← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 110

Sashe 102

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kwana tashi ba wuya wajen Ubangiji Ramadana ya zo ƙarshe, su shatou an karɓo ɗin ki sai murna ake yi.
" Inna ni wallahi kayan nan sun mugun yin kyau ba zaki gane ni ba ranar Sallah ".
Murmushi Inna ni kawai tayi tana girgiza mata kai.
Tana furta " da wannan ƙashin na ki na wuya sai kace wadda tayi a zumi talatin ciff ".
Dariya shatou tayi tana taɓa wuyan ta ta ce " ai ana gama azumi zan cika sa ".
" Allah ya sa " Inna ni ta furta tana Murmushi.
Bibu ma murna yake ta yi yana gwada kayan na sa kala biyu...Kamar na shatou da hijab É—aya.
Cikin ikon Allah an ga wata yau gobe ake hawan idi ta kowa ne bangare murna ake yi da yi wa juna Barka da Sallah.
Mahaj ma gida yayi Sallah sai dai tun da aka dawo Idi ya shigewar sa duk yadda Abbu ya so ya fito ya ƙi fitowa.
A ɓangaren masu aiki kuma sun kammala gyara sabon ɓangaren makarantar su shatou a bun ka ga harkar Naira,sannan an samar musu da hanyoyin ruwa masu kyau da tsafta bisa ga inda suke zuwa ɗebo ruwan su.
Dan haka Abbu ya saka ranar ƙaddamar da aikin dan fara amfani da shi sallah da sati biyu.

A cikin wannan lokaci na bukukuwan Sallah shatou an sha tangaririya ita da su Amina da su Ramata da Bibu dan duk inda za,a je da shi ake zuwa.
Kowaccen su ta sha ado ta labta jan baki a baki da ja gira babu ma kamar su Ramata da Jawairiyya.
Sai dai A wannan karon itama shatou ta sha Jan bakin ta da Ja gira ta yi kyau a irin kwalliyar ƙauye Inna ni dai in ta kalle ta sai dai tayi murmushi kawai ta girgiza kan ta,da ta so hana ta yi sai ta ga rashin amfanin hakan dan haka ta bar ta ta kashe fuskar ta sai gashi ta ɗan mata kyau,dan kafin su fita Tv ta mayar da ita har sai da Shatou ta kai ga cewa " Inna ni nayi kyau ko" ?.Kai Inna ni kawai ta gyaɗa kafin ta ce " Sosai kuwa kamar amaryar kauye ".
".a'a nikam Amaryar Birni ce ba zan yi aure a ƙauyen nan ba ni da ma zan zama yar sanda Aure na ba yanzu ba ".
Inna ni dai a yanzu ma Murmushin tayi kafin ta ce " Allah ya ce "
Har suka fice tana kallon Shatou tana Murmushi kafin hawaye kuma ya wanke mata fuska,daga nan ta shige ɗaki ta saki wani irin kuka mai ciwo da ƙunar zuciya sai da tayi mai isar ta sannan ta share hawayen ta daga nan barci ya kwashe ta kasancewar ita kaɗai ce a gidan.Sai su shatoun........

" Uban wa na kama "

