← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 110

Sashe 66

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A haka su Baffa na suka same su suna karanta azkar bayan gama addu'oin kasancewar su Baffa na sun tsaya masallacin sauraren wa,azi.
Kamar kullum a tare suka ci abincin daren su su uku.Suna gamawa suka fara taɓa yar fira kafin suka yi Sallama kasancewar gobe Akwai makaranta gashi yanzu shatou na zuwa latti kuma ansha mata faɗa bata denawa saboda kullum da faɗa take zuwa dan bata son karatun yanzu ko kaɗan tilasta mata kawai take jin ana yi dan haka kullum yanzu sai tayi faɗa da Inna ni Baffa na yayi ta Rarrashin kayar sa,Bibu na Dariya a haka da lallaɓawa ake samun tana tafiya,kuma ko taje a banza.
A ɓangaren Baffa na tambayoyi ne bakin sa game da amsar da mai gari ya bawa shatou sai dai kuma ya share zancen kan wani dalili na sa.
A haka Kowa yayi alwallah ya shige suka yi wa juna sai da safe.
Dukkanin su sai da Inna ni ta tabbatar da sunyi addu'oin su kafin ta ƙara shafa musu Sannan ta shige tare da abincin ta da bata ci ba.
Zaune ta kai kan wata yar tabarmar kabar ta dake shimfiÉ—e a É—an tsakiyar É—akin da yake da É—an siminti da ya fara ciccirewa saboda rashin isasshen suminti a cikin sa.
Abincin ta zubawa ido kafin ta haɗiye wani irin ɗaci A maƙoshin ta.Zuciyar ta ta mata wani irin zafi.Hawayen da take ta dannