Sashe 46
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Madallah to ku wucekke,har da manyan baƙi ake yau ".
Murmushi Abba ya sake yi yana kallon su Reena da suke É—an satar kallon Abba É—in su ga ko ya chan za fuskar sa da take haÉ—e.
Sai ko Gashi yanzu sun ga ya saki dan haka suka fara samun natsuwa a zukatan su.Suka fara sakin jiki babu ma kamar Reena Ita dai Leena bata wani saki fuskar ta ba.
Zama suka yi a wani Madaidaicin falo da yake É—auke da tarin littafan addini ya sha gyara sai ya zama ko ina yayi haske dakin babu hayaniya daga kujeru sai carpet da littafan addini da suke a tsare jere gwanin burge wa.
Gaisawa suka yi cike da girmama juna.Har yana tambayar Abba Ina Sir da yake abokin su Sir ne da Dada sun yi gwagwarmaya tare anan.Malan Sunan sa shine Hambali.Ana kiran sa malam ne gaba É—aya yanzu saboda ya zamowar sa Babban Malamin Addini shi ya sa da wuya kaji wani ya ambaci sunan sa sai dai malan É—in.
Gaisuwar su Leena ce ta maido da hankalin sa kan su.Zuba musu idanu yayi kamar yana karantar wani abu akan su kafin ya saki É—an murmushi yana amsa musu Gaisuwar cike da sakin fuska.
Yana cewa " Yan biyu an girma " Yayi zancen yana sakin É—an murmushi.Baki Reena ta washe cike da jin daÉ—i tana gyaÉ—a masa kai.
Ita kuwa cike da jin haushi ta sakar wa Leena harara bayan sun haÉ—a ido ganin ta É—aga masa kai.
Abba ne ya fara magana yana cewa " Dama Malam ya ran nan ne abun yake damuna shine nake son ka ƙara dubamin su idan ta dace ko raƙiya a musu a gani,Ni lamarin su tsoro yake bani,babu mai son ɗan uwan sa ya shiga inuwar sa,chan baya mun zo kace babu komai Malam dan Allah ina son a kara duba mana yanzu ko akwai iska a kan dayan su ".
Abbu ya haÉ—iye wani abu mai É—aci yana ajiye ayar zancen wanda ke nuna maka yadda abun yake damun sa.
Kai Malam ya gyaɗa dan an taɓa kawo masa su chan baya kuma ya duba su kuma tun a wancan lokacin ya ga abun da suke tare da shi sai dai bai sanar ma da kowa ba ya ce babu komai a tare da su. Wanda bamu san dalilin sa nayin hakan ba.Zuba musu ido ya sake yi musamman Leena kafin ya saki guntun murmushi ganin tana ɗauke idanun ta akan sa bayan sun haɗa ido.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kalli Abba dake jiran jin yace akwai iska akan Leena ɗin dan ayi mata ruƙiyar.
Sai dai jin ya ce " Babu komai kawai ƙuruciyar su ce haka,kar ka damu da sannu zasu daina in Allah ya yarda ".
Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yana fatan hakan ya tabbata tun da wanchan karon ma haka Malam yace masa dan ko wancan lokacin shi ya kawo su da kan sa.
Har malam ya ce masa idan ta sake faruwa ya kawo su nan a gani ko akwai ɗin dan yan zu babu alamar komai a tare da su lafiyar su ƙalau.
A yanzu ma Malam ne ya katse masa tunani da tausayin ya yan na sa da ya ke so fiye da shi kan sa a cikin duniyar nan.Yana cewa " Idan abun yayi ƙamari ka ƙara kawo su sai a basu magani na miyagu,kar ka kai su wani wajen a wahalar da su kaji,Saleh zasu daina in Sha ALLAH ".
A jiyar zuciya Abba ya sauke dan haka aka yi a wancan karon kafin ya ƙara tsintar Muryan malam da yake magana da ita anatse cikin natsuwa da kamala ya furta
Yanzu zan basu ruwan Addua, kowaccen su ta sha sai ta shafa ".
Wata ƙatuwar Jarkan zam zam ya jawo daga gefen sa sannan ya bude ya tsiyaya a wani ɗan ƙaramin cup sai da ya cika sa tab sannan ya rufe Jarkan yana mayar da ita inda take.
Ya daɗe yana tofa ma ruwan Adduo,i kafin ya ɗago kan sa ya ɗauki ruwan ya raba biyu inda ya zuba a wani cup irin wannan Sannan ya miƙa ma kowaccen su cike da murmushi yana cewa suyi Bismillah su sha.Amsa suka yi sai dai kafin su amsa sai da Leena ta zuba ma ruwan idanu kamar ta ce bazaa ta sha ba sai kuma ta karɓa jikin ta na yin sanyi ƙalau Bismillah tayi ta kafa kai bata tsaya ba sai da ta shanye komai sannan ta sauke cup ɗin tana yatsinar kyakkyawar fuskar ta mai cike da ƙuruciya.
Malam ma Numfashi ya sauke da ajiyar zuciya kafin ya ɗan matsa kusa da su ya fara tofa musu Addu,oi sai da ya daɗe yana yin su sannan ya shafa ma Reena akai ita kuwa Leena A ƙafafu.Hakan da yayi sai ya bawa Abba mamaki amma sai dai ya kasa tambayar sa dalilin yin hakan.su kan su su Leena sun ga abun da yayi sai dai basu kawo komai ba saboda ƙuruciyar su basu ɗauka akwai dalili ba.
