Sashe 5
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar ba zata yi magana ba ta buɗe bakin ta cikin rashin tsoro ta ce " Dukkanin abokan sa munafukai ne wallahi mai gari shine bai da gaskiya,Sun dai rufe zancen da ƙaryar su,maƙaryatan banza ko kunya baku ji gashi malam Habu yace wuta ake saka mai ƙarya da badan bawa bai isa ya yanke wa bawa hukunci ba da dan an muna karatun da tuni nace yan wuta kuke dukkanin ku Tarin dolaye kawai,Bari kaji mai Gari wallahi a tambayi su Amina a ji Haka kawai suka yi cikin mu muna wasa suka kama faɗawa jikin mu,Ni kuma gashi Inna ni ta ce kar na bar kowa ya taɓa ni,sannan malam Habu ma ya muna karatun shine na cije sa kuma ni ban ma san cewa Iron ka bane da sai dai na gudu ba zan taɓa maka shi ba ".Tana kai ayar zancen tayi shiru.Inda Fadar mai gari tayi wata irin hargitsewa lokaci ɗaya Abokan Iro kamar zasu cire bakunan su wasu na zagin Shatou wasu na tsinema ta,wasu na ƙarya ta abun da ta faɗa duk sun cika wajen da Surutun su,inda da ƙyar aka samu suka lafa dan har wasu suna son kai hannu kan Shatou sai da Baffa na yayi da ƙyar da sun taɓa yar gaban goshi.Maganganun Shatou sun yi tsauri gare su take wani Haushin ta ya da muguwar tsanar ta suka fara kutsa su ji suke kamar su kashe ta take gurin.
Baffa na da hankali ya kwanta ya ce " Allah ya ƙara ma lafiya mai gari ni na san cewa SHATOU ba zata taɓa yin ƙarya ba a bincika a tabbatar".
ÆŠan jim mai gari yayi badan komai ba sai dan yadda zantukan SHATU suka shige sa dan yayi mamakin yadda ta iya zaro irin wannan kalamai kamar ana tsara mata.
Sai da ya gama ƙare ma Iro da sauran abokan sa kallo sannan ya dawo da kallon sa ga su Amina da suke tsaye cirko cirko.
" Gaskiya ne abun da Shatou ta faÉ—a "?
Mai gari yayi furucin yana kallon su Amina, Ramatu,Jawariyya Manyan ƙawayen na Shatou.Kame kame suka fara gaba ɗaya kowaccen su na son faɗin gaskiya sai dai tsoro ya cika musu zukata ganin yadda iro yake bin su da wani irin kallo da Zaidu ga kuma sauran abokan na sa da suke jifar su da mugun kallon nan na idan kuka faɗi gaskiya zaku gane kuren ku.
Amina ce da tafi su Tsoro ta buɗe bakin ta da ƙyar bayan kashe din da Iro yayi mata yanzu ido cikin ido ta furta " A'a ba haka bane,Suma sun shiga ayi wasan da su ne wai ".takai ƙarshen zancen jikin ta na rawa Muryan ta ma na rawa kamar mazari.
Wani irin mugun kallo SHATOU ta jefa mata kafin cikin ta kaici ta ce " Wallahi ƙarya ya faɗa,Wallahi tsoron su take ji,ki rantse idan ba jikin ki suka je taɓawa ba " Ta kai ƙarshen zancen cikin takaici wasu irin hawaye suna zubo mata na raɗaɗi da baƙin cikin amsar da Amina ta bada dan ta ji zafin amsar tata fiye da abun da su Iro suka mata dan ita kam ta rage zafin abun da iro ya mata dan ta bar masa dafin da bazai ƙara gigin kai hannun sa kan ta ba.
Kuka take yi wiwi Saboda yadda ranta ya ɓa ci musamman dasu Ramatu suka ƙara tabbatar da zancen na Amina haka ma sauran abokan wasan na su.
Baffa na ne yake Rarrashin ta da bata baki inda da ƙyar ya samu ta yi shiru.
" To ka dai ji kai da kake nuna ka yarda da yar ka ɗari bisa yaran yanzu ai ba abun yarda bane,suna da wayon da kai kan ka zasu iya sayar da kai inba kayi hankali ba,yanzu dai SHATOU ƙarya kika yiwa Iro ni dama na san ba za su iya aikata wannan aiki ba ƙazafi ne kawai ".
Shiru Baffa na yayi ran shi yayi matuƙar ɓaci amma da yake mutun ne mai haƙuri matuƙa sai yayi ƙoƙarin shanye ɓacin ran sa.
SHATOU kuwa samun hawayen ta tayi sun ƙafe ƙaff kafin cikin wani irin kakkausar murya ta furta " Mai gari nice mai ƙarya ko,wallahi bana ƙarya,a tambayi Baffa na amma tunda kace shi ne mai gaskiya naji na yarda, amma ku sani wallahi kune maƙarya ta gaba ɗaya wannan shari'ar ta ƙarya ce,kuma wallahi sai Allah ya saka mini badai kunce ƙazafi na masa ba,wallahi sai haƙƙi na ya fita nan kusa,Ku kuma su Amina daga yau babu ni babu ku kowa ya tsaya kan sa ni ba mutuniyar banza bace maƙarya ciya.Zan bashi haƙuri kamar yadda aka ce ".Sannan ta kalli Iro tace Kayi haƙuri Muryan ta a sanyaye cikin wani irin baƙin cikin da ya mamaye mata zuciyar ta.
