Sashe 81
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ya kai ƙarshen zancen yana kafe Shatou da ido.Aiko yana aje ayar zancen ta Gwale manyan idanun na ta masu haske ta ɗaura kan sa kai daga nin yadda take zare su ka san ba lafiya ba.
Murmushin gefen baki ta saki kafin ta juyar da ƙwayar idanun ta kan Inna ni da take makure idanun ta Sun rikiɗe sun sauya ga hawaye kwance cikin su wanda kowanne irin lokaci tana iya fashewa da kuka.
Idanu Inna ni ta saka cikin na Shatou ɗin duk da idanun na ta kallon su ciki da ciki akwai tsoro domin ko ƙyafta su bata yi.
Kai Inna ni ta girgiza mata,bayan hango bakin ta na motsi kamar kullum idan sun zo da magana.Sai dai ba zata so ta ji komai ba a gaban Baffa na ba domin dole ne ya san abun da ta furta mata.
Aiko kamar ta fahimci abinda Inna ni ke nufi sai kawai ta É—auke idanun ta,ta mayar kan Baffa na sai da ta masa kallon yan seconni kafin a hankali ta mayar da kan ta gefen Inna ni sai kuma ta fashe mata da kuka.
Wani irin bugawa ƙirjin Inna ni yayi wanda har sai dai Baffa ba ya ga alama dan idanun ta sun fito waje sosai na tashin hankalin da ya bayyana a gare ta domin kuwa ta san kukan na Shatou Ko tace mutanen Shatou bana lafiya bane,kuka ne da ke nuna akwai matsala daga abun da take faɗa mata wanda har yanzu ta ka sa gasgata lamarin dan bata san ta inda zata fara ba,domin kuwa abune mai ɗaure kan mai tunani da hankali.
Baffa na kuwa haka kawai ya samu kan sa da kafe Inna ni da idanun sa yana kallon yanayin ta da karantar sa kafin a hankali ya ɗauke kallon sa daga gare ta yana sauke numfashi sai dai zuciyar sa ta fara masa wani zancen kamar na da walakin akan yanayin da Inna ni ta shiga dan bai taɓa ganin ta a wannan yanayin ba tun bayan Samun lafiyar Shatou ɗin da ita kan ta na doguwar jinyar da tayi.
Kuka ne Shatou take yi wanda ke fitowa daga ƙasan zuciyar ta jikin ta har girgiza yake yi gashi an kasa samun mai rarrashin ta a haka Bibu ya same su kowa yayi jigumm ga shatou na ta darzan kuka.
" Adda shatou "!
" Me yake damun ki,?Baki da lafiya ne,ina yake Miki ciwo " ?
Wayen nan sune tambayoyin da yake ta jerawa Shatou bayan shigowar ta sa hankalin sa ta she ya matsa kusa da ita kamar zai fashe da kuka shima idanun sa har sun cika da hawaye na Tausayin yar uwar ta sa.
A jiyar zuciya dukkanin su suka sauke ganin tayi shiru bayan zaman Bibu kusa da ita.Dan kuwa shima idanun ta zuba masa har sai da ya ɗan tsorata kafin ta janye su kan shi hannunn sa ta riƙo " kafin a hankali ta ƙyafato shi tana nuna masa ya karo kunnen sa kusa da bakin ta dan da alama shaƙaƙƙiyar murya ga re ta ko gare shi Dan har yanzu Inna ni bata san wane jinsin bane na mace ko namiji amma tafi masu kallon mace.
Karo kunnen na sa kuwa yayi kafin a hankali ya tsinkayo yar ƙaramar Muryan ta da bai fita sosai ciki ciki take sai ma kana da lafiyayyen kunne zaka ji ta furta.
" Ka yi haƙuri ba da gangan na dake ka ba,kuskure ne,Kar ka sanar wa da Baffa na abunda nace amma kana iya faɗawa Inna ni,idan kuwa ya matsa yana son ji ka faɗa masa ".
Hawaye ne suka cika idon Bibu a take kai ya girgiza mata share hawayen sa yayi kafin ya yi kokarin riko ta, ta tashi zaune sai dai kamar dutse haka ya ji dan haka ya sake ta yana sauke a jiyar zuciya fuskar sa cike da damuwa dan duk shi ganin yake yi duk shiru shirun da ta koma abun da ta masa ne ke damun ta.
Idanun ta ta mayar kan Baffa na kafin a hankali ta masa wata alama kamar ta kurame.Sak kuwa ya fahimta alamar zasu tafi ne suke masa dan haka bai ce komai ba.Kan Inna ni suka juya kafin suka ƙara kallon ta sannan ta fara rufe idanun ta bayan ta sakar wa Inna ni murmushi mai nuna tabbacin akwai damuwa sai dai tunda ta fahimci Inna ni bata son sanin komai ne ne gaban Baffa na sai ta haɗiye komai shine dalilin sakin kukan na baƙin cikin duk da ta san ko faɗawa Inna ni tayi babu abinda zata iya,amma ta san addu'ar ta kamar dafi ce akan abinda ta zo dashi.