Muryan sa ta daki kunnen ta ba ita kaɗai ba har ta da su Amina sai da ƙirjin su ya buga jin muryan sa dan tunda aka fara a zumi ko hanya basu ƙara haɗuwa da shi ba wanda sai daga baya suke jin ya shiga birni kai rake.
Tsuru shatou tayi da ido tana kallon sa.
Shima haka.
" Yarinyar nan sai yar shila kike zama ".
Maganar sa ta ƙara ratsa Kunnuwan ta.
Ya kai ƙarshen zancen yana lasar baki kamar wani maye.
Hararar sa ta samu ƙarfin yi sannan ta ce " kai muje " Bibu da ke a tsorace ya riƙe hannun Shatou gamm.
Kara shan gaban su yayi kallon kallo aka fara tsakanin ta da su Amina kowa na tunanin abin yi dan sun ma fita tsorata.
Dariya abokan sa dake tare da shi suka sanya ganin yadda shatou ke ta zarar ido.
Hararar su ta ke ta yi tana jan tsaki.
Wani mai zafin nama ne ya É—aga hannu da zummar kai ma bakin ta bugu
Sai dai bai samu damar yin hakan ba domin kuwa hannun sa aka kama da ƙarfi.
Ba kowa bane kuwa face Iro da ya sha shaddar sa yellow sa ka wanke sai walƙiya take yi kamar an mata ruwan mai.
Wani sanyi ne ya ratsa Shatou.Tana gode ma Allah.
" Wallahi da ka taɓa ta sai zaman garin nan ya gagare ka ".
Iro yayi zancen yana Harare Harare,Wanda ya je gidan su Shatou aka ce bata nan dan yaje gwada mata wankan san na yau dan yanzu ta ɗan fara sake masa sai dai yana ganin wulaƙanci kuma hakan ya ke shanye wa dan shi burge shi hakan ke yi saboda yana shiga birni,sai yake ganin kamar tana masa irin yadda yan matan birni ke yiwa matan su ganin sa abun da take masa yan ga ce.
Hannun sa ya janye yana huci kafin ya ce " To uban ya zai sa ta mana tsaki,ita fa wannan yarinyar ji take kamar uban ta ya gina ƙauyen nan,ke ba yar kowa ba babu asali mai kyau amma ke har kin samu damar raina mana mu da ƙauyen mu,wallahi kin cin sa,a da mun Miki figar kaza, Ni da ace nine kika yiwa budurwa ta wannan bugun da tuni na jeme ki amma ko yanzu ba zan bar Shamsu yayi wannan yaƙin shi kaɗai ba ,zaki gane kuren ki ".
Ya kai ƙarshen zancen yana jan mugun ƙyafci wanda ke nuna a hasale yake.
" Ka kashe ta idan ka ta shi ".
Iro ya furta shima cike da hasalaaa.
Shatou dai ganin cacar baki ta kaure tsakanin su ne hakan ya sa ta ja hannun su Amina suka yi gaba.Tana ji yo muryan Shamsu na zagin ta da aiban ta ta,da kalmomi mara sa daÉ—i wayen da yarintar ta ba zata iya bata damar tantance su ba da ma,anar su.
" Wallahi sai na mata mugun wulaƙancin da bazata taɓa mantawa da shi ba,ba dai kai ka ɗaure mata ba daga kai har ita sai na jefa ku a masifa,zaka san ka shiga hurumin Shamsu,Shatou sai ta zamo a bar tausayi ka rubuta ka aje ".
Wayen nan sune kalmomin da suka mata wani irin tsayi a kunne da zuciya dan dakatawa tayi tana juyawa kadan ta kalli Shamsu dake maganar wanda ya ke zancen yana ƙure ta da kallo yana huci saboda yadda Iro ya tare hanyar ta sannan ya ce idan ma mutun ya cika Shege ya matsa ya taɓa ta sun san halin sa hakan ya sa kowa ya yi cirko cirko,shi ko Shamsu ya ce aka mo masa ita,Amma duk sun ƙi matsawa dan haka ran sa ya mugun ɓaci ya ƙara ƙulla masifar da ke cin zuciyar sa ta ƙiyayyar shatou da ya ɗaurawa kan sa.
Haka kawai jikin shatou yayi mugun sanyi har ta ji kafafun ta sun kasa É—aukar ta.
Yawon Sallahn da ba,ayi ba kenan yau dan jikin ta ya mutu mutuss ta kasa ko tafiya da kuzari tayi sauri bare gudun da suke yi idan sun ga ji kafin su samu mafaka su huta suna dariya.
Gidan su Amina suka wuce har Bibu.
A chan ta É—an wartsake har ta saki maganganun Shamsu suka cigaba da wasannin su na É—iyar kara.Sai kusan Magriba suka yi gida ita Bibu kuma ta ce
Bibu kar ya faɗi komai game da abun da ya faru yau,ɗan kallon ta kawai yayi bai ce komai ba dan duk da shima ba wani girma gare sa ba ya ji kalmomin na Shamsu sun ratsa kan sa dan haka ya ƙara tsorata ta da shi,tsoron sa idan ba kashe masu shatou zai yi ba.Dan haka yake jin kamar ba zai iya shiru ba sai ya fadawa Baffa na.Sai dai tuna cewa Inna ni zata iya ji kuma sai ta daki Shatoun hakan ya sa ya ji zai iya kame bakin sa.
Koda suka isa gida Baffa na bai dawo ba shima daga fadar mai gari.
Sun tarar da Inna ni tsakar gida tana sauraren rediyo ana zaɓen Barka da Sallah na gaishe gaishe na sallah ga yan uwa.
Suna saka waƙoƙin soyayya na zamani.
" Inna ni ma idan na yi Aure wata rana haka zance ina gaida Inna ta ina mata Barka da Sallah da ita Baffa na da Bibu da su Amina,Amma idan nayi Aure nesa ".
Murmushi Inna ni tayi kafin ta ce " Ohh amaryar Iro ko kin manta an gama zancen ne ko dan kin ji nayi shiru ne ai magana ta kan kama tuni baffan ku har ya fara zancen kuɗin Aure zai karɓo jibi tunda ke kika bada dama a nemo Miki ".
Idanu Shatou ta ƙwalalo ta ce " Dagaske Inna ni " ?Tayi maganar tana dariya.
Baki sake Inna ni ta Kalle ta kafin ta ce " Dagaske dai kina son yaron nan ".?
" Allah ya raba ni nikamm wallahi sai É—an birni ".
Kai Inna ni kawai ta girgiza tana ɓoye dariyar ta.
Ganin yadda ta haÉ—e rai.
" To ai na ga ko É—azu angon naki ya zo neman ki "
" Eh ai kawai gaisawa muke yi Ni bana son sa ina da miji na É—an birni ".
" Dagaske wane ne wannan mai sa,a ".
Baki washe shatou tace " ban san shi ba amma dai ɗan birni ne,kuma zai zo nan ya kwashe mu tare da ke da Bibu da Baffa na,kin san Inna ni na taɓa mafarkin na je birni,ƙila ma shi zai zo ya kai ni makarantar yan sanda ".
Chapter 102 · 0% Book details