← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 110

Sashe 25

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da ido yayi ma sauran alama da suke kallon ikon Allah su wuce ya rage daga shi sai wanda ke kula da motar dashi na hannun da man sa wanda suke mota É—aya dashi.
Wucewa suka yi kowannen su cike da Haushin da ya ƙunsa dan sun so su nunawa Shatou ƙarshen rashin jin ta,su yi maganin ta dan gobe idan sun dawo ba zata ƙara gigin shiga sabgar mai gidan su ba.

" Mubarak ka ba wa yarinyar nan haƙuri ".

Yana gama zancen ya shige motar sa aka rufe.Bayan ya jefa mata kallon da ta kasa fassara shi dan ƙafafun ta sagewa suka ƙara yi.

Bata samu damar yin magana ba har sai da motocin da suke gaba suka tada motocin sun fara tafiya sannan ta ce cikin ɗaga murya " Wallahi ni ba yarin ya bace kuma ban karɓi haƙurin ba dan kai nake so sai ka bamu haƙuri,kuma Allah ya isa na,mai bilicin kawai ".

Mubarak mai kula dashi wanda ya girme masa sosai kuwa haƙuri ya bata murmushi ɗauke akan fuskar sa sai dai ko kallon gefen da yake bata yi ba dan kalmar yarinyar da ya kira mata ta ɓata mata rai.

Da sauri da É—an gudu ya koma motar su yana mamakin halin wannan yarinya da uban gidan na su da yakan yi sati bai yi magana ba sai dai alama ta ido yau gashi da yin magana ta kusan seconni,a tsakiyar rana.

Daga chan cikin mota kuwa bayan sa ya jingina da seat yana sauke numfashi tare da ajiyar zuciya dan kansa ya fara sara masa da hayaniyar ta ga rana ya san sai ya kwanta ciwo wannan ranar da ya shiga mai zafi.
Kalaman ta ne da suka gama ratsa kunnen sa suka sake dawo masa " Wallahi ni ba yarin ya bace kuma ban karɓi haƙurin.... "....

Katse tunanin yayi yana jan mugun tsaki kafin a hankali ya furta " witch " saboda haÉ—a idon da suka yi babu abun da ya hango face Zallar masifar da take son sauke musu da bai jin zai iya É—aukar ta dan yanzu haka kan sa ya fara juya masa.
Idanun sa ya lumshe a hankali yana cire duk wani tunani a kan sa,yana janyo wata hadaddiyar kwalba kamar zinari sai walƙiya take yi tana ɗauke da shisha flavour,ya fara zuƙar ta yana ja da sauri kamar zai haɗiye hayaƙin gaba ɗaya.
Mubarak dake gaban mota kallon sa kawai yayi ta madubin yana girgiza kan sa.

A ɓangaren Shatou kuwa kuka ne ya ƙwace mata saboda yace mata yarinya kuma yadda yayi zancen cike da rainin wayau hakan ya sa ran ta ya ƙonu matuƙa dan haka ta fashe ma su Ramata da kuka abun da basu ta ɓa gani ba sai yau tattare da SHATOU kowaccen su ta kasa iya furta komai sai ma yar kallon kallon da ake yi tsakanin su kowaccen su ta kasa furta komai.

Jawairiyya ce ta yi ƙarfin halin furta " SHATOU kiyi haƙuri idan ma dan haƙurin ne mun yafe masa ".

Wani irin kallo ta jefawa Ramata da hawayen ta jage jage a kan ido kafin ta ce " wallahi ba su ci ban za mugu kawai mai jajayen Kunnuwa dama an ce Turawa mugaye ne basu son baƙar fata ".

Tayi zancen tana share hawayen ta da suka tsaya chak.

" Ai nida ke ba baƙaƙe muke ba inda ma su Ramata kika ce ".
Amina tayi zancen tana kallon SHATOU.
Suko su Ramata kallon ta suke yi cike da harara.Itako murmushi kawai tayi dan ta san gaskiya ta faɗa ba ƙarya ba.

" Yanzu dai muje fara zuwa gidan su Ramata daga nan kowa ta je gida ta chanza kaya Ni na wanke fuska ta kar malam ya muna faɗa bamu dawo da wuri kar baƙin su zo muna nan,dama ina son na ga wani Shegen ne aka saka mu wahala saboda shi ".

