← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 110

Sashe 20

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👅👀👂Ka tsarkake wayen nan ɗan uwa.
Na farko_harshen ka.(Magana mara daÉ—i,mai iya jefa ka haÉ—ari )
Na biyu _Ganin ka.(Daga haramun)
Kunnuwan ka _ Jin ka.(Daga Haramun )
Idan ka kiyaye waÉ—an nan kaga ma samun natsuwa ta duniya É—an uwa.

🌻🌱🌻🌱🌻🌱🌻

A ɓangaren su LINA kuwa tun da Ya'u ya hau titi babu wanda ya cewa ɗan uwan sa ci kan ka tsakanin ta da su Ninah ɗin.Har suka sauka gaban ƙatuwar gate ta makarantar kai da ganin ta kasan Naira ce ke aikin ta dan haka malammai ma suke iya yin su saboda yadda iyayen yara suke zube kuɗade makudai dan samun ingantaccen ilmin Arabia na ya'yan su kamar na boko kamar dai Familyn SS da suke da wannan babu gefen da suka saki dan akwai wayen da duniyar kaɗai suka saka gaba.
Firfitowa suka yi suka shige cikin makarantar kasancewar basu yi latti ba kai tsaye kowaccen su tayi na ta aji dan an rabasu gaba É—ayan su waccan an kai ta Faslul A'isha R.A wacchan Usman R.A kowacce da nata sai dai duk a bu É—aya ake koya musu.

Zaman ta ke da wuya wata ƙawar ta da halin su ya zo kamar ɗaya mai suna Anisa ce ta zo da sauri kasancewar ta ga shigowar su tana wani ajin tana faɗa da wani yaro da ya buge ƙanwar ta.Anisa da Lina kawancen su ya fara ne lokacin da kowaccen su ta gano kanwar kasa ce ita,dan farkon zuwan su LINA itace kaɗai take nuna rashin tsoron ta har dai suka saba,kuma itace ta fi kowa sake mata saboda yadda kowa yake shayin ta saboda agaban su ranar da aka kawo su tayi dambe da REENA ta daddaki kayan ta.Shine silar haɗa kan su amma duk da haka ko yanzu ta haɗa su sai an raba su kare jini biri jini suke yi.

" Ke lafiya nagan ki kamar a tsorace "
LINA tayi zancen tana kallon ta.

" Isah na dako,da ya daki Rahima ".
Ta bata amsa kai tsaye tana cigaba da zare ido.

" To shi ko zare idon na me ye " ?Ta ƙara yin zancen tana Hararar ta tana ciro qur'anin ta a jaka.

" Wallahi ina kai shi ƙasa na fara nusa naji tsitt ashe Ustaz Babba na tsaye yana kallon na " Shine duk ajin suka natsu bayan ganin tsayuwar sa.

" To sai me dan ustaz Babba ya ganki,ba bulala ce ba kawai sai ki tsaya a Miki ki tashi ki kakkaɓe hannun ki da hijab ".

LINA tayi zancen tana buÉ—e shafin da zata bada yau.

" Hmmm ba zaki gane ba bane ustaz Babba ya fi kowa iya Bulala a makarantar nan,kin zata irin dukan su Uztaz ne da kike kakkaɓe ma hijab ".

" Shi kuma Isah sai yayi bayani bari a tashi,haka kawai zai kama ta ya daka saboda yana shugaba ".

LINA tayi Furucin ba tare da ta tan ka ma Anisa ba.

Shiru suka yi tana cigaba da karatun ta cikin sauti mara ƙara dan duk abunta ta wannan fannin akwai natsuwa da mai da hankali,dan ta tsani ta je karatu tayi ta kure a na mata gyara.Dan duk littafin ta na karɓan hadda jaidan ne ke tashi a rubuce.