Godiya Abba yayi wa malam kafin ya sauke masa manyan kuÉ—aÉ—e yace a yi sadaka.
Duk yadda malam ya nuna ya bar su haka Abba ya tule masa su yana Murmushi tare da ƙara yin godiya.
Har gate ya raka su tare da yiwa Abba kyautar zuma mai kyau wadda sai da ya shiga Mota sannan ya bawa driver saboda ya san halin sa ba lallai ya karɓa ba."Ka gaishe mini da Sada da Usman".Malam ya furta yana ɗaga musu hannu ta glashin motar.
Hannu suma suka ɗaga masa kafin driver ya tada motar suka bar bakin ƙofar gidan.
Numfashi Malam ya sauke da ajiyar zuciya kafin ya furta wa kan sa a hankali murya a karye cike da tausayin Saleh da Su Leena " Ba yanzu ne lokacin da zaka ka san komai ba,Saleh bana jin zuciyar ka na iya ɗaukar wannan ƙaddarar a karo na biyu,a sannu komai zai warware kan sa,tabbas ya' yan ka suna cikin matsala Babba amma faɗar matsala ce a cikin rayuwa ta, ka gafar ce ni Saleh,amma muna ta ya ka yaƙi muna kai wa Allah duk dare,komai zai zama tarihi za,a wayi gari mai aikata wannan aika aikar ya bayyana da kan sa,kafin mu"
Ya kai ƙarashen zancen yana sauke ajiyar zuciya yana komawa cikin gida jin kan sa na sarawa dan ya ji fitar ma ta fita ransa.Abubuwa da dama na dawo masa a kai har bai son yana tunawa saboda yadda zuciyar sa take tsinkewa da rayuwar duniyar.
Abba kuwa umurni.ya bawa Driven na sa ya kai su Wani haÉ—adden mall Inda ya zuba musu Leena siyayya kamar bai san darajar kuÉ—i ba saboda adalci haka ya siya wa su
Hamrah harda Ninah da ba yar sa ta cikin sa ba.Siyyaya su kayi mai Shegen yawa kafin ya biya kuÉ—in aka saka musu kayan a mota.Sannan suka yi gida kowaccen su tana ta faman sakin murmushi dan kwana biyu ba su je ba dama yaya Bilal ne yake kai su sai Abba wata rana amma ya kan daÉ—e.Cike da farin ciki suka yiwa Abba godiya Saboda koyar war Ummah ce wannan.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke yana zuba ma Reena idanun sa wadda ta ke ta faman shan ice cream ɗin ta hankali kwance bai san dalilin da ya sa yake jin ƙirjin sa na faɗuwa ba idan ya tuna yadda malam ya shafa ma ƙafafun ta Addu'a sai ya rasa samun natsuwa sai dai bai jin zai iya maganar da kowa saboda haka kawai yake jin akwai wani ɓoyayyen lamari da yake a jiye a duhu da Allah kaɗai ya bar wa kan sa sani,ba zai zargi malam ba amma zuciyar sa sai kai kawo take yi akan maganganun malan.
Kallon sa ya mayar kan Leena itama dai anatse take shan ice cream É—in ta tana sakin murmushi.Murmushin ya samu kan sa da yi yana jingina kan sa da seat.
Tare da rufe idanun sa wani shuÉ—aÉ—É—en lokaci na dawo masa a kai samun kan sa yayi da sakin murmushi a karo na biyu kan sa ya girgiza sannan ya buÉ—e idanun sa ya shafa kan Reena.
Dai dai sun kawo gida inda aka wangale musu ƙaton gate ɗin.
Shigowa motar tayi bata tsaya a ko ina ba sai bakin sashen Hajiya Asma'u.
Kayan Hamrah da na Ninah suka fito da su inda suka shige ciki.Ba tare da sun jira Abba ba.
Hamrah dake falon tana kallo ne tare da mahaifiyar ta ta daka tsalle tana murna ta karɓe kayan.Tana tambayar waya siyo muna.
Reena ce ta bata amsa baki washe tana faÉ—in " Abba ne ".
Hajiya Asma'u dake zaune ce ta ɓata fuskar ta tana haɗiye wani irin ƙololon baƙin ciki kafin ta saki fuskar ta ganin Abba ɗin ya shigo.
Gayar da ita su Reena suka yi cike da bata girma,sai dai ita Leena gaisuwar bata ma yi niyyar yin ta ba.Haka kawai jinin ta bai haÉ—u da na Momy ba.
Zama Abba yayi yana sauke numfashi kafin ya amsa gaisuwar da Momy ke masa wadda kowa ya san itace mace ta farko a gidan na sa sai.Ita ce uwar gida.Sai dai ya É—aya gare ta.
" Abban su daga ina haka,sai ga yara sun shigo da kaya Masha ALLAH "?
Murmushi Abba ya É—an saki kafin ya furta.
" Sun raka ni,na gano malam shine sai na biya da su aka yo siyayyar nan ".
Wani irin raɗaɗi zuciyar Momy ta ƙara yi jin yana faɗin rakiya dan son kai ai ya san yar ta Na nan mai ya sa bai je da ita ba ta yo siyayyar da kan ta sai yan son sa,zata yi maganin sa da shi har uwar su take ayyana wa a ranta.Inda maganar Abba ta katse mata shirun na ta yana cewa " Kuje ku kaiwa Ninah nata ku dawo ko ".Kai suka jinjina masa kafin suka miƙe cike da murna suka fice har Hamrah tare da kayan Ninah ɗin a hannun su.