhaila baki take ta bata kamar ta yi kuka, ita ganin ta yi kamar ma Ishaa ɗin ta bata numfashi, Badan Suhail ya sanar mata da ran ta bazata yarda ba,ga kuma suhaila da take ta bata ƙwarin guiwa, baiwar Allah hankalin ta duk ya tashi lokaci ɗaya.
Dukkanin su sai suka matsu su isa gida dan bai sanar musu da komai ba kuma ya gargaɗi Suhaila ɗin dan haka take ta kame kame ta ƙi yin magana.
Dan haka yana cewa zasu dawo gobe hankalin su ya koma ga jin yadda lafiyar ta ta take sai dai ya datse kiran tare da kashe wayar sa hakan shi ya hana musu sanin komai har Rayyan dan Ya san halin sa da zuciya kamar ta mata zai iya tsorata ya furta wata magana kusa da Amoh ya tayar mata da ciwo duk da ko yanzu fama take yi da kan ta.
Hankalin Amoh ya kwanta sosai jin cewa an gano matsalar har an bada maganin ta tare da zuwa duba ta duk bayan wasu yan lokutta.Kasancewar Dady ya gargaɗe sa kar ya sanar mata bayan saukar su gama breakfast ɗin su sai ya keɓe da Dady ya fara sanar masa dan haka ya gargaɗe sa dan dama shima ko kwonton faɗa mata yake yi.
Dukkanin su kallon Amoh kawai suke yi dake ta farin ciki tana ta faman lailayar Isha dake ta baccin ta har yanzu.Wani sanyi ta ji labarin da Suhail ya kawo mata,itadai Suhaila murmushi kawai take yi tun da ta ji ya'yan ta ya ɓoye ta san cewa saboda Amoh ɗin ne dan haka ta ja ta ƙara tsuke bakin ta,kamar farko.
MA'ISHA kwanan ta ɗaya kafin ta farfaɗo,Yanayin ta na shiru shiru ya dawo ta yi sati haka,kafin suka tashi da wani sabon tashin hankalin da suka shiga domin kuwa yanayin da take ciki ya dawo sabo na haukar ta da har yafi na da domin kuwa kayan jikin ta yanzu babu wanda yake kalluwa duk ta musu fata fata ta yaga kamar yankan reza kuma duk wanda ya matsa wajen ta sai ta masa illa.Amoh harda kwanciya asibiti duk da yadda aka kwantar mata da hankali da cewar likitotan ta sunce dole zata yi hakan kafin komai ya fara yin ƙasa.Dan haka suka samu ta ɗan kwantar da hankalin ta.
Yanzu har ta kai Ishaa Ɗaure ta ake yi saboda yadda take azabtar da kan ta.Cikin ɗan wannan lokaci wannan a hali sun shiga tashin hankali matuƙa,sai dai sun duƙufa wajen faɗawa Ubangiji ba dare ba rana,sun san shi ya ɗaura mata wannan lalurar shi ya jarabce ta da ita kuma shi zai yaye mata..
Chapter 70 · 0% Book details