Kasancewar Ustaz na ajin na su ya zo ya sa suka natsu karɓan hadda ya fara a hankali ta kowane ɗalibi kuma gwargwado ajin kowannen su yana ƙokari.
Su LINA ne seat na baya a sashen mata kuma itace ta ƙarshen seat itace ta ƙarshe a karɓa.Cikin ƙwarewa da iyawar da Allah ya bata ta yi ta tayi ta rera karatun ta a cikin suratul kahfi ustaz na su sai gyaɗa kai yake yi yana jinjina kai saboda yadda take tafiya babu wani kuskure.
Haka har ta gama ta miƙe bayan an mata kabbara kamar yadda aka yiwa kowannen su.
Ƙari aka musu gaba ɗaya saboda tare suke tafiya gaba ɗaya ajin.
Sallamar Ustaz Babba ce ta sanya ƙirjin Anisa bugawa da ƙarfi kafin ta lafe a kan kujerar su tana sauke niƙab ɗin ta.

Gaisawa suka yi da Ustaz.Kasancewar Duka malamman na su Suna kiransu da ustaz Babban da suka ƙara na shugaban makaranta ne shine banbancin.Suna banbanta wa ne kuma a lokacin da magana ta shigo sai su faɗi ustaz wane da da sunan sa.

Da Larabci yayi wa Ustaz na su bayanin komai harda sunan Anisa kasancewar kowannen su yana jin Yaren sai suka fara waigen Anisa da take zaune cikin ta ya ɗuri ruwa kamar kace ƙyat ta yi gaba saboda a kunnen ta Ustaz Babba ya faɗi komai.
Kallon ta Ustaz na su yayi kafin ya ce " ta'al ta'al Anisa " Jikin ta ne ya fara rawa dan ta san yau sai ta ci na jakuna ganin yadda ran ustaz na su ran shi ya ɓaci ganin sa duk irin ƙoƙarin da yake kan su ace wai ɗalibar sa ce dambe da maza,inda ma Isah ƙarami ne amma da kallon ta kasan ya girme mata koda shekara biyu ne.
Ta sowa tayi tana jin kamar tafiyar gaban Allo ta ƙara tsawo.
Niƙab ɗin ta Ustaz ya sa ta ɗage wanda idanun ta sun cika da hawaye har sun fara zuba,kafin ya fara mata faɗa dai dai lokacin da bulalar da Ustaz Babba ya aika a ɗauko masa ta iso.Saboda Har Isah yayi wa hukunci itace ya bari ta samu damar karɓan hadda.

Sai da ya gama faɗan sa Sannan Ustaz Babba ya yi mata bulala Goma a ƙafafun ta.Kowa sai da ya tausaya mata kuka ta ke tayi amma hakan bai sa Ustaz Babba ya ƙyale ta ba.
LINA ta tausaya mata matuƙa dan haka ta sha alwashin sai ta yiwa Isah bugun wahala dan zasu yi same age dashi,Wanda ko nan gaba aka ce ya taɓa wani ba zai ƙara ba.
Da ƙyar ta rarrashe ta tana jin zafin abun da aka yiwa ƙawar Tata.Duk da bugun da aka yiwa Anisa bai sa LINA jin tsoron aiwatar da wani a bu dan Anisa da ƙyar ta iya taka ƙafafun ta sunyi jaaa sosai dan sai ka cire socks.
Ana tashi Ya'u ya zo ɗaukar su,tare da Anisa da ƙanwar ta suka wuce ganin ba,a zo ɗaukar su da wuri ba gashi sai kuka take yi,hakan ya sa LINA shigar da ita tasu su sauke su gidan su sannan su wuce na su.

Har gida suka ajiye Anisa tare da yiwa Maman su bayani sai dai mahaifiyar su Anisa faÉ—a tayi ta mata na dambe da maza da ta fara.Su dai su LINA dama ita da REENA suka shiga da ita,Sallama suka yi mata.

