Sashe 65
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Daga yau ma kaine wa na karɓe daga gare ta,idan tayi laifi ka zane ta a matsayin ka na babba ".
Tunda Inna ni ta fara zancen yake wasar baki yana dariya.
Ita ma Inna ni dariyar take yi ƙasa ƙasa ganin yadda hakimar ta haɗe rai kamar an mata mutuwa ga hawaye sun wanke fuskar ta ta a wannan karon Dagaske.
Tsalle Bibu ya daka yana murnar sa ita ko shatou kamar ance mata Inna ni ce ta mutu ko Baffa na ko shi Bibu da su Amina ta cigaba da sakin kukan ta mai ƙara.
" Amma dai anyi ƙatuwar banza SHATOU "
Inna ni ta ƙara furta wa.
Matsawa ta yi kusa da SHATOU É—in tana dariya sai kuma ta juya ta shiga madafar su sai gata ta fito da maburkaki a hannun ta, fuskar ta haÉ—e dan ta lura lamarin na Shatou sai a hankali.
Aiko Shatou na hango ta,ta miƙe tana shigewa ɗakin ta tana waigen Inna ni.
Dariya Bibu yayi kamar zai kai ƙasa kafin ya yi alwallah ya fice masallaci yayi Sallah.
Inna ni ma kan ta,ta girgiza tana sakin guntun murmushi tana furtawa a ranta kura ga tsoro ga ban tsoro.
A ɓangaren Baffa na kuwa koda ya isa fadar mai gari gaisawa kawai yayi da mai gari da sauran jama'ar fadar yayi gaba,Mai gari da ya fahimci dalilin zuwan sa ya wuce ɗin bai ce masa komai ba sai sakin murmushi da ya ɗan yi ta gefen baki kulawar Baffa na ga yar sa na burge sa.
A ɓangaren shatou kuwa tunda ta shige ɗakin ta,ta ke sauke ajiyar zuciya kafin ta tura baki gefe ta miƙe tuna bata yi Sallah ba.Koda ta fito tsakar gidan babu kowa dan haka tayi alwallah ta wuce ɗaki tayi sallah anan bacci ya kwashe ta bata farka ba sai gab da magriba.Cike da mafarkaii haka ta tashi tana zarar idanu addu'oi tayi tayi a zuciyar ta kafin ta samu su fito fili har ta buɗe idanun ta tar akan Inna ni dake kan ta wadda itace ta tada ita daga baccin na ta ganin shiru har su Baffa na sun yi masallaci bata fito ba shine ta zo duba lafiya ta same ta tana bacci dan ta yi zaton ma a ɗazu ta fice gidan su Amina ko Jawairiyya sai Bibu yace mata ai tana nan ya dubo ta lokacin da Baffa na yake zancen ina take kafin ya sake ficewa,dan haka ta fita iskan ta dan ta san ƙila wani abun ya ɗauke mata hankali kamar aikin aji da sauran su dan baya ma yi zaton bacci take yi ba.
Inna ni zuba mata idanu tayi ganin tana zare ido alamar har yanzu tsoron abinda ta gani a mafarkin bai sake ta ba dan ta fahimci mafarki tayi dan haka tayi ta tofa mata addu'a, itama da ta fahimci ta farka daga mugun mafarkin ta fara addu'oi Inna ni na taya ta a hankali kuwa ta fara sauke dogon numfashi tana ya mutsar fuska cike da son tuna yanayin mafarkin na ta sai dai duk yadda take son tunawa ta kasa dan haka ta kalli Inna ni da idanun ta da ke cike da hawaye da suka taru lokaci É—aya dan zata iya tuna mafarkin ba mai kyau bane duk abun da ta gani a cikin sa akwai tashin hankali a cikin sa mai girma.
" Mafarkin me kika yi haka Shatou " ???
Inna ni ta faɗa tana zuba ma yar Tata idanu cike da wani irin rauni da ya dabaibaiye ta ganin hawayen yar ta wanda suke tabbatar da cewa har zuci lamarin babba ne na abunda zai karya mata zuciya haka a game da mafarki wanda kuma kowa ya san kaso goma kashi uku duka ƙarya ne mafarki.
