Sashe 55
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
" Na ra sa yadda zanyi da matar nan wállahi ta san bana buƙatar ganin ko ɗigon jinin ta ne a kusa dani amma wallahi saboda muguwar gulma da munafunci musamman take Turo su gaisuwa waje na har Babban su,Shin dole ne bana so wallahi bana kaunar ta ko kaɗan da ina inada yadda zan yi da ita da tuni nayi ".
Hajiya Sa'ada ce ke zancen tana kishingide kan mahehen gadon ta na alfarma daga ita É—an towel wanda ya rufe mata jiki da alama daga wanka ta fito sai hular wanka akan ta.
Ban san abinda aka furta mata ta chan ɓangaren ba na ga tayi dariya kafin ta sake cewa " Ki bar Ni da ita wallahi zan yi maganin ta,ke ni har mai gidan ma yanzu mugun Haushin sa nake ji yayi tafiya Lagos kwana biyu da suka wuce da ya dawo ɗaki na ya kamata ya sauka amma wallahi Sashen matar chan ya sauka da na kalubalance shi sai ce mini yayi ai ya'yan sa kawai ya je gani da yayi kewa kiji munafunci fa,Sai yanzu nake jin dana sani matuƙa akan ƙwayoyin hana haihuwa da na yi ta bankawa kaina,wallahi tunda likitota suka ce sai an cire mahaifa ta ta lalace nake cike da tashin hankali haryanzu da aka zare ta bana samun isasshen bacci mai daɗi Mabaruka "
Handsfree ta saka wayar ta sauko ta zauna kan mirror da ke wadace da kayan gyara fata sannan ta cigaba da sauraren maganar da ake yi ta ɗayan ɓangaren " Sa'ada sai da nace Miki kar ki yi,amma kika rufe ido bakya son haihuwa da wuri yanzu gashi nan ai mu kan mu kin barmu cikin damuwa, kuma nace ki karɓa yara ko na dangi ne yan ƙanana ki raina kin kasa kin fison baƙincikin Barirah da wannan su kai ki ƙasa,ki na kallo zata kwashe komai ita da ya'yan ta ga dukiya har ba a san iyakar ta ka ba amma babu magajin ki ai na yi baƙuncikin wannan lamari ".
" Hmmm Ba zaki gane ba ne,Bana son sai na gama wahala da yaya su koma gun mahaifiyar su ne su bar Ni da ciwon zuciya da ƙunci shi ya sa kawai na karɓi kaddara ta hannu biyu,kuma bana fatan wata rana Saleh ya san da wannan maganar tunda bai san komai ba akan hakan sanin sa kawai bana haihuwa dan haka na haɗa baki da likita ya faɗa masa "
" Allah ya kyauta ai Bama zai sani ba ''
" Yanzu dai zamu yi magana zuwa gobe in Sha ALLAH idan na samu time zan shigo sai mu ga abun yi dan matar nan da alama ba tsaye take ba Bayan saye zuciyar shi da ya'ya har da wani sharrin da ban Dan Barirah da ganin ta nan macijin sari ka noce ce,zan shigo dai zamu yi magana "
" Tau yayi yar uwata Nagode ki gaida Alhaji Mamman da yara " " Zasu ji in sha ALLAH bye "
Daga haka suka yanke kiran.
Tsaki ta ja tana cigaba da mirza mayukkan ta hankali kwance.
Numfashi ya sauke da ajiyar zuciya tun bayan sauke wayar kunnen sa yake kallon wayar yana jin sautin kukan nata har tsakiyar kan sa.Murmushi ya saki a hankali kafin ya furta " Ni kowa ye zai kwashe mini wannan rigimammiyar ƙanwar ta wa,hankali sai baya yake yi "
" Allah ya shirya mini ku twins "
Miƙewa yayi ya shige rooms ɗin sa dai dai nan Ab ya shigo da Aiken da yayi masa.
Wayar sa ya kira hakan ya sa ganin Ab ne ya É—aga " shigo " Kawai yace masa ya katse kiran.
Cikin haÉ—aÉ—É—un Rugs dake wadace da falo mai kyau da ya ji dark purple light rugs and curtain komai sai san Barka ko ina tar ga wata haÉ—aÉ—É—iyar tv dake ta aiki.
Sara masa yayi kafin ya miƙa masa wata yar takarda.
Karba yayi yana dubawa ya ja tsaki bai ce ma AB komai ba yayi gaba ya shige Bedroom ɗin sa, Ab kan sa kawai ya girgiza ya fice dan shi kam bai san amfanin aikin da ogan sa ya saka shi ba shi inda ma ya ga yarinyar da zai iya ma binciken ƙwaƙwaf amma ba kowace asibiti ne suke iya bada bayan nan mara lafiya ba,saboda doka ce bare Babbar asibitin SHAHABS ta manyan mutane.
