← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 110

Sashe 2

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yar matashiyar matar dake zaune a kan tabarmar kaba ce wadda kamar ta take kamar an tsaga kara da Shatou saboda ita ta biyo bata wani kama da Baffana ta amsa Sallama fuskar ta cike da murmushi tana kallon su musamman Shatu dake ta tsallen murna na irin ƙwazon da tayi a yau ɗin duk da dama tana yawan samun abun harin ta awurin farauta amma na yau ya banbanta saboda Babban kamu tayi ba irin ƙananan dabbobi bane.
" Maraba lale maraba ".
Ta yi furucin bayan amsa Sallamar su miƙewa tayi da ɗan sauri ta riƙa ma Baffa kayan dake riƙe a hannun sa cikin sakin fuska.
Murmushin ya saki shima tare da sauke ƙwaryar naman da suka feɗe a bakin wani rafi.
"Sannu da dawowa Baffan su."
"Yawwa Sannu A'i "
"Kin san yau Mutuniya ta tayi muna babban kamu".Ya ƙara yin furucin yana murmushi.

Murmushi ta yi tana mamaki mai girma da wannan lamari nan Shatou gashi bata san yadda zata raba ta da Farautar nan ba.
A hankali ta kalli kuma ta kalli Shatu dake ta murmushi ta furta " Su Hajiya rigima an yi sa,a,Kuka fa ta zauna ta na mini harda murje murje,Allah da na same ta da sai ta ci na jaki yan nema shekara sha biyu cikin ta uku babu wayau sai rigimar tsiya,ko Bibu na yafi ta hankali ".

Murmushi Baffa na yayi yana furta " Sai gata kuwa,na so ace ta zauna ta huta,bana son yadda mutanen ƙauyen nan ke magana akan guje gujen ta ".

" Allah dai ya shirye ta indai Shatu ce sai Addu,a,Allah ya shirya maka ita ".
Inna ni tayi furucin

" Amin A'iie ". Baffa na yayi furucin yana sakin murmushi yana kallon Shatu da ta turo bakin ta gaba ganin Bibu na dariya ƙasa ƙasa ance yafi ta hankali.

Sallar la,asar kawai kowa yayi yi suka huta suka ci abinci sannan suka zauna a tare suka yi aikin yanke naman tsaff ita da su Bibu da shatu yana yi yana bata labarin yadda komai ya wakana a chan dajin.Ita ko tana mitar guje gujen da zuwa farautan na ta da yawan fita ma da take yi a sace da take ƙokarin hana ta.Amma abu ya gagara.
A haka har suka gama zuwa lokacin ta hura wuta da yangan ice da shatu tayo jiya
Har aka kusa Sallar magriba suna nan zaune suna taɓa fira tare da ƙara rura wuta akan tukunyar dahuwar naman su,wanda suke dafa wa a matsayin abincin daren su.
Wanka kowannen su yayi Sannan mazan suka wuce Masallaci dan gabatar da sallahn magriba.Suna dawowa dai dai naman yayi rugu rugu,Inna ni ta gama shirya komai da taimakon Shatu suka zauna suka ci suka ƙoshi kowannen su yayi nak.
Sannann Aka yiwa su Shatu bitar karatun su.Sallar Isha'i ce ta tashe su gaba ɗaya Sannan kowannen su ya wuce wajen sauƙe Haƙƙin Allah dan har yaran iyayen su sun sabar musu da yin Sallah a lokacin ta.
Tun da aka gama Sallolin Isha bayan dawowar su Baffa da Bibu Inna ni kamar yadda suke kiran ta,take jiran fitowar Shatu daga É—an madaidaicin É—akin na ta da yake kamar yar bukka saboda ba wani mai girma bane, sai dai wayam shiru babu labarin fitowar ta.A zaton ta ma sallar ce bata gama ba amma sai gashi har aka gama sallolin mazan suka shigo gidan babu labarin ta,sai dai dan tabbatar da zargin ta bayan shigowar ta su ya sa ta faÉ—a dakin na ta yadda taji shiru haka É—akin yake babu mai kama da shatu sai yan kayan ta da yar tabarmar ta dake da É—auke da zanen shimfiÉ—ar ta ko ina tsaf sai dai ga kayan da ta cire nan yanzu a watse ta chanza wani.
Shiru tayi bayan fitowar ta daga É—akin kafin ta nisa ta girgiza kan ta.Yawon shatu tsoro yake bata data samu dama sai ta fice daga gidan duk irin faÉ—an da take mata a banza gashi wata rana harda bugu take haÉ—a mata mata dashi dan ma Baffa na, na hana ta da kullum sai ta jibge ta.

" Ta fice ko "???

Baffa ya yi furucin yana girgiza kan sa shima fuskar wanze da Murmushi dan ko É—azu kafin su fice sallah sai da ya ce mata " banda fita Shatu a zauna gida a huta a haka yau anyi farauta Babba."
Ashe bata shiga kunnen ta ba maganar.