Ranka ya suka yi zuwa gidan sai dai kafin su isa Shatoun sai jini take yi wai kamar ita wani mai jajayen kunne zai kirama yarinya ita da Inna ni ta daÉ—e da yaye ta.
Nan dai su Amina suka fahimci kalmar ce ta saka ta kuka.Suko sai yaba kyaun sa suke yi cike da santi kowa na faɗin albarkacin bakin sa,har da faɗin ba su zaci yana jin Hausa ba.Ita kuwa tana kushe sa tare da zagin uwayen sa da ta manna masa su Elizabeth da donald trump wayen da ta ɓa jin su a wani karatu da aka musu ana bada tarihin ƙasashe shine ta riƙe sunayen kuma sai aka yi rashin sa,a ba dai dai ta riƙe sunayen ba.

A gidan mahaifiyar Ramata da suke kira Inna faÉ—a tayi ta musu na rashin kallon hanya gashi garin haka sun jawa kan su wanka da ruwan kwata kwata dan basu yi mata bayanin asalin abun da ya faru ba sun ce mai mashin ne ya zo wucewa ya taka kwatar ta wanke su duk da haka bata yarda ba duk da SHATOU ce ta bada labarin.Wanda su basu san amfanin hakan ba,ita kuwa kar faÉ—an yayi yawa ne ya sa ta ce haka.
Babu ɓata lokaci suka fito saboda suma sauran sun chanzo kayan makarantar su ramata ce kawai suke jira dan ta fi wankuwa da ruwan dole sai da ta watsa ruwa.

Ficewa suka yi bayan sun mata sun tafi ta musu addu,a da tuna musu da kiyaye hanya.
Tunda suka fito suka yi ta fanfalan gudu dan sun san sun buga latti daga zuwa cin abinci wanda ba ma bari ake yi ba amma suka yi sa,a aka bar su.
SHATOU ce a gaba cikin su dan tafi su gudu nesa ba kusa ba basu dakata ba sai tsakiyar makarantar su dan a sake take babu ko ƙofa bare gate sai filin Allah da take zagaye dashi.Turus ta ja ta tsaya tana ƙarewa motocin kallo ƙirjin ta na sama yana ƙasa tana tuno abun da ya faru ɗazu,tana tsoron a ce sun faɗa ta san in haka ne dole za,a dake su,dan ta san tabbas ƙarar su ce suka kawo,sai dai ta san bugu bai kashewa dan haka ta kwantar da hankalin ta..Haka suma su Amina tsaye suka yi cike da macewar jiki, malam Yusi ne ya hango su daga chan gefe aiko ya taso da sauri bai ce musu ƙala ba sai alamar ido da yayi musu,su shigo a hankali yana nuna musu haɗaɗɗiyar kujerar da yake zaune ya haɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya ita bata ma san akwai irin wannan kujarar a ƙauyen ba bare ma cikin makarantar.Cike da mamaki take bin bayan kujerar da kallo sannan ta na ƙarewa mai riƙe da lemar sa kallo ganin kowannen su a natse,kamar wani abu ya kawo su ba abun da take zargi ba, sai A lokacin kuma ta tuno da baƙin da zasu yi kenan shine baƙon ta faɗa a cikin zuciyar ta.
Gaba É—aya yaran kowa zuba ma Shatou idanu yayi ganin yadda suma kan su masu tsaron na sa da sauran jama'ar da ya zo da su suke kallon su musamman SHATOU.
Shi dai bai lura da komai da ke faruwa ba saboda hankalin sa na kan abun da yake dubawa, sai da ta tsayu agaban sa, saboda dama tana cikin wayen da ake ji da su anan makaranta ko mai gari zai zo ko baƙo tana cikin ɗalibban da ake ajiyewa gaba saboda tana da tsafta,da ilmi gwargwado ko yanzu tsaf take sai fuskar ta da har yanzu take nuna alamar an jiƙata da ruwa da kuma ɓacin ran da ya taso mata na sa.
Ido cikin ido suka haɗa ido dai dai lokacin da ya gama kallon duk bayanin makarantar da abun da ake buƙata na bayanin da p.a ɗin sa da suka tattara a yanzu bayan gama zagayen da su ka yi yanzu.

Lumshe idanun sa yayi yana sake buɗe su sai yanzu ma ya lura da uniform ɗin makarantar ashe kalar nata ne.Haɗe fuska r sa yayi ganin yadda take buɗe manyan idanun ta alamar ƙiriss take jira tayi rashin kunya nan gurin tun da ta ga ba,a mata komai achan ba.
Su Ramata shan jinin jikinsu suka yi suma kowaccen kamar an tsamo ta a rame tsoro ya cika zukatan su,su tsoron su ace Dagske ya bada labarin abun da ya faru ko ƙarar su aka kawo dan su har yanzu ba su yi zaton shine baƙon ba ganin sa yaro ne ba irin babba da ake magana ba.
Chapter 25 · 0% Book details