← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 110

Sashe 38

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A ɓangaren su Abba kuwa ranka ya suka yi zuwa gida fuskokin su cike da farin ciki,bayan ya Rarrashi LEENA.Tare da Masu tsaron sa da come boy na sa da suke cike da kewar sa suma.Ma'aikatan masu kula da kamfanonin sa,dan suma sun zo tarbon Sa.
Cike da farin ciki dukkanin ahalin suka tarbe sa,Har su Hamida sun zo da iyayen su dan Abba ya ɗauki yan watanni chan.Farin ciki Sir da Hajjo da su Uwani bai ɓoyuwa dan Abba mutun ne mai kula duk da kuwa baya nan yana ƙoƙarin kiran yan uwan sa da iyayen sa,surukan sa.
Ƙaton dinning dake babban falon na Ummah aka baje masa komai da akayi masa duk wani wanda yayi masa abun tarba nan aka kawo masa shi.Dan faranta masa yana mugun son yaga ko ina ahalin sa ne dan haka har su Sir aka zauna akayi ci aka ƙoshi kafin aka ƙara yi masa ya hanya,ya kuma baro Germany ɗin dan chan ya tafi.

Su LEENA da su REENA take aka fara mantawa da wani faɗa aka cigaba da bawa Abba kulawa.Ummah bakin ta kamar ya yage saboda farin ciki sai dai ta wani ɓangaren tana kaƙalo murmushi ne kawai bata san dalilin da ya sa bata son ganin kishiyoyin na ta a part na ta ba.Amma gudun abun magana sai take ƙoƙarin haɗiye komai gashi an shedeta da haƙuri dan Ummah mace ce mai haƙuri da kau da kai.Dan kafin ma kaji ance wani abun ya haɗa su da wani sai an bincika.ta san ta kan ta bata bari kishin ta ko kaɗan ya fita har ya zame mata illa..
Sai da aka watse gaba É—aya sannan abba ya samu ya je ya watsa ruwa sannan ya dawo falo cikin ya yan sa.Cikin su ya zauna yana biye musu ana bashi labari rabi duk shirme ne dan REENA ce mai bada labarin idan ta faÉ—i wani abun sai dai yayi dariya ita ko LEENA sai ta galla mata harara.Cikin Surutun nan ne na ta wanda indai tana gaban mahaifin su bakin ta bai iya shiru duk da rashin hayaniyar ta ta sanar da shi Damben da suka yi aschl shekaranjiya.

Yi yayi kamar bai sani ba ya tsaya ya saurare ta kafin yace " Amma ALEENATU Baki kyauta ba gaskiya,Yar ƙaramar ƙanwar taki zaki daka,baki san kin girma ba ".

Ya kai ƙarshen zancen yana sakin guntun murmushi tunda abun ya wuce.

Ɓata fuska Leena tayi kafin ta ce " Ai Abba itace sai ta dinga yin abu kamar bata da wayau Ni kuma sai na dinga jin haushi ".

Kai Abba ya girgiza yana mai da kallon sa kan REENA da ta ke ta Hararar Alina sannan ya furta " Laaa laaa daina kin ji yar gaban goshin Umman ta,harara Anty kike yi,ita wannan Munbar wa BILAL S S ƙanwar sa " ya nuna Alina,nufin sa ita.

Ya É—an yi gefe da kan sa kamar bai ga yadda idanun ta suka cika da hawaye ba.

" Allah Abba,Ni ta gaban goshin Familyn SSS ce gaba É—aya nice hasken idaniyar ku,Ni bana son na zauna gaban goshin ya Bilal a bar Ni da kai da Sir da KaKa,Kuma inada Baba Mai bIllions a gefe na ".

Ta kai ƙarshen zancen ran ta ɓace cike da ƙuruciya.

Dariya Abba yayi yana son su tado da zancen sai dai sun ƙi dan haka bai ƙara tada zancen ba.

Sai ma shiru da yayi yana kallon Ummah da tayi shiru kamar mai tunani fuskar ta babu annuri ta zuba ma waje ɗaya ido kamar hankalin ta bai kan su sai dai kuma duk abinda suke yi tana jin su,hasalima wata kalmar da Abba yayi ce ta ɓata mata rai.

" Ai kuma REENA ce ta gaban goshin ta Abba bani ba ka tambayi Ummah kaji ".

Zancen Leena ne ya shiga kunnen sa hakan ya sa ya É—an juyo da kallon sa kan ta yana furta " ai kema ta gaban goshin sa ce ".

Ummah ce tayi karaf ta amshe zancen cikin sakin Murmushi tana furta " Ai dukkanin ku na gaban goshin sa ne,his precious girls,kawai rashin jin maganar nan ne ke haÉ—a ku,idan kika daina zaki ga Kun shirya ".
Ta kai ƙarshen zancen tana dariya.

