← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 110

Sashe 23

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Guraren Ƙarfe Biyu ta buɗe idanun ta da suka gagara rufuwa da bacci,dan ta daɗe haka kwance.Miƙewa tayi zaune tana kunna fitilar ɗakin na ta.Idanun ta da suka yi nauyi ta ƙara buɗewa kafin hawaye suka silalo mata masu zafi.Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi kafin Kuka ya kubce mata mai tsuma zuciya kamar ko yaushe sai da tayi mai isar ta sannan ta share hawayen ta.
Tana nan zaune yadda take bacci ya kwashe ta.
" Yadda suke kuka suna ƙoƙarin rungume ta ne ya sa ta zuba musu ido tana kallon su ta kasa rarrashin su wata mata ce da baƙin mayafi fuska a rufe ta zo da sauri ta janye su jikin ta da ƙarfi wanda ita kan ta har da zabura tayi " Wanda ya sa ta miƙe firgigit daga zaunen da take tana buɗe idanun ta daga nannauyan baccin da ya ɗebe ta.Duk yadda take son tuno fuskokin da ta gani yanzu a mafarkin na ta a bin ya gagara dan haka ta miƙe ta fice alwallah ta ɗauro ta sallah tayi addu,oi sannan ta miƙe ta koma kan ɗan madaidaicin gadon na ta.

Yau an tashi da abun farin ciki a cikin kauyen kasancewar zasuyi manyan baƙi domin ɗan gidan babban ministar ne na Abuja zai zo duba yadda tsarin makarantun su yake kafin a fara wani abun.Dan haka yau ta ko ina su SHATOU basu samu sauƙi ba tun da suka je makaranta sai aikace aikace suke yi.Tana son guduwa gida abu ya gagara dan yunwa take ji dan haka saboda Abar ta taje ta san malamin su ba zai hana ba idan ta tafi tare da su Ramata ta san zai yarda zata dawo.Da ƙyar da rarrashi ta roƙe sa ya bar su suka fice daga makarantar da zummar zasu dawo.
Sai dai Shatou ba yunwar kaɗai ba ce ke damun ta ta gundura da aikin ne kawai a cewar ta dan wani banza zai zo sai a saka su aiki kamar tumakai dan duk da aikin nata na shan ruwan tsuntsaye ta cire jin Haushin aikin da aka tataro musu ba, dan har da su cirar yana da cire ƙananan hakukuwa,duk yadda prefect suke matsin lamba da malammai amma ita tana gefe tana ragwanci bakin ta ture kaɗan take jira ayi ta ruwan masifa tsakanin ta da prefect ɗin sai dai fahimtar halin da take ciki sai suka fita iskan ta bayan malamin su ya basu umurni kuma ko ba dan haka ba sun san halin ta.

***

" REENA kin san jiya mafarkin me nayi,mafarkin fuskokin mu nida ke nayi,muna kuka muna miƙa hannayen mu ga wasu hannayen da ba,a ganin fuskokin su wai muna kuka suma suna kuka ".

LINA ce ta yi Furucin bayan sun gama sallar asuba.
Kai REENA ta ɗaga alamar tunani kafin ta furta " Me yasa baki bari kika ga ko su waye ba kafin ki farka ".ta kai ƙarshen zancen cike da yarinta kamar yadda LINA tayi zancen.

" Mtsww ke fa Wawuya ce waya ce Miki ana iya saka wani abu a mafarki,kai ba sai dai ka gani ba ne ".

LINA tayi Furucin tana cigaba da tofa Addu'a.

" Mtsww Ni dai ba Wawuya ba ce wallahi,idan kin san Wawuya nake mai ya kawo ki bedroom É—ina ai da sai ki tsaya naki".
REENA ta kai ƙarshen zancen tana ɓata fuska kamar zata yi kuka.

" Uban me zai shigo da ni nan ni ma ban san wanda ya kawo ni nan ba,da ba zan kwanta a wannan banzan gadon ba " Ta kai wa bed É—in bugu kamar irin zai ji.

Kuka REENA ta fashe dashi kafin ta furta " Wallahi ki ka ƙara dakar mini bed Allah ya isa na muguwa ".

Dariya LINA ta ƙyalƙyace da ita kafin ta miƙe ta na wani irin ja baya sannan ta kai wa bed ɗin mugun shuri da ƙafar ta,ta dama har da yin suluka kamar wata Chinese sannan ta haye bed ɗin.

Kuka ne ya ƙara ƙwace wa REENA har da murje murjen ƙafafu an daki gadon ta.
Tana furta " bai yafe ba wallahi,kuma sai na rama ma sa ".
Miƙewa tayi tana cire hijab ɗin ta dogo har ƙasa kafin ta haye gadon ta faɗa kan LINA da ke ta tsalle tana dakar bed ɗin tana dariyar ƙeta jin REENA na ƙara giyar kukan ta.

Tana hayewa kan gadon kuwa kamar dama LINA jiran ta take ta faɗa mata aiko ta hau dakar abar ta har sai dai ta kai tun REENA na ƙara ta kai Muryar ta bata fita kafin ka a an kara ta sume ga jini ta bakin ta yana gangara kaɗan.

Ummah da take jin hayaniyar su ƙasa ƙasa ne ta leƙo tana tambayar lafiya.

" Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un "
" LINA me nake shirin gani,Allah ka rabani da mugun ji da mugun gani Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un LINA kashe kashe mini ita zaki yi ".?

Ummah tayi furucin Ganin Yadda LINA take jibgar REENA dake kwance a Kasan ta bata motsi kuma duk da haka bata daina jibgar ta ba kamar Allah ya aiko ta.