" Baffa tashi muje ".Tayi furucin bayan ta miƙe tana jan hannun rigar ta da ya saɓule kaɗan saboda rashin jikin ta gashi kwana biyu tayi yar rashin lafiya ta faɗa.
Ƙaramin kallabin ta, da ta cire yanzu ta sanya a kan fuskar ta goge hawayen baƙin cikin da ya silalo mata a ɓoye.
Baffa na bai iya cewa komai ba ya miƙe ya riƙe hannun yar sa suka bar fadar bata re da jiran jin wata magana daga bakin mai gari ba.
Mai gari haka kawai ya samu kan sa da zuba ma yarinyar ido wadda yake mugun jin Tausayin ta saboda yanayin da rayuwar ta take ,sai dai ya san bata jin magana kuma shi akan iro zai iya ɓatawa da kowa ma dan haka Tausayin ta yake yin ƙasa ya kasa aiwatar da ƙwaƙƙwaran bincike,ya rasa mai yasa suke yawan samun matsala da Iro duk da shima ya ja masa kunne akan ta.
Kalaman ta ne suka sanya jikin sa yin mugun sanyi sannan da kalmar haƙuri da ta bawa Iron da babu wanda yayi tsammani acikin su sun zata sai sun kwana wajen ko shi mahaifin ta bai yi zaton haka ba saboda yasan kafuwar ta akan gaskiyar ta,ya so ya ƙara cewa wani abu amma saboda ganin yadda ta nuna tana son barin wajen ya sa ya amince idan shine farin cikin ta.
A ɓangaren SHATOU kuwa bata nuna komai akan fuskar ta ba sai dai akwai ɓacin ran da take ɓoyewa wanda shi mahaifin ta ya hango sa.
Haƙuri ya yi ta bata da rarrashin ta har suka iso gida.
A ƙofar gidan suka tarar da Bibu wanda aka yi komai gaban sa yana ganin sun ta so ya bi hanya mafi sauri ya ya riga su zuwa gida ranshi jagule amma ya san tunda tayi Allah ya isa lallai Allah zai isar mata haka ma kuma ba lallai haƙurin da ta bada ya tabbata ba har zucin ta ba akwai dalilin ta.
" Adda SHATOU kundawo,Baffa na adda ta aka bawa gaskiyar ta koh "?
Yayi furucin yana riƙo hannun ta.
Hararar wasa Baffa na ya sakar masa yana cewa " Bayan ka gama laɓen ka ai na ganka Malam Habibu,hanyar ma daka biyo na san ta ".
Yakai ƙarshen zancen yana murmushi tare da shafa kan sa.
Shiko Bibu yar dariya yayi irin ta yara cikin yar kunyar ganin sa da Baffa na yayi ya ce " Allah Baffa na ka ganni " Yayi zancen cikin yar dariya.
Dariya Baffa na yayi yana gyaÉ—a masa kai.
Ita kan ta SHATOU sai da ta É—an murmusa dama ta san sai ya je gurin koda Inni ni ta hana sa.
" Dama na san dole zaka je Sarkin wayau "
Baffa na ya ƙara faɗa yana dariya.
Dariya Bibu yayi sannan yace " Wallahi Allah Baffa na sai Allah ya isar wa Adda SHATOU an cuce ta ga gaskiya ƙarara amma sun danne haka ranar aka yi wanchan case ɗin,Wallahi bamu yafe ba tunda suka saka Adda ta zubar da hawaye gaban su,mugaye ".Ya kai ƙarshen zancen yana sharar hawaye masu zafi na jin Haushin abinda aka yiwa yar uwar sa.
" Kuyi Haƙuri kunji kuma SHATOU A riƙa tausasa harshe kinji gaban manya wata rana mai gari zai iya saka a zane ki ba zai dubi ƙarancin ki ba ".Cewar Baffa na.
Baki ta turo gaba tana cewa " Allah ni ba ƙarama bace Baffa na Sai dai Bibu dan yafi Ni tsawo ne ma yake jin shi kamar Babba " .
SHATOU tayi zancen tana tura bakin ta gaba irin na sakuwa.Dan in tana cikin su ji take kamar yau ta zo duniya.
Dariya Bibu yayi yace " Baffa na ai in tsawon Banza ne wani yayi mugani Adda SHATOU guntuwa yar ƙarama,kuma ma ai Baffa na tace ma Inna ni bata son ta girma haka take son zama yar ƙarama kamar yar gidan mai gari saratu" Ya na kai ƙarshen zancen yayi cikin gida da gudu yana dariya cikin farin cikin yadda SHATOU ta saki fuskar ta.
Yadda ta zaro ido waje ne ya san ya tsokano rigima hakan ya sa ya gudu ciki yana dariya.Saboda bata son ya na ko kaman ta ta da saratu yar tsohon mai gari wadda take Wada domin haka halittar ta take.
Baffa ma dariya yayi ganin yadda ta bishi a guje tana cewa " Wallahi Allah ya raba Ni da zama saratu Wada miyan ka ya tsallaka rafin maliya ya wanke tass "..
Ciki Baffa ya shige shima yana sayo gidan na su bakin shi washe kamar ba yanzu dukkanin su suke cikin zafi ba amma gashi har Bibu ya sa sun manta musamman Shatou koda yaushe yana ƙara ƙaunar soyayyar dake tsakanin junan su,yana Roƙon Allah ya shirya masa su ya daɗa haɗa masa kan su.