← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 110

Sashe 84

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

***Yau Shatou a sake ta tashi cike da fara,a dan haka suka yi duk wasu ayyukan da suka saba yiwa Inna ni ita da Bibu kafin suka fice makaranta bayan sun yi wa Inna ni da Baffa sai sun dawo kasancewar Baffa na yau bai fita da wuri ba ya É—an tashi da ciwon kai.
Koda suka isa makaranta kowa ya san yau Shatou ta dawo ta asali ba shatoun jiya ba ce.
Dan haka kowa yake kokarin shige mata aka cigaba da yadda aka saba farin cikin Amina ya kasa ɓoyuwa dan koda ta zo makarantar a tsorace take ta yi zaton Shatou ta chanza musu sai ta tarar da aka sin haka dan haka take jin daɗi kamar ta goye shatoun kuma Shatou ta fuskan ci hakan da dukkanin su ma sai dai bata tambaye su ba ta share.
A haka aka tada su tara suka fito gida kowannen su gida yayi dan an basu dama yau É—in dan haka Shatou tana cikin masu zuwa gidan su Amina kuwa duk basu je ba dan sun san dole zasu yi latti a zane su Gara ita sun san bata jin tsoron bulalan sosai dan tana mazewa kar a raina ta.
Gidan ta wuce sai da ta ci abinci Inna ni nata mita sannan ta fito ganin tana neman yin latti.
Koda ta fito gida ta ci karo da Iro.Yana ganin ta ya washe baki.Gaba tayi kamar ba zata tanka masa ba da sunan ta da ya kira.
Har ta ɗan yi gaba ta tuno da taimakon da yayi mata jiyan sai ta ɗan ji Tausayin sa hakan ta sa ta ja burki tana juyowa tana kallon sa,sama da ƙasa ta gama ƙare masa kallo kafin ta yatsine fuskar ta sannan kuma ta sake ta.
Sannan a hankali ta amsa da " Na'am " bayan ya ƙara kiran sunan ta har da wani haɗawa da ta.Na nata sunan ta yi wai Shatou ta sannan ta ja ƙaramin tsaki iya laɓban ta shi ko sokon sai ya ga kamar tayi masa wani ɗan style na murmushi daya ga ya ƙara mata kyau.
A haka suka jera suna tafiya Iro na jin kan sa sama sai washe jajayen haƙoran sa yake yi.Dan Shatou hakan ne kawai take ganin mafitar rabuwa da iro lafiya,musamman da ya fara yi mata amfani ko dan haka yanzu dole ta ƙara sake masa dan ya dagargaji maƙiyan ta dan shatou ba dai wayau ba shi ya sa yanzu ta saki fuska tana sauraren labarin faɗan su na jiya da yake bata wani abun tayi murmushi wani ta ɗai juya kai.

*A ɓangaren su MAHAJ kuwa kasancewar suna da lafiyayyun motoci basu wani jimaba suka iso ƙauyen.
Kasancewar ba baƙi suke ba Mubarak da sauran drivers sun san inda ake aikin ya sa basu tafi wajen mai gari ba direct suka kama hanyar wajen.
Jingine yake da seat ɗin motar kamar yadda suka fito da Bluetooth a kunnen sa yana sauraren ƙira'ar minshawi idanun sa a lumshe p cap ɗin sa ya juyar da kan ta baya ya sanya haɗaɗɗen radon sa baƙi wulik mai kyau da ya ƙara wa fatar sa armashi da kyaun sa da yake fitar da wani annuri na haske na Hutu,arziki,da lafiya.
Gudun motar ta su Muby ya rage kasancewar ya hango ta tun daga nesa haka kuma ya gane wanda take tare dashi É—in dan haka ya É—an saci kallon MAHAJ ta glass ganin bai lura da ita ba ya sa da gangan Muby ya ci wani irin burki wanda ya saka MAHAJ dake jingine kamar baya numfashi buÉ—e kyawawan idanun sa masu haske yana sauke su akan Muby É—in.