A haka bacci ya kwashe Shatou jikin ta ya saki sai numfashi da ta fara saukewa a hankali.
Baffa na ganin haka ya sa ya sauke ajiyar zuciya kan shi kuwa da yake har yanzu a kulle ya dafe kafin ya miƙe ya fice daga gidan jin kiran Sallah la,asar da ya karaɗe ƙauyen bayan ya sanar da fitar ta sa.
Inna ni ma numfashi ta sauke da ajiyar zuciya mai nauyi kamar wadda ta haɗiyi zuciya damuwar ta na sake dawowa sabuwa Badan komai ba sai dan rasa jin abinda suka zo da shi a yau ɗin wanda ta tabbatar babu lafiya tunda ga yanayin Aljannun na Shatou.A haka ta gyara mata kwanciya ta miƙe tare da ɗaga Bibu tana cewa.
" Muje ka watsa ruwa kayi Sallah kaci abinci ka kwaso yunwa,Addan ka ta samu bacci ".
Babu musu kuwa ya miƙe yana share hawaye.
" Baccin ta samu fa kuma zata tashi kaji ".
Inna ni ta furta jikin ta a sanyaye ganin yadda Bibun ya kasa sakewa.
Kai Bibu ya É—aga kafin ya shige É—an É—akin sa ya cire kayan sa ya canza da wasu sannan yayi alwallah ya wuce masallaci yana dawowa sannan ya shiga ya watsa ruwa yana gama shirya wa ya zauna cin abinci kuma har lokacin Shatou bata farka ba yana yi yana kallon ta har ya gama cin abincin sa.
Baffa na kuwa wani uzuri ya hana sa dawowa gidan bai dawo ba sai Gab da magriba kuma yana shigowa ana kiran Sallah dan haka kai tsaye ya yi alwallah ya wuce masallaci tare da Bibu da ya ke ta yiwa Shatou Fifita tana shan baccin ta hankali kwance.
Dai dai fitar su kuma Shatou ta fara motsi alamar tashi a hankali kuwa ta fara ware manyan idanun ta da suka ƙara girma da haske tar kuwa ta ware su akan Inna ni dake zaune akan yar zuƙunno ta buga ta gumi tana kallon ta.
Ya mutsa kyakkyawar fuskar ta tayi da ta ƙara yin fayau farin ta ya ƙara bayyana sai shinning take yi kamar yadda kuka san fatar nan ta yan Korea mai walƙiya kamar suna wanka da mai na madara.
Murmushi ta sakar ma Inna ni kafin ta miƙe zaune cike da kuzarin ta,tana jan doguwar miƙa tare da Nanata addu,ar tashi daga bacci.
Inna ni ma Murmushin ta sakar mata tana jan ajiyar zuciya tare da riƙo hannun ta ɗaya.Bata ce mata komai ba sai da ta dangane ta da ɗakin ta,da taimakon ta shatou ta cire kayan jikin ta Sannan ta ɗaura zanen da take wanka dashi.
Fitowa Inna ni tayi ta haÉ—a mata ruwan wanka ta kai mata makewayi.
Ɗan leƙawa tayi bayan ta kai mata ruwan ta ce.
" Kije ki watsa ruwa na kai Miki ki samu ki yi Sallolin ki,dan ban samu ta da ke daga bacci ba ".
" Touh ".
Shatou ta furta a hankali babu musu kafin ta fito daga É—akin,makewayin ta shige ba tare da ta ce wa Inna ni komai ba da ke alwallah.
Sallah ta kabbarta bayan gama alwallah.
Koda Shatou ta fito Inna ni na Sallah bata ko gama magriba ba.
Ruwan Alwallan da ta zuba mata a wata ƙaramar buta ta ɗauka kafin ta yi alwallah sannan ta shige ɗakin na ta.Bata jima ba ta fito ta sanye da wata yar kodadddiyar riga da take mugun so ta roban gwanjo da Baffa na ya taɓa siyo mata da yayi tafiya.Dan rigar da jan ta take yi amma yanzu ta ɗan shige mata dan haka take jan ta tun Inna ni na dariya idan ta sako har ta daina.
Kusa da Inna ni ta tsaya ta sanya hijabin ta ta kabbara Sallah lokacin Inna ni ta sallame magriba zata fara nafilan bayan magriba.
Magriba ta fara yi kafin ta ranka la,asar A tsanake tayi Sallolin ta koda ta gama su Baffa na sun shigo suna zaune gefe shida Bibu akan yar tabarmar kaba sun zuba mata ido babu ma kamar Baffa na sai dai fuskokin su cike suke da annuri ganin ta zaune harda sallah.Samun kan ta tayi da sakar musu murmushi haka suma.
" Ya jikin ki Adda shatou " ?