Abba dake jin ta kuwa wani guntun murmushi ya sauke kawai bai ce ƙala ba sai ma miƙewa da yayi,ya kama hanyar barin falon dan bacci yake ji saboda kwana biyu bai samu ya runtsa ba saboda yana shirin baro ƙasar..

" Zanyi bacci Barry,kar a tashe ni kowaye ya zo " .
Ya ce wa Ummah.Dan haka yake kiran ta ko kuma Umman su.

" Abba ko Yaya BILAL ne ya dawo "

Reena tayi zancen tana Murmushi.

Kai ya girgiza shima yana son yin dariya hango yadda Leena ke ta Hararar ta.
Saboda jin wani sabon sakar ci.wanda ita bata É—auke shi komai ba.
yadai suɓuto bakin ta kuma ta fitar.

" Ko shi ne SARINA ai ya san inda na fito ba zai so a tashe da Abban sa ba yana hutawa ".

Hayewa yayi da É—an sauri Ummah da ido ta bishi bayan ta amsa " TOH a fito lafiya " wani irin abu na tsaya mata arai.
Kafin ta sauke numfashi.
Miƙewa itama tayi ta shige ta kama hanyar bedroom na ta ba tare da tace wa su Lina komai ba.
Ganin haka ya sa suko suka fito suka yi Sashen Uwani.
A chan suka yada zango duk sun cika kaka da surutu gashi ba wata Isasshiyar lafiya amma haka yake biye musu,shida Uwani sai dai suna ta ƙoƙarin ganin an rabu lafiya gudun kar su fara faɗace faɗacen na su dan haka da an kwata Uwani zata tare.

Su waye suka yi missing rigumar Shatou 🤗🤣😂Kar ku damu Nima ina kewar ta zamu je sashen ta next part in Sha ALLAH.

Da ga yanzu update ya koma duk bayan kwana É—aya.
Saboda na koma school lecture sai a hankali.Allah ya sa zaku fahimce ni.ngd.

_FA'EEH BG✍️_

Book one free
Book two paid#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haÉ—a document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞

Comment,share,like pls 🙏

_*💋KURMAN ƘADDARA💋*_

_©®Faiza Almustapha Murai_

_FA'EEH BG✍️_

P_____2️⃣0️⃣

*BOOK ONE*
_FREE._

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*

👑👑👑

___________________Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a ɓangararen.Yau da daɗi gobe babu daɗi.Faɗan su Leena yanzu har gaban Abba yi suke yi sai dai yayi ta faɗa shida Ummah.Tun da haka yarintar su take babu abinda zasu iya yi Musu sai fatan shiriya.
BILAL ya samu kwanciyar hankali shima ya duƙufa aikin sa kasancewar hutun da ya samu ya ƙare masa achan ya ƙarar dashi.Sai dai har yanzu baya neman Leena ko ya kira waya baya zancen ta.Haka itama babu ruwan ta dashi fushi take yi dashi mai zafi dan haka a gaban ta zasu yi waya da Reena bata taɓa cewa a bata su yi magana,wata rana a gaban ta har video call suke yi kuma tana fitowa zai gan ta sai dai bata kula ko nuna cewa ta san abun da suke yi,abun na damun Bilal ɗin sai dai ya zuba mata idanu kawai ya ga iya inda fushin zai tsaya,Ummah kuma da Abba sun zuba musu ido a cewar su sun fi kusa da ya'yan na su zasu ma sauko ne,kowa yayi mamakin fushin na ta dan tana da saurin sauka bisa ga ma Leena da bata da faɗan amma tana da wahalar sauka idan tayi fushi.
Duk abun da ƙannen na sa suke ciki yana sane dan har case ɗin Anisa da ta shiga ta yi dambe da Wanda ya daki ƙanwar Anisa ɗin,kamar yadda ta ce sai ta koya masa hankali, wanda kan hakan ya sa Uztas Babba ya zane ta tare da mayar da ita gida suspension na rana ɗaya.Sai da tayi kusan kwana biyar hakan ya sa aka bawa Nina takarda ta kai gida saboda gaba ɗayan su har ita har REENA ya ji suka yi sai dai sun ce hutun kwana biyu aka ba su ana su ajujuwan dan haka Ummah da Abba suka yarda.Sai dai bayan hutun ya ƙare har sun ƙara wani Ummah ta sha kai da zancen komawar su makaranta.Ana cikin haka sai ga Nina da Hamra sun zo da takarda suka ci sa,a Abba ranar a sashen yake dan haka suka damƙa masa aiko ya tara su su duka biyun ya yi ta musu faɗa dan babu abun da aka ɓoye a takardar ga cikakken sunan Leena nan.ALINA SALEH SADA.
Har Reena haka na ta yake rattafe an rubuta nata rashin zuwa makarantar wanda shine laifin ta kawai.
Da haka aka tasa ƙeyar su bayan an musu faɗan da ya bi taɗa yan kunnen leena ya bi ta ɗaya ya fita...
Chapter 38 · 0% Book details