← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 110

Sashe 109

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

" Ahaf ai sai kiyi ".

Ɓata kyakkyawar fuskar ta ta ƙara yi kafin ta dawo cike da yar shagwaɓa ta kama hanyar dinning da komai yake kai.
Mamma Murmushi tayi kafin ta ce " Wa kunbo wa kayan ta ".
ÆŠan guntun murmushi Aleeshat tayi kafin ta zauna ta haÉ—a ma kan ta shayi mai zafi shi kaÉ—ai ta saka ma cikin ta inda tayi ta sipping É—in sa a hankali tana duba tsadadden a gogon hannun ta.Har ta shanye sa dama kaÉ—an ta haÉ—a dai dai cikin ta.
Tana gama wa ta miƙe bayan ta ɗan goge bakin ta da tissue sannan ta ce a hankali " Mamma na tafi sai na dawo ".
Ta kama hanya tana Amsawa da Amin jin addu'ar da Mamma take yi mata.
Mamma da ido ta bita cike da tausayin ta domin kuwa ta san yanzu sai sun gan ta sai kuma idan lokacin tashi school na su Asad yayi idan ta dawo ta kan ƙara fita sauƙin ta ma yanzu saboda ya fara wayau ta rage fitar,da sun yi ƙokarin hana ta fita koda yaushe abu ya gagara har sun zuba ma sarautar Allah ido domin kuwaa duk lokacin da suka so hana ta fita musamman ta dare ita da su wani yanayi suke shiga domin haka take koma musu kamar zata haukace musu da magiya tace ita kaɗai ta san abinda take ji a jikin ta a duk lokacin da suka yi yunƙurin hana ta fita.Sauƙin ta ma yanzu ta rage sosai.
Numfashi Mamma ta sauke kafin ta kama hanyar da zata sada ta da É—akin ta.
A ɓangaren Aleeshat kuwa cike da takon ta na rausaya kamar tarwaɗa haka ta isa kusa da motar ta,wata ce daban ta buɗe ta shiga yanzu kamar irin BMW ɗin na Black mai kyau.
Wuta ta bawa motar bayan ta kunna ta inda aka wangale mata gate É—in ta fice.
A Guje kamar zata tashi sama dan dama ta saba da gudun ta ba Damuwar ta ba ce duk inda zata shiga cikin Abuja a high speed take gudun ta,sai ko idan Asad na aciki ne ta ke yin gudu kaÉ—an.
Ba ta haura mintuna arba'in ba sai gata a iconic University Abuja branch parking ɗin motar ta dai dai ta, ta fito.Koda ta fito idanu ne kan ta kamar ƙasa dama kuma sun san wacece domin ita kaɗai ce Dalibar da ke yin parking na motar ta a parking space na staff ba tare da an mata komai ba.Ita ce kawai mai wannan capacity ɗin.
Kawar da kan ta tayi daga kallon sa dan da shi ta fara haÉ—a ido kasancewar bakin department na su ne tayi parking.
Ba tare da ta ce masa ƙala ba ta rufe motar tare da locking ɗin ta sannan ta cigaba da tafiyar ta inda ta san zasu haɗu zai iya yuyuwa chan ne inda team ɗin suke dan ba ta jin zata masa wata magana daga inda yake ko ta isa wajen sa.
Shiko Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗan shafa kan sa dan ya shagala da kallon ta dan koda yaushe kyawun ta ƙaruwa yake a idanun sa ba ma shi kaɗai ba kowa ya san Leesha yar gayu ce ƙwarai ga kyau da zubin halitta da Allah yayi mata,a awasu lokuttan yakan ji kishi mai yawa ya rufe masa idanu sai dai bashi da yadda zai yi ne,domin wata shigar da take yi shikan sa fitina ce a gare sa bare wanin sa.
Gashi manyan Alhazzawa ne ke bibiyar ta da sunan soyayya masu dukiya tana wulaƙan ta su bare shi da yake ɗan talakan sa duk da suna da kuɗi gwargwado amma bai kai na wayen da take kulawa ba.Abin na ƙona masa rai matuƙa baya da yadda zai yi ne da tuni ya furta mata kalmar da sauran mazan suke furta mata da suke shan wulaƙanci asalin sa.Bayan ta ya bi yana ƙarewa halittar ta kallo yadda hips ɗin ta ke juyawa cikin rigar.Numfashi ya sauke kafin ya janye idanun sa a kan ta,da suke dauke da wani mugun kishi.
Aleeshat kuwa bata damu da duk kallon da ake mata ba daga student har teachers haka take ratsa mutane tana baɗe su da ƙamshin ta.
Bakin Audit É—in su ta dakata dan ya zo ya nuna mata inda suke kai tsaye ba tare da ta wahala ba.
Bata daÉ—e da tsayuwa ba sai gashi ya iso Murmushi ya saki kafin ya ce '' Ran ki ya daÉ—e Barka da isowa ".
ÆŠan kallon sa tayi jin wani sabon kilin bibin da ya zo mata dashi na kiran ta da ranki ya daÉ—e.