Kai kawai Inna ta iya É—aga masa tana zama akan sallayar da ta sha jiki wadda ta shimfiÉ—a akan Tabarmar kaba da take kai.
Charbin ta da take jaa ta cigaba da jaaa sai dai hankalin ta na kan yar ta tsoron ta ɗaya kar ta jawo musu abun magana saboda Mafaɗaciya ce ta ƙwarai shatu koda yaushe cikin kawo ƙarar ta ake gidan ta yiwa wani, wani abun daga cikin warin ta ko wayen da basu kai ta ba har manya ma in suka shiga gonar ta sai ta rufe ido ta yi rashin mutum ci shi yasa bata shiga sabgar da bata shafe ta ba saboda bata da haƙuri idan ka taɓa sai ta rama a kullum Addu,ar iyayen ta kenan samun hankalin ta na wannan yawan faɗaɗace faɗacen, idan ka mata kallo ɗaya zaka hango natsuwa a tattare da ita amma ana taɓa ta zaka san akwai ruwan rigima da suke ɓoye a cikin ta,wanda Tsokanar ta ke iya tsokalo su.

"Baffan su,wai ni Shatu ba igiya zan fara saka mata ba,tsoro nake ji ta jawo muna wata rigimar domin ban manta karon ta da É—an gidan mai gari ba da yan zu ya illata ta ga tsoro ga ban tsoro kura,bana son fita wasar nan ta Dare".

Murmushin Baffa yayi jin Furucin Inna ni kafin ya sauke Kan sa ƙasa Yana kallon Bibu dake jin kamar ya saka kuka jin mahaifiyar su ta fara zancen ɗaure Adda shatu.

" Baza,ayi haka ba ai ".

" Na san abun da zanyi A'ie."

Bata iya furta komai ba ta miƙe daman bata yi shafa'i da wutiri ba ta kabbarta Sallar ta,.Sai dai Ranta a jagule yake matuƙa.Kusan kullum sai ta mata faɗa Dan shi Baffa bai son ana mata faɗan ma ko kaɗan idan tayi sai yayi ta Rarrashin ta yana mata faɗan cikin hikima a cewar sa yarinya ta ce,kuma ya san duk wanda ta taɓa shine ya fara tsokanar ta.Bibu kuwa da Baffa cigaba da bita karatun Alqur'anin suka yi a tare hankali kwance duk da rabin hankalin su na kan Shatoun su.

A ɓangaren Shatu kuwa tunda ta samu ta fice ta ke fanfala gudu kamar wadda take harin abu farautar ta a daji bata tsaya ba sai inda suka saba tsaya wa suyi wasannin su ita da sauran ƙawayen na ta.
Sai dai yau anyi rashin sa,a duka basu taru gurin ba sai ita sai mazan dake wajen yan na iya masu zuwa kallon su.
Wuri ta samu ta zauna zaman jiran su saboda zasu kai su goma amma manyan ƙawayen ta su uku ne kuma kan su komai tana iya yi mafi yawan rigimar ta akan su ne su aka taɓa saboda kowa na tsoron shiga sabgar ta.

" Yan mata ".!!

Duk yadda take jin sautin na shiga kunnen ta bata jin zata ko kalli mai maganar Dan bata da lokacin sa,saboda ta raina sa tun asali,kuma ta san kowane ne.Ibro ne É—an gidan mai gari da yake ta Bibiyar ta..

Like and share.

Ku ta yani Sharing saboda Allah.🙏

Daga Alƙalamin✍️
Firstlady🙌 (Fa'eeh BG)
GIMBIYAR TASKIRA 👑

08069059746
For more information👆

UPDATE👇

https://chat.whatsapp.com/BzXaAD3pB6yJ1wBBrkE4V0

Masu son ganin ƙarshen labarin sai suyi following channel ɗita.👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*💋KURMAN ƘADDARA💋*

©®Fa'iza Almustapha Murai

Daga Alkalamin✏

👄FA'EEH BG👄

💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18.A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

______________💔

_Wannan Shafi naki ne baki ɗaya masoyiya ta AMMYN LAYLAH 😘💞 Ina godiya da kulawar ki a kaina da wannan labari,Ina roƙon Alkhairin Allah ya kai Miki A duk inda kike,kuma ya raya muna Love(Layla).🥰🤲🏾_
______________💔

_Daga marubuciyar littafin_
*A MAFARKI NASANTA*
*RAYUWAR MU A YAU*

'''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''’'''

*BOOK ONE*

Free pages👌

P..0️⃣2️⃣

Shiru ta masa tana fatan kar ya ƙule ta ta masa rashin mutunci kamar na ranar Da ya tashi kaɗe ta, ta fahimci bai da zuciya bai ji kashe din da aka musu ba a tsakanin su.Tunda har zai iya Binta a karo na biyu.Ganin ya dawo ta gaban ta yasa ta ƙara ɗauke kanta tare da rufe Hancin ta irin na wari yake yi dan ta ɓata masa rai da siffar wulaƙanci duk da ba warin yake yi ba.
Shiko Iro murmushi kawai ya saki na yaƙe sannan jiki mace ya ja baya yana komawa cikin yan uwan sa da suke masa dariyar abun da ta yi masa duk da ya san laifin sa ne,amma zai yi maganin ta zai cire mata girman kan dake kan ta.

" Ya kamata fa ake ce raini dake tsakanin ka da Yar shilar chan yarinya ba komai a ƙirji sai ƙwailanci amma kana ta Bibiyar ta tana dizga ka,yaro mai ilmi duk ƙauyen nan kana Buz guy,gaskiya Iro ka yi tunanin abin yi dan ni waccan yarinyar tsafff zan iya karya ta karass na watsa ƙasusuwan ta a rafi "
Chapter 2 · 0% Book details