Koda suka fito suka shiga Mota Ninah sai faÉ—an an bar su zaune a mota take yi su sun gaji har da cewa Ya'u ya tafiyar sa.
Sai dai ya ƙi saboda ya san inda rigimar zata ƙare kan sa.
Babu wanda ya tanka mata cikin su sai dai LINA da ta yi kamar bata ji ta ba ta ce " Ke bafa shirun kura ya zamo tsoro bane,wallahi yanzu sai na lallasaki gurin nan,Uban wa zaki É—agawa murya mtsww ".
"Ke É—in ko kema kin zata tsoron ki ake ji da da yan zu ba É—aya bace wallahi sai dai muci uban juna ".Cewar Ninah.

" Uban wa kike zagi " ?
LINA ta yi Furucin tana ƙoƙarin baro gaban motar da take.
Ya'u ne yayi parking motar yana cewa " Dan Allah Hajiya ALINA Kiyi haƙuri kinji ku bari nidai na kai ku gida lafiya,ku tausaya wa abinci na yanzu idan wani ya taɓa wani ya ji mashi ciwo cewa za,ayi laifi na ne da ban raba ku ba,dan Allah kiyi haƙuri,REENA ki bata baki ".

Hararar sa tayi tana jan ƙyafci REENA da ta buɗa bakin ta tana furta " Kefa LINA saurin ɗaukar zafi gare ki ".

" Rana ce " LINA ta bata amsa tana Hararar ta " kuma wallahi kika matsa mini sai na haɗe ku duka na ci ƙaniyar ku ".Ta ƙara furta wa
REENA Hararar ta kawai tayi tana jan mugun tsaki kafin ta ce baki iyawa wallahi.

LINA saboda kawai ya'u da ya roƙe ta ya sa ta share ta da sai ta yiwa bakin nan aiki ta cika sa da jini.
Shiru motar ta ɗauka babu wanda ya ƙara furta komai itadai Hamrah shiru take saboda tsoro gare ta ta san halin LINA ƙwarai bata manta yadda ta sha wahalar ta chan da bata san halin ta ba.

Yana dai dai ta parking ta fito tare da wartar jakar ta.Koda ta shiga ta tarar da su Ummah da BILAL zaune a falon sai kuma Hamida yar wajen Ƙanen su Ummah.Wadda ta girme ma su LINA sosai dan ita budurwa ce duk da bata cika irin cikar nan ba.Amma a shekaru zata yi shekara sha Shida.

Duka da ido suka bita Hamida dake kiran sunan ta shiru tayi dan ko juyowa bata yi ba duk da ta gane Muryan ta duk da bata lura da ita ba kan ta sama yake.
Kai Kawai BILAL ya girgiza kafin ya ce " Ummah kin gani ko ".

Numfashi ummah ta sauke kafin ta kalli Hamida da tayi shiru sannan ta furta " Hamida kin san halin mutuniyar taki sai ahankali ƙila wani ya taɓa ta awaje tun da kina nan har an jima zata sauko ".

Kai Hamida ta gyaɗa tana sakin murmushi kafin suka cigaba da taɓa fira rabi duk ta jikin kakan su A bukar ce da yake ɗan fama da jiki kwana biyu dan ita Ummah bata ma sani ba sai yanzu a bakin Hamida dan yace kar a faɗa ma kowa ba wani ciwo bane tsufa ne kawai.Dan dama baya da Isasshiyar lafiya abubuwa biyu sun ƙara Raunata sa ga tsufa.

Shigowar REENA ce ta sanya su kallon ta cike da murmushi kamar yadda fuskar ta take washe.

" Oyoyo yaya Hamida,shekaran jiya ma sai da nayi wa LINA maganar muje muga Baban Billions amma tace mu bari sai week end muje mu yi shi chan ".

Murmushi Hamida tayi fuskar ta washe itama kafin ta furta " ai nayi fushi gashi ni na zo da kai na duk da haka ".
Chapter 20 · 0% Book details