Sashe 49
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Fahimtar suɓutar bakin da Inna ni tayi ne ya sa ta furta " eh ina nufin Bibu da Amina ai kin ce kamar dubu suke a gare ki ".
Murmushi Shatou tayi tana gyaɗa kanta kafin ta ce " Ba zan ƙara maganar ba nikam,Bana son ƙannen ma ".
Tayi zancen da iya kar gaskiyar ta.Sai dai a lokacin ƙuruciyar ta bata damar tunanin tambayar Inna ni dalili ba.
Kallon ta Inna ni tayi tana sauke Ajiyar zuciya kafin ta saki murmushi ganin yadda SHATOU ta narke fuska.
Sallar Isha'i ce da aka kira ta sanya Shatou miƙewa dan chanza Alwallah dama Inna ni taji warin tusa dan haka da yake su biyu ne ya sa bata ce mata ƙala ba dan ta san itace.Tana zuba ido taga idan lokacin Sallah yayi ko zata miƙe tayi.Sai ko ta miƙe.
(" Mai gari É—aya,Amina,da Jawairiyya É—aya,dan ba zan ba Ramata ba ta saka musu warin baki ".)
Murmushi Inna ni tayi tuna wayen nan kalaman da suka fi bata dariya duk da ƙirjin ta na ɗagawa akan yadda kwana biyun nan Shatou take addabar ta yau zancen Aure gobe haihuwa,dudu shekarar Shatou nawa da zata fara wannan shirmen koda yake wasu yaran haka ƙuruciyar su take da jajiɓe jajiɓe idan ba shirmen Shatou ba yaushe haihuwar ta zama mara wahala da zata haifi yan goma,abu kamar wasan yaran ai bata mata fatan samun yan goma ko nan gaba ne.Shi Raino harda mai gari..Ta ƙara furtawa acikin zuciyar ta kafin ta saki yar ƙaramar dariya a bayyane dai dai lokacin da Shatou ta same ta,kallon ta tayi ta ce
" Inna ni me kike yiwa dariya halan "?
" Babu komai Shatou,Addu'a kawai nake yi Allah ya shirya min ke,Ya sa naga Auren ki,ke da yan uwan ki (...da bani tabbas akan su ") ....ta kai ƙarshen zancen cikin zuciyar ta cike da wani irin raunin da take ɓoyewa a lokutta da dama musamman a gaban Baffa na.
Sai kuma ta É—ago Afili ta cigaba da cewa.
" Amina,Ramata, Jawairiyya Habibu na ga kuma Yar gaban Goshin Baffa nan ta ".
Tana sauke zancen ta sauke ajiyar zuciya a ɓoye.
" Amin Inna ni,har da nasu Iro ma Allah ya nuna miki ".
Shatou ta furta babu kunya cike da ƙuruciya.
Inna ni kuwa cike da dariyar da ta bayyanar da wushiryar ta yar ƙarama irin irin ta shatou,cike da mamakin ƙuruciyar Shatou ta kalli yar kyakkyawar fuskar ta da take ɗan ya sharaff da alama zancen har zuci tayi sa wanda ya nuna ma Inna ni cewa shatou bata da riƙo yanzu gashi har da Abokin faɗan ta a cikin wayen da take fatan Inna ni taga Auren ta cike da murmushi ta ce.
" Yar mafarauci manya,har da iro alamarin".
Kai SHATOU ta gyaɗa kafin Inna ni ta koma sakin murmushi dan yau firar ta da yar ta ƙayatar da ita take yi matuƙa tana samun farin ciki duk da akwai shirme ciki.
" Tomh Allah ya nuna muna,ya sa muna da rai da lafiya ".
" Amin " Shatou ta ƙara furtawa tana sakin murmushi.
Ita ma Inna ni murmushin ta saki kafin ta kalli Shatou tace " ki kabbara Sallah ".
Tana gama zancen ta tayar da sallah.
Itama shatou haka ta tayar da ita cike da natsuwa kuwa ta gama sai dai duk da Inna ni ta riga ta farawa ta riga ta gamawa.
Inna ni kai kawai ta girgiza bata ce mata ƙala ba bayan gama sallahn
Tana jin ta tana Yin Addu'a wadda rabi da kwatan sa duk Inna ni ake yiwa da Baffa na.
Murmushi Inna ni ta samu kan ta da yi dai dai lokacin da ta gama jan charbin ta tace.
"Ke ma fa kina buƙatar Addu,ar nan Shatou,kiyi wa kan ki bamu kaɗai ba da Bibu ".
Fuska ta ɓata sannan ta ce " Nidai Inna ni na fi son ku na riga ku mutuwa,Dan nafi son na riƙa ganin ku kusa dani,idan bakwa nan kuma Ni na san bazan ma iya rayuwa ba ".
Shiru Inna ni tayi tana zuba mata ido ganin yadda take zancen cike da ƙuruciya da gaskiyar ta, kafin ta saki guntun murmushi cike da tausayin Yar Tata abun son ta wadda take kallo a matsayin sanyin idanun ta wadda bata son damuwa ko ɗigo ce ta gan ta atattare da ita,akwai dalilai da dama da suka saka Inna ni bawa Shatou wani waje na musamman a cikin zuciyar ta,mai cike da tausayi wanda ita kaɗai ta bar wa kan ta sani sai lillahi.Ita kan ta Abar tausayi ce sai dai Shatou take ji ma wa.
" Allah ya sa mu mutu Muna masu imani kowa ta É—auka a tsakanin mu duk É—aya ne dama lokaci kawai muke jira "
Shiru Shatou tayi bata bi maganar Inna ni ba wadda ta sauke a jiyar zuciya tana haɗiye wani irin ɗaci a ƙasan zuciyar ta mai girma da ciwo.
Shatou kuwa shiru tayi sai dai ta zuba ma Inna ni idanu tana Murmushi kafin ta ce.
" Amin "
Murmushi itama Inna ni tayi.
Sallamar su Bibu ce ta katse ma Shatou wata maganar da take son yi.Dan haka cike da murmushi ta gayar da Baffa na.
Amsawa yayi shima cike da sakin fuska da murmushi yana ƙara bin ta da kallo kamar yau ya saba ganin shatoun.
Inna ni ce da ta lura ta É—an yi gyaran murya hakan ya sa ya juya yana kallon ta kafin ya sauke a jiyar zuciya yana sakin murmushi.
Zama suka yi a kan ta barman da Inna ni ta shimfiɗa musu tun ɗazu a bincin su ta sauke musu nan kafin ta dawo ta zauna bayan ta tabbatar komai ta ajiye na buƙata dan ta san tare zasu ci abincin dan haka bata wahalar da kan ta da raba musu shi ba.
A haka suka ci abincin tare ita Inna ni bata ma ci na ta ba sai dai Baffa na bai ce mata ƙala ba.Cikin natsuwa suka ci suka ƙoshi suka wanke hannayen su kafin Baffa na ya ƙara bita musu karatukan su,kowannen su yayi bita sannan ganin dare yayi suka fara ƙoƙarin miƙewa dan lokacin tara ta buga.
Sai dai Shatou na miƙewa Ta tsinkayi Muryan yaro na Sallama wai ana yiwa SHATOU Sallama yadda ta zuba ma yaron da ake tsaye ido haka ma Inna ni, Baffa na ji yayi kamar an masa dabaibaiyi jikin shi ya sauya lokaci ɗaya ya tsinci kan sa cikin wani irin tashin hankali dan haka da ƙyar ya zaƙulo a bun da zai iya furtawa " Wa ya ke kiran ta ".?
" IRO ne É—an gidan mai gari ".
"IRO"!
Suka haɗa baki wajen faɗa cike da mamaki ita kuwa SHATOU da farko daɗi ta fara ji an fara zuwa wajen ta zance sai dai jin sunan Iro ya sa ta ɓata rai tana Hararar yaron cikin ɗan hasken fitilar da Inna ni ta kunna musu.
Inna ni kuwa samun kan ta tayi da sakin murmushi kawai kafin ta bar su nan ta shige É—akin ta dan ita sai abun ya bata dariya zillau (wai ana yiwa SHATOU Sallama,)sai lamarin ya bata kunya.
Ajiyar zuciya Baffa na ya sauke mai nauyi ganin shatou ta wuce fuuu bayan ta furta " Ka ce masa nayi Bacci,idan wani abu na masa ya bari mu haɗu fadar mai gari ".Ta kai ƙarshen zancen tana jan tsaki,irin ita Babbar budurwan nan.
Bibu dariya yake ta saki yana kallon Shatou ɗin wadda ta galla masa Harara ya san yadda take yawan faɗin za,a ga saurayin ta kyakkyawan gaske ranar da ya fara zuwa ƙofar gidan nan sai kowa ya suma saboda kyaun sa amma daga ƙarshe sai aka ɓuge da ganin Iro abokin faɗan ta dan haka yake ta sakin dariya yana tuno kalaman na ta.