← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 110

Sashe 56

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru yayi ma Abbu hakan ya sa Abbu sakin guntun murmushi dan ya san ba tan ka masa zai yi ba.
" Allah ya sa ka da Alkhairii,ya sa matar Auren ka ta zame maka ta gari,ya baka yaya masu albarka da maka biyayya kamar yadda kake yi mini ".
Haka kawai ya ji bakin sa yayi masa nauyi dan haka ya kasa Amsawa da Amin.A duk lokacin da mahaifin sa yayi masa irin wannan addu'ar wani yanayi yake tsintar kan sa ko yanzun dai hakan ya samu kan sa.Yana jin kamar yana yiwa mahaifin sa zagon ƙasa domin duk wannan zancen na mahaifin sa babu shi Aran sa ko nan da shekara goma ne,ba zai so rayuwar da ya ta so ta kaɗaici ya yan sa su yi ta ba dan haka bai shirya ma zuwan kowa karƙashin sa ba hasalima private life ɗin sa itace yake ganin tafi dacewa dashi har ƙarshen rayuwar sa saboda yadda ba ya son takura.
Abbu bai ji komai ba na kin amsawar ta sa , sai murmushi da yayi bai yi masa maganar ya amsa ba yau kamm, shi kan sa Mahaj murmushi kawai ya yi cikin mamaki ya É—an sauke wayar sai kuma ya tsinkayo Muryan sa yana furta " Mubarak zai sauka in the next thirty minutes in Sha ALLAH ka tura a É—auko sa ko kaje da kan ka ".
Baki ya tura gaba kamar Abbu na ganin sa jin shirun sa ya sa Abbu dariya kaÉ—an ya ce " kun fi kusa,ka kula da kan ka bye,Allah yayi maka albarka".
" Amin " ya furta a ƙarƙashin laɓɓansa sa da suka ƙara yin jaaa sosai dan sai ɗan taunar su yake yi a hankali miyan bakin sa na ƙara musu sheƙi da nuna Zallar yadda suke a taushi.
Headphones ya makala dake gefen sa bayan ya sauke ajiyar zuciya yana ƙara zuba wa wayar ta sa manyan idanun sa.
Ɗan lemu dake gefen sa kan wani table ya ɗan yi sipping wanda ke a kan wani haɗaɗɗen cup yanayin dai na turawa haka irin wanda ake saka mocktail,jaaa yayi kaɗan da straw ɗin ya ajiye yana mai da idanun sa ya rufe ruff iskan da ke shiga jikin sa na ƙara masa wani jin daɗin wajen dan yadda ta garwaye da turaren sa mai Shegen ƙamshi sai kayi zaton shine mallakin wajen gaba ɗaya.

A ɓangaren shatou dukkanin kwanakkin nan da suka shuɗe kullum sai Iro ya tare ta a hanyar makaranta ko aika,har ta kai yanzu ba ta son fita farautar ma da ta ke yawan matsawa idan ba,a je da ita ba yanzu bata zuwa,su Baffa na sun sakawa ikon Allah ido dan kowa ya fahimci Iro dai son Shatou yake yi duk da taƙi barin sa ya faɗa ɗin ma dan ga tsau ga tsau haka take jefa masa magana mara daɗi amma duka ya shanye.Yau ma daga wajen farauta ta fito saboda ta gaji sai ta baro su Baffa na chan Ita dai saboda gajiyar da ta kwaso bata san cewa akwai mutun bayan ta ba hakan ya sa ta ke tafiyar ta hankali kwance dan ta rage guje gujen yanzu.
Ta kawo wajen wata bishiya kenan kawai ta ji mutun bayan ta ya ce "keeeh "
Irin abun nan na ka bawa mutun tsoro cikin soyayya shine Iro ya yi mata aiko ta zabura ta zunduma a Guje ko waigen sa ba tayi ba, shima bayan ta ya bi yana ƙwala mata kira yana dariya cike da nishaɗi. Fahimtar shine hakan ya sa ta ƙara giyar gudun cike da Haushin sa.Su Ramata ne suka tare ta da Amina suka shaaa gaban ta hakan ya sa ta dakata dan har ta yi niyyar wuce su.Sai kuma ta ci burki tana Hararar su.Dai dai nan shima Iro ya iso wajen yana sauke numfashi yana cewa " Haba Shatou ke ko tausayi na baki ji kin fa gane Ni amma kike cigaba da gudu na haba Shatou na".
Wata uwar Harara ta jefa masa kafin ta kalli su Amina da suka yi tsuru tsuru suna kallon Iro ganin yadda ya ƙara komawa kamar ba shi ba abokin faɗan Shatou wai yau shi ke kiran Shatou da shatoun sa.
Dariya suke son yi babu dama dan shatou bata ƙaunar ko tsayuwar su ne duk sun shaida hakan yadda take tserewa kafin a tashi makaranta saboda shi har wajen wasannin su ta daina zuwa sosai saboda shi dan duk wata hanya da ya san zasu haɗu sai ya bita,ƙofar gidan su idan ya je zai gaji da tsayi yayi gaba.
'' Nifa wallahi Iro ka fara isata wallahi zan kai ka ƙara wajen mai gari haba duk ka bi ka ta kura mini kamar bani da gata saboda jarabar ka ko kofar gida ta daina burge ni,ni kan wallahi ga mai gari zan kai ka ya ƙara mana kashe di "ta kai ƙarshen zancen kamar zata saka kuka musanman da ta ga ko ajikinnsa sai ma Murmushi da yake ta saki dan shi wata dama ya hango a nan take wajen.✍️

# 2025
# Hausa novel
# Love,and romance story
# Labari mai tafiyar saƙar gizo gizo
# Soyayya mai tsayawa a zuciya
# Kaddara mai cike da ƙalubalen rayuwa
# zamba ma yar aike ce.
# Cuta mai mai ban tsoro.
# Mummunan Zuciya kai bawa mahalaka
# All in one story
~*KURMAN ƘADDARA*✍️~

# Wannan labari na kuÉ—i ne akan Naira#800

# _FA'EEH BG CE✍️_

Book one free
Book two paid N#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haÉ—a document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Daga Alƙalamin✍️
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞

Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔

_*💋KURMAN ƘADDARA💋*_

_©®Faiza Almustapha Murai_

_FA'EEH BG✍️_

P_____2️⃣7️⃣

*BOOK ONE*
_FREE._

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t

*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*

♣️♣️♣️

Fuuu haka ta wuce ta bar su nan shi da su Amina ana kallon kallo kafin ya ɗan bi bayan ta da sauri sauri sai dai kafin ya an kara ta zunduma a guje dan ta fahimci muddin ba haka ta yiwa Iro ba,ba zata zauna lafiya ba.Dan bata taɓa jin zata iya tsayuwa dashi.
Koda ta shiga gida babu sallama Inna ni na aikin wanke kayan da ake zubawa shanayen Baffa na abinci wayen da suka yi datti.Dan tun safe bayan Shatou ta gyara musu wajen su ta ce ta wanke su amma bata yi ba saboda shiriritar ta,sai ta ɓuge da bin su Baffa na Farauta.
Kai kawai Inna ni ta girgiza bata iya ce mata komai ba sai cigaba da aikin ta dan ko bata tambaya ba ta san cewa Iro ne ta ke yiwa wannan guje gujen.Ta rasa dalilin da ya sa shatoun bata ƙaunar Iro ko kaɗan domin ga alama nan ko tsayu wa ta arziki ta ka sa yi da shi,itama wani farin ciki take ji duk da bata jin zata yi mata auren wuri kamar yadda ake yi a Ƙauyen na su duk da ƙalubalen da zasu fuskanta tana son Shatou tayi karatu mai zurfi ta taimaki mutanen wannan ƙauye ta mayar da kyauta da karamci.
Zaune ta kai daɓass tana huci da sauke numfashi kafin ta ce ''Inna ni dubi dan Allah yadda Iro ya sako ni gaba wallahi na kusa kai shi ƙara wajen mai gari "
" Aah ba ayi haka ba,kefa matsala ta dake rashin wayau shi iron ne meye dalilin zuwan sa wajen ki " ?
Ƙin bata amsa Shatou tayi dai zumɓura baki.
Murmushi Inna ni tayi kafin ta ce " to tunda kin san abinda ke kawo ɗan mutane ai sai ki bari ki ji abun da zai faɗa daga baya sai ki san abun ce masa,kuma banda wulaƙan ta wa Shatou rayuwa bata da tabbas karki wulakanta kowa domin baki san ɓoyayyen Alkhairii sa gare ki ba,sannan baka san mai taimakon ka ba dan haka idan ma tsayawa ne ba kya son yi dashi ki gaya masa ke an hana ki tsayuwa da kowa a gida faqat ".
Bakin dai ta ƙara tun zurawa gaba bata ce komai ba.
Chan kuma kamar an tsakure ta,ta mike tsaye ta kalli Inna ni ta ce " amma ai ni Inna ni bana son sa kuma ni ba a ƙauyen nan zan yi aure ba miji na birni yake shi ya sa bana kula shi duk ga su Amina nan amma sai ni da ya raina ".
" Sannu matan É—an birni,Haba SHATOU Soyayya ce fa "
Baki ta kara turawa sai kuma kunya ta kama ta tayi kasa da kan ta tana dariya da ɗan murmushi Inna ni dai bata ce mata ƙala ba.
Sai kuma ta matsa ta fara ɗauraya wa Inna ni kwanonin tana yi tana langaɓe kai maganar Inna ni na bata dariya wai Sannu matar ɗan birni,soyayya ce fa.
A haka suka gama aikin tare.
Su ko su Amina gaba suka yi kowacce su tayi gida suna ƙara mamakin Iro suna zuwa gida kuwa kowaccen su ta fara bawa innar ta labari suna dariya suma iyayen na su dariya abun ya basu duk da sun san haɗin mai wahala ne sai suka bi Su da addu'ar fatan Alkhairi.
" Ina su Baffan naku,ba tare kike da su ba " ?
" Ni na gaji ne shi yasa na tafowa ta "
" Shine wanchan uban nacin ya biyo ni".
Shatou ta bawa Inna amsa tana ƙara tura baki gaba.
Komai Inna ni bata ce ba sai karɓe wanda yayi saura a hannun Shatou dan ta kasa dauraye shi sai juya shi da ta keyi har ta fara jiƙe kayan jikin ta.
A tare suka kaiwa Shanayen da sauran dabbobin abincin su dan tun da safe sunyi gyaran wajen ita da Bibu saboda babu makaranta yau É—in.
Chapter 56 · 0% Book details