" Sorry ina gudun rigimar yarinyar chan ne kar mu tada mata da ƙura ya sa na rage gudun motar sai kuma ta nemi kubce mini dole na taka burki da sauri ".
Muby ya faÉ—a yana danne Dariyar sa tuno farkon haÉ—uwar su da ita.Da mamakin ta gata yar mitsitsiya tana fira shi gaulan sai sakin baki yake yana kallon ta.

MAHAJ da bai wani fahimci wace yarinya yake zance ba ya ɗauke idanun sa daga kan sa yana lumshe su kamar yadda suke sai dai kuma jin Muby ya tsayar da motar ya ƙi cigaba da tafiya ne ya sa ya zare space ɗin sa a hankali yana bin Muby da kallo na zargi.
Sai dai bai iya yin kallo mai tsawo ba hakan ya sa ya É—auke idanun sa daga kan sa.
Ya ƙara lumshe idanun sa tare da mayar da glass ɗin na sa.
Tafiya Muby ya cigaba da yi a hankali yana fatan Allah ya sa idon Mahaj ya kai inda yake buƙata yaga Abokiyar faɗan sa.koda suka gota su ya ji haushi na rashin ganin ta da Mahaj ɗin bai yi ba.
Sai dai abun da bai sani ba dai dai sun iso wajen MAHAJ da ya ke ƙara mamakin abinda Muby yayi ya ware idanun na sa da ƙyar ta cikin rado ɗin na sa ta yanda mai zato ba zai taɓa zato ba ya ɗan saci gefe da gefen motar sai dai kamar an ce ya ɗaga idon sa ta gaban su sai gashi ya sauke ganin sa kan ta a hankali kafin Iro,tana ta washe bakin ta abunda bata saba yi ba da kowa idan ba Bibu ba da su Amina.
Dan dai dai lokacin ne Iro yake gaya mata Yadda ya yaga bakin Shamsu ya san harda jini yayi.
Yana bata labarin yana dariya itama haka dan ta ji daɗi ta ji ƙeta.Aiko Iro sai kallon ta yake yi har ya shagala ganin yadda dimples ɗin ta yau suka wani bayyana haɗe da yar ƙaramar wushiryar ta suka ƙara mata kyau na musamman.
Idanun sa ya ɗauke da sauri kamar wanda ya ga kashi dan dukkanin su ya gane su tsaf,kuma idan ba mistake yayi ba abinda Muby yayi,yayi hakan ne dan ya ja hankalin sa.Ƙaramin tsaki ya ja a ƙasan laɓɓan sa wanda shi kaɗai ya ji fitar abun sa.
Har suka gota su bai ƙara ko tada kan kan sa ba hasalima idanun sa a lumshe suke.
Ita kuwa Shatou haka kawai ta dakatar da dariyar ta tana bin danƙara danƙaran motocin da kallo a hankali kasancewar haka kawai ta ji alamar kamar ana kallon ta ganin bata ganin komai har suka wuce ya sa ta janye idanun ta kan su.
Shi ko Iro da ya shagala da kallon ta sai da suka matsa nesa da su kaɗan sannan ya lura da motocin...✍️

Yau dai da alama mutanen zasu ƙara haɗuwa fa 🚴🚴🚴😅
Ohni yar babanta Shatoun ku rigima gare ta.Arado Allah ya sa ta bar mana Mahaj ɗin mu kar ta saka mana ciwon kai.🚴🚴🚴💃💃😂

Page biyu ba haɗe muku na jiya da na yau.🙏🙏🙏🚴🚴🚴
Typing 🥺🥺🥺A samu wata hiliss ta muna typing 🚴🚴

Wannan labari na kuÉ—i ne akan Naira#800

# _FA'EEH BG CE✍️_

Book one free
Book two and three paid N#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haÉ—a document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Daga Alƙalamin✍️
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞

Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔

_*KURMAN ƘADDARA*_

*_©®Faiza Almustapha Murai_*

_*FA'EEH BG*✍️_

P________3️⃣8️⃣

*BOOK ONE*
*_FREE_*

*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t

_*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_

Not edited😴
_____________
Chapter 84 · 0% Book details