Aiken da BILAL yayi wa Ab kuwa shine tura sa asibitin ne ya nemo masa bayanan wannan mara lafiya É—in dan mugun tausayin ta ne ya É—ar sa masa lokaci É—aya ya kasa samun natsuwa yana son tallafa mata ya kai ta wajen wani Babban likita a Chaina,kafin su koma Lagos ya so su gama komai da ya dace.Sai dai yanzu bayan zuwan AB ya samu labarin an sallame ta sannan sun hana bayanai dan komai nata da ban yake hakan ne ya sa ran BILAL sosuwa ya ta shi ya shige daki yana jan tsaki mara sauti da tunanin shisshigin me zai kai sa dan haka take ya watsar da maganar bin ta da addu'ar samun lafiya.
Shiru ya zuba ma wani hoto guda biyu da ke a jiye da bandan ɗaya na mace ne tana sanye cikin farar abaya ta yane kan ta da veil ɗin sa tayi kyau sosai a kallo ɗaya zaka mata san cewa Babbar mace ce sai na biyu hoton shima dai Hoton Matashin magidanci ne sanye da ƙanana kaya yana ɗauke da briefcase yana murmushi an masa hoton kamar dai wajen taro aka ɗauke shi ma a hoton.
Wani irin abu ya haɗiye mai kauri a maƙoshin sa wanda yake ta kai kawo tun zuba ma hotunan biyu idanu.Hawayen da suka cika idanun sa ne ya shafe kafin ya fashe da wani irin kuka mai cike da kewa da raɗaɗi da baƙin cikin da yake jin ba zai taɓa gushe masa ba,wazai tun kara ya warware masa wannan lamari,me ya sa sai shi mai ya sa,zuciyar sa ta kasa gasgatawa me ya sa ya furta a bayyane da ƙarfi yana buga kan sa da kan gado kafin ya mike cike da ƙunar zuciya ya shige toilet kan sa ya sakarwa ruwa yana yi hawaye na silalar masa wani irin raɗaɗi a zuciya na sake mamaye sa.
*Wani irin kaɗawa iskan wajen keyi tana bada wani irin ƙamshi mai narka zuciya da ruhi yadda wajen ya wadatu da shuke shuke da yanayin ruwa dake gudana a ƙasa zaka tabbatar ta Babban waje ne baida hayaniya ko kaɗan a wajen kowa yana harkan gaban sa ne babu ruwan kowa da kowa,a gefe akwai hadaɗden restaurant dake tsare gwamnin burge wa.
Zaune yake daga shi sai guntun wando ya mike ƙafafun sa ɗaya akan ɗaya kan yar rumfar da yake cikin ta ya ɗaura hannayen sa kan ƙeyar sa idanun sa kuwa sanye da wani irin faskeken rado mai kyau black wanda ya ƙara bayyanar da ainahin zubin kyaun sa.
Wayar sa ce tayi ringing kusan sau uku kafin ya ɗan ɗago ya zuba mata idanun sa wani kiran ne ya sake shigowa dan haka a hankali ya miƙa hannun sa ya zari wayar.
Abbu shine abun da ya furta a ƙasan laɓɓansa sa.
Goshin sa ya É—an dafa dan bai yi zaton Abbu bane yayi zaton Mubarak da zai zo yau ne yayi zaton ya iso yana tunanin ya je ya dauko sa ne kamar bai san hanya ba.
Sai da kiran ya katse sannan ya bi bayan sa.
" Assalamu alaikum Abbu "
Shine abinda ya furta kafin yayi shiru.
Abbu cike da farin ciki ya amsa yana sauke ajiyar zuciya tare da sakin Murmushi mai sanyi.
" Shine bazaka neme ni ba yau kusan kwana biyar MAHAJ kamar ba ka ma yi kewa na ba ".
Murmushi ya saki mai sanyi kamar yana gaban Abbu sannan ya ce " Abbu kana lafiya ai Mubarak yana faÉ—a mini komai na shiga busy ne saboda mun fara preparations na presentations É—in da zamuyi " shiru yayi har Abbu ya fidda rai da zai kara magana ya ce " Abbu ai kana raina daga ku har su Ayya ".
Murmushi Abbu yayi sai kuma ya ji hawaye sun tarar masa na tausayin É—an na sa da yake cikin kewa ta kulawar mahaifiya da bai samu ba.
Ajiyar zuciya MAHAJ ya sauke dan shi da Badan mahaifin sa ba sai Samrah da babu abun da zai saka shi yawan komawa gidan ma Hutu sai dai yayi zaman sa nan.Amma ko yaya ne yana duba farin cikin da zai gani akan fuskokin Wayen nan mutanen guda biyu.
" Aikin Ƙauyen ne an fara shi tun kwana biyu da suka wuce,na san kana da labarin komai ".