Kuka ta ta fashe ma Inna ni dashi rarrashin ta Inna ni ta dinga yi kafin ta samu ta lafa ta yi shiru.
Cike da wani irin É—an tsoro tace " Mafarkin na kasa tunawa fa shine nake ta son na tuna amma na kasa Inna ni kuma fa abun da na gani ba mai kyau bane,Harda kuka nayi a mafarkin "
Sai kuma ta fashe da kuka
" Ya isa barshi kawai kinji duk ranar da kika tuna sai ki sanar mini yanzu dai ki dage da addu'a ƙila da zaki kwanta baki yi addu'a bane ba ko ? "
Kai shatou ta gyaÉ—a mata.
Ɗan murmushi Inna ni ta ƙaƙalo kafin tace " Yawwa yanzu anyi Sallah tashi kinji ".
Miƙe tayi da taimakon Inna ni suka fice daga ɗakin.
Ruwan Alwallah ta zuba mata sannan ta miƙa mata ita kuma ta shige nata ɗaki kafin ta fito da littafin azkar ɗin ta dan kwana biyu ba su zauna zaman karatun azkar ɗin ba.
Tabar mar dake shinfiÉ—e ta gyara mata abun Sallah kafin ita ma ta kabbara Tata Sallahn akan abun Sallahn da ta shimfiÉ—a ma kan ta,hijabi shatou ta É—auko É—akin ta itama mai É—an girma ta tada Sallah a natse , abun mamaki yau Inna ni ta riga Shatou gama sallah.
Inna ni dai ikon Allah take ta kallo da wani shakku akan yanayin shatou da mamakin wannan wane irin mafarki ne ya lallasa jikin Shatou haka komai babu kuzari take yin sa.
Tun Inna ni na mamaki ta daina dan shatou bata gama Sallahn ba sai da a ka kusa kiran Sallahn Isha shima tana gama magriba É—in ta hau yin Ba,adil magrib.Inna ni dai ga mamaki ga kuma wani irin karye wa da zuciyar ta ke yi na yanayin yar ta É—in.
Ƙarshe sai dai ta girgiza kai tana sakin murmushi tana tuna wani lokaci da ya shuɗe lokacin da tana amarya ta dinga rafka sallah tana amarya bayan ango ya tafi Rakiyar abokai har ya dawo ya same ta haka,sai yanayin ya dawo mata da komai sabo ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi zuciyar ta na fara wani irin rawa kamar ana daka sakwara ga wani irin ɗaci da ya maƙare zuciyar ta da ruhi wani duhu da ta fara gani na damuwa ne da baƙin ciki hakan ya sa ta fara ambaton sunan Allah da neman agaji take kuwa ya kawo mata ɗauki ya hana yanayin da zuciyar ta ke neman shiga yin tasiri a gare ta.
Bayan ta samu natsuwa ne ta juyar da kallon ta kan Shatou da tayi zugum tana kallon ta ganin yadda take ta rintse ido tana dafe ƙirji.
Murmushi ta ƙaƙalo dan bata son ta fahimci komai bare ta dame ta da tambaya har Baffa na ya fahimci wani abu.
Aiko tambayar da ta guda itace ta ratsa dodon kunnen ta.
" Inna ni me kike dafewa ƙirji da rufe ido ko bakya da lafiya "?
Murmushi ta ƙara saki ganin shatou na gama furucin ta ƙara zuba mata manyan idanun ta alamar amsa take jira dan haka ta ce " Babu komai shatou gajiya ce kawai "
" Irin yadda naji ranar ne kika ji ko Inna ni ai nima haka na dafe ƙirji na har kika ce mini sakarci ne kawai "
Murmushin inna ni ta saki kafin ta ce " Eh fa shine ai na fahimce ki fa,ranar gajiya ce ta saka ki jin haka,Nima itace dan haka yau da wuri ma zan kwanta ".
Kai shatou ta jinjina cike da gamsuwa kafin ta cigaba da addu,oin ta ita kuwa Inna ni É—an murmusa wa tayi kafin ta sauke ajiyar zuciya.
Dan bata san mai zata ce mata ba dan ko ita ta ta faduwar Æ™irjin a wancan ranar abun ya tsaya mata a rai ta san tabbas babban abu ne zai kawo wa yarinya Æ™arama irin wannan matsalar sai kuma idan an haifi ya ro da hawan jini ko ya samu tsoro mai girma.To bare ita da ta san ainahin ta ta damuwar,da ta kasu kashi kashi wanda ta san hankalin shatou ba zai taÉ“a iya É—auka ba,ba yanzu ya kamata ta fuskanci komai ba.Ƙaddarar ta wani babi ne da take ganin shafin sa É—aya bayan É—ayan akan yar ta kuma Garkuwar ta,da Æ™addarar su take tafiya a tare da rayuwar su.Numfashi ta Æ™ara sauke wa tare da su jan ajiyar zuciya wanda har sai da Shatou ta waiwayo sai dai bata ce mata komai ba ta cigaba da yin addu'a tana jerawa su Inna ni Addu'oi tun rana yi a zuci har ta fito fili hakan shi ya sanya ya zuciyar Inna ni yin sanyi tare da sakin murmushi tana karÉ“awa da Amin.âœï¸
Ku GAFARCE Ni hiliss mutane kirki na san na muku laifi wallahi na shiga.Busy kwana biyu dan haka typing ya gagare ni.🙠Jama'ar facebook ma da muka wuce sosai gashi a jiye basu samu update ba ayi haÆ™uri âœï¸
Wannan labari na kuÉ—i ne akan Naira#800
# _FA'EEH BG CEâœï¸_
Book one free
Book two paid N#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haÉ—a document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga AlÆ™alaminâœï¸
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Like,react,share,and Comment,Vote PLS ðŸ™ðŸ¥ºðŸ’”
https://chat.whatsapp.com/H5xKfOMK5QE2YtMirvcsat?mode=r_t
_*KURMAN ƘADDARA*_
_©®Faiza Almustapha Murai_
_FA'EEH BGâœï¸_
P________3ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
*BOOK ONE*
_FREE._
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*
ADVERTISING! ADVERISING!💃💃💃
KHADSEEN'S COLLECTION
GIDAN KAYAN ADO 👜👛ðŸ‘👡👠⌚👗ðŸ›ï¸
BABBAR YAR KASUWAR NAN TA KU TA MATA MAI SUNA KHADSEEN'S COLLECTION TA ƘARA KAWO MUKU HAJAR TA MAI KYAWON KALLO DOMIN KO BAKA SAYA BA ZAKA GAMSU DAGA KALLON SU.💃💃💃
TANA DA DUK WANI NAU' I NA KAYAN ƘAWA NA KWALLIYAR MATA DA MAZA,MASU KYAU KAMA DAGA TOTE BAGS,COMFY BAGS,DUBAI MATERIALS,LUXURY BAGS,LUXURY ABAYAS.FLAT SHOES.Da sauran su.
WANI ABU SAI A KHADSEEN'S COLLECTION💃💃💃💃💃💃WO HOHO HAJIYA TA, KE DAI GARZAYA KI CIKA KAPACITYN 💃 KI A KHADSEEN'S COLLECTION Wa.me//. 8149484562
ZA,A IYA TUN TUÆAR TA TA WANNAN LAMBA DAKE SAMA👆
SAI KUMA LINK NA GROUP NA TA A SAMA 👆A CHAN ZAKU GA KAYAN KECE RAINI,KUDAI💃💃 KU GAR ZAYA KU CIKA KAPACITYN KU MANYAN MATA MASU ADO👜👛👠KHADSEEN'S COLLECTION NA AIKAWA DA KAYAN TA A KOWACE NAHIYAR DUNIYA CIKIN GAMSAR DA ABOKAN KASUWAN CI TA.ðŸ›ï¸ðŸ›ï¸ðŸ›ï¸ https://chat.whatsapp.com/H5xKfOMK5QE2YtMirvcsat?mode=r_t
_________________