ÆŠan sake fuskar ta tayi kaÉ—an ba ta nuna komai ba " yawwa Kamal " Daga haka bata sake cewa komai ba.
Sai ma janyo wayar ta da tayi tana kokarin yin kira.
" Muje " ya furta Fahimtar dama abun da take jira kenan.Bayan yayi wani murmushi na jin daɗin yadda sunan sa ke fita bakin ta cikin wani salo wanda ita ba da wata manufa tayi sa ba.Gaba yayi kafin ta bi bayan sa.Chan ƙarshe suka nufa sai dai tun da ta shigo idanun kowa ya koma kan ta musamman mazan da ke ciki suna karatu.Har da matan ma masu jin haushin ta suka fara zagi da Harare gare ta sai dai a banza babu wanda ta kalli gefen sa cikin su.
Suma sauran team ɗin idanun duk suka zuba mata sai dai tun da tayi sallama bata ƙara cewa komai ba.
Suma babu wanda ya ƙara yin magana cikin su.
Sai ɗan satar kallon ta suke yi mazan, macen dake wajen ita ɗaya,kasancewar suna ɗan gaisawa ta saki fuska suka gaisa, anan suka haɗu da Nafisa sai dai duk yadda Nafisa ta so su jone a bu ya gagara kusan yan zu shekarar su ta uku da fara karatun Law.Nafisa Hamza Indabawa itama yarinya ce yar wanka da gayu mai kirkiri ita kanta bata ɗaukar raini dan haka ya sa ma take sake mata kaɗan.Dan ta fahimci itama ba ƙyalliyar ta bace,kowaccen su nada nata aji gwargwado.
Abun da ya tara su,suka fara kafin kowa ya riƙa bada ideas na sa ita ce ƙarshe wadda ta kawo Tata idea.
Har ta gama bayanin ta a tsanake cikin ƙwarewa da basira kowannenn su idanu ya zuba mata,kafin ta dasa aya tayi shiru,kuma take suka karɓa dan kan ta na mugun jaaa dan tun da suka fara wannan program tana cikin wayen da ba su taɓa yin carry over ba,ba a class na su.
Daga nan suka fara haÉ—a bayanai suka haÉ—a komai Aleeshat ma tun kafin a tashi kiran Alhaji Mamman ya fito da ita wanda bata ma yi niyyar É—agawa ba amma saboda yadda wajen ya dame ta sai tayi amfani da damar kar su ga kawai ta fita bata cewa komai ba.
Aiko tana fito wa ta yanke kiran Alhaji Mamman da kan ta.Tana jan mugun ƙaramin tsaki.
Sai ga kira ya shigo wayen ta daga teacher É—in su.Asad.
Cike da sauri da wani irin mugun tashin hankali ta faÉ—a motar ta kafin ta kunna ta, ta fige a tsiyace ta bar school É—in baki É—aya bayan yanke kiran.
Idanun ta ne suka rikiɗe lokaci ɗaya damuwa ta bayyana ƙara ra akan fuskar ta sa.
Gudu ta ke tsugawa bana arziki ba dan cikin abun da bai wuce min tuna goma ba ta isa bakin gate É—in wata haÉ—aÉ—É—iyar asibiti da ta amsa sunan ta asibiti dan asibiti ce ta a manya sai dai ko talaka gwargwado zai iya kai kan sa Amma tabbas asibitin manyan mutane ce kama da ga yanayin zubin ta da Nairan da aka kashe mata.
MMG Hospital shine sunan wannan asibiti a taƙaice.
Kamar kullum sashen yara ta nufa bayan yin parking motar zuciyar ta na wani irin rawa da harbawa kamar Ance mata Asad É—in ya Mutu.
Idanun ta har dushi dushi suke gani saboda tsabar tsoro da firgici da ya shige ta da tashin hankali.
KafaÉ—an wani da ta buga ce ta sanya ta É—an dawowa hayyacin ta kafin ba tare da ta tsaya kula wanda ta buge É—in ba ta cigaba da tafiya,cikin kiÉ—ima.
Su biyu ne a tare ɗaya da kayan likitota ɗaya kuma sanye cikin kaya na alfarma mutun mai kamala da natsuwa daga nin sa dai ba ƙaramin mutun bane.
ÆŠan juyawa yayi ya Kalle ta kafin ya É—auke idanun sa kan ta.Yana furta astagfirullah a cikin zuciyar sa.
" Sorry M Ina ga tana da patient ne a ciki shi ya sa, hankalin ta na kan sa ".Ya kai ƙarshen maganar yana sakin murmushi ganin yadda Mutumin ya nuna babu komai yana sakin guntun murmushi kafin ya ce " Babu komai na ga alama kammm,Allah ya basu lafiya ".
Amin wannan likitan ya furta.
" Ammm Jibi zai shigo ko gobe,zamu yi magana in sha ALLAH idan ya amince,Ba abun damuwa bane Mahuta. ".
Godiya wannan Dr da sunan shi ke maƙale a jikin rigar sa shine Dr Sada sabo Mahuta,Amma an fi kiran sa da Doctor Mahuta.Kayan sa da suka zube suka duƙa suka kwashe tare kafin suka yi musabaha da wannan likitan sannan ya raka shi har mota suna ƙara tattaunawa kan maganar da suke yi ɗin kafin su fito yanayin su dai kamar a bokai ko mutanen da suka shaƙu da juna sai dai akwai ɗan nuna girma ga likitan zuwa ga mutumen da ya kira M.Yana barin asibitin shi kuma ya juya ya koma cikin asibiti.
Haka kawai yake jin ƙirjin shi ya buga da ya tuno da yanayin gefen fuskar ta da yayi arba da ita duk da ba sosai ya gani ba saboda saurin da take yi.
Wani tunani ne ya shigo masa akai sai dai da sauri ya furta " No impossible gaskiya ".
Haka ya cigaba da tafiya har ya isa inda zai je.
A ɓangaren Aleeshat kuwa kasancewar ta san room no.nasa dan komai Anty prise ta sanar mata a waya hakan ya sa ta tura ƙofar jikin ta na rawa.
Ko Sallama babu haka ta faÉ—a É—akin
,wannan Aunty ta su Asad mai suna Anty Prise sai ganin ta tayi tsaye kan ƙafafun ta..
Zuba ma Asad idanun ta tayi da suka sauya kamannin su sai ga wasu hawaye Sun Silalo mata musamman ganin sa haka kwance marabin sa da gawa numfashi,gashi numfashin na sa ma har yanzu bai dai dai ta ba.
Bacci yake yi kai daga nin sa kasan ya na shan baƙar wahala.
Kujerarar da ke kusa da shi É—ayar ta zauna tana haÉ—iye kukan da ke shirin ta so mata.
Tana taɓa hannun sa dake maƙale da drip.
Kan ta ta kife akan cinyar ta saboda ta kasa jurewa musamman ganin sa yayi wani sharr da shi kamar wanda baya da jini a jikin sa.ÆŠan É—agowa tayi ta duba É—akin tsitt wanda har Malamar ta tafi kasancewar dama mahaifiyar sa take jira duk da suna da clinic a school Amma na sa ciwon bana treating bane clinic dan wanccen karon clinic aka kai shi dan abun ya fara ta sar masa a makaranta gadan gadan,sai dai na yanzu ya fi worse,dan haka suka nemi asibiti mai kyau mafi kusa.Duk da lokacin da ya na É—an shekaru biyu ya yi ciwon ya fara nuna alamar sa a jikin sa.
Sai dai ba su taɓa kawo cewa abun zai zamo haka ba dan dukkanin su tsorace suke tun karɓan report na sa na farko da aka yi masa bincike a school clinic...
Numfashi ta sauke mai nauyi kafin ta ɗago kan ta ta ƙara kallon Asad da har yanzu ko motsi bai yi ba.
Wasu hawaye ne masu zafi suka ƙara biyo wa ta fuskar ta damuwa ta ƙara bayyanar ma ta da tashin hankali.
Sai alokacin ta lura Aunty prise ta wuce.Shiru ta yi cike da tunani kala kala tana kallon Asad zuciyar ta cike da wani irin zafi da ƙunci.Tana nan zaune sai ga nurse ta shigo ta sanar da ita Dr na neman Iyayen Asad Jibril.
Aiko babu musu ta fito bayan ta yi wiping tears nata da wata hanky É—in ta mai kyau fara tass.
Asad kuwa ta bar shi hannun Nurse dan dama jinyar mutun É—aya ke yin ta,idan ya kasance ku zaku yi jinyar abun ku ba nurse ba.
Cikin sanyin muryan ta tayi Sallama zuwa cikin office É—in.
ÆŠago idanun sa yayi ya zuba mata ido dan koda basu ga fuskar ta ba ya gane shigar ta.
Masha ALLAH ya furta a cikin zuciyar sa sai da ya ƙare mata kallon tsafta sannan ya ce " Bismillah ga seat ".Ya furta yana nuna mata seatt ɗin.
Aleeshat kuwa babu musu ta nemi waje ta zauna tana sauke ajiyar zuciya,haka kawai take son jin wani abu da ban bayan report na farko na Asad ɗin dan haka ta ƙagara ya sanar da ita komai ta san halin da Asad ɗin ta yake ciki.
" Ammm ke wacece a gurin Asad F Jibril ".?
Yayi mata tambayar duk da cewar ya ga yanayin kamannin su amma yana son tabbatarwa ko ƙanen ta ne ko ɗan ɗan ta dan daga yanayin shigar ta baiga alamar matar Aure bace ko kaɗan.
Ɗan jimm tayi tana wasa da zoben ta na azurfa mai kyau da ya ƙara yiwa yatsun ta kyau ta ce " Ɗa na ne " .
Daga haka bata ƙara ce masa komai ba.
Kai ya jinjina yana saka record É—in a system dake gaban sa.Sai dai mamaki ya kashe shi daga zaune,sai dai ya shanye abun sa tun da su likitota ne sun saba ganin abun mamaki wanda ya fi wannan su haÉ—iye.
Chapter 109 · 0% Book details