LINA da bata fahimci aika aikar da tayi ba ne saboda yadda idanun ta suka rufe ta juyo da sauri tana kallon Ummah kafin ta mai da idanun ta kan REENA dai dai zaro idanun ta da faɗuwar ƙirjin ta ganin yadda jini ke zuba bakin yar uwar ta hannu ta aza a kai ganin babu numfashi a jikin ta.Miƙewa tayi tana sauka daga kan ta kafin kuma wata irin juwa ta kwashe ta ta faɗi ƙasa yaraff babu numfashi.

Ummah dake riƙe da REENA hankalin ta ƙara tashi yayi hakan ya sa ta miƙe cike da sauri tafi ce tana ƙwala kiran Sunan Soja.
BILAL da bai daɗe da shigowa bane bai ko isa sashen sa ba ya ji kiran mahaifiyar ta sa cike da tashin hankali.Juyowa yayi da sauri yana dosar sama dai dai lokacin da itama ta iso ƙofar ɗakin REENA ta nuna masa da sauri ta ma kasa magana.

Shigewa yayi da sauri cike da tambaya sai dai bata bashi amsa ba.

Abun da ya ci karo da shi ne ya tayar masa da hankali ganin REENA kwance kamar gawa fuskar ta ta kumbura lokaci É—aya ta chanza kamanni kamar wadda ta yi dambe a filin dambe.
Kan ta yayi da sauri yana ɗan marin fuskar ta yana kiran sunan ta sai dai ganin bata motsa ba ya sa shi tunani wata mafita kallon bedroom ɗin ya fara kafin ya hango LINA itama yashe a ƙasa idanun sa ya waro wani sabon tashin hankalin na mamaye sa ga tambaya rass dafe da zuciyar sa babu amsa.Ummah ce ta shigo da ruwa mai sanyi a hannun ta.Hankali tashe ruwan ta yayyafa ma LINA har sau biyu sannan ta miƙe a razane sabo da tashin hankali ne ya kai ta ƙasa da tsoro.
Miƙa ma BILAL ruwan ta yi ya yayyafa ma REENA baiwar Allah tana jin sanyin ruwa ajikin ta ta buɗe idanun ta a galabaice sun yi jawur da su na azaba.
Hawayen ma sun ƙafe.Zama take son yi amma ta kasa, fahimtar hakan ne ya sa BILAL miƙa ta hannun Ummah bayan ya ɗago ta, toilet ya faɗa ya haɗa ruwan masu ɗan ɗumi da zasu taimaka mata sannan yadawo ya ɗauke ta ya shige toilet ɗin da ita. Bayan shi Umma ta bi cike da tausayin REENA babu wanda ya kula halin da LINA take ciki dan kuka take ta rizga harda shiɗewa.
Ganin Ummah bayan sa ya sa shi ɗan kallon ta ƙasa ƙasa kafin ya baro toilet ɗin yana mamakin wasu halaye da Ummah take nuna wa duk da alƙawarin da ya ɗaukar mata a chan shekarun baya da suka wuce.

Ummah kuwa kan REENA tayi bata ma kula da shi ba.Cike da tausaya wa ta ke É—an gasa mata fuskar ta da ruwan É—umi bata fito daga cikin bahon ba sai da tayi kusan mintuna goma sannan Ummah ta chanza mata wasu ruwa tare da yi mata wanka ta É—aauro mata towel suka fito.
Koda suka fito BILAL ya fita É—auko first aid kit.yana shigowa kuwa kallo É—aya yayiwa LINA da ta ta kure waje É—aya alamar bata da gaskiya.Zama yayi bakin gadon yana Fiddo da maganin kashe zafi da su pain relive na oral,Tare Da maganin da zai taimaka mata tayi bacci dan ta bugu,BILAL duk da bai san abun da ke faruwa ba amma zuciyar sa ta riga ta gama amince masa aikin LINA ne musamman yadda ya ga ta takure gefe É—aya sai satar kallon sa take yi tare da REENA da ke ta sauke nishin azaba.
Shayin da Ummah ta haɗa mata yanzu ta sha kafin ya miƙa mata maganin ta sha kamar zata dawo dashi dan itama bata wani son magani.Duk da tafi LINA ita da wuya a bata magani bata zubar ba,ko ta ɓoye.
Kwantawa tayi ya lulluɓe ta da blanket yana mata sannu.Kai kawai Take iya ɗagawa sai hawaye da suke sauka kaɗan a gefen idanun ta.Cike da tausayin ta ya fice daga bedroom ɗin.
Fitar BILAL ta sa LINA jin sauƙi a zuciyar ta,dan wata irin masifa ta hango cikin kwayar idanun sa a kallon da yayi ƙara yanzu kafin fitar sa.
Ummah kuwa yana fita ta fara mata faɗa cike da ɓacin rai ta inda take shiga bata nan take fita ba.Shigowar BILAL ce da wata iriyar bulala mai harshe biyu ya sa Ummah yin shiru tana kallon sa kafin ta furta me zaka yi BILAL....

______________

🍀🌻🍀🌻🍀

A ɓangaren SHATOU kuwa gidan su ka wuce suka ci suka ƙoshi kafin suka fito suna firar su da wasannin su a hanya harda yan guje guje,Suna tsaka da tafiya su huɗu manyan danƙararrun motocin da ke ƙoƙarin mamaye yar hanyar suka ratso kusa dasu dai dai wata babbar mota mai walƙiya kamar an ƙera ta da zinari wacce duk tafi sauran kyau kuma itace a tsakiya tayi wa su Amina da Ramata, jawairiyya wanka da ruwan kwatar dake zube a wajen saboda akwai kwata wajen dan ƙofar gidan suna niƙan injin na ruwa ko wane kala sai ya zama wajen ya tara ruwan kwata,gashi ba,a tsaftace sa.
Chapter 23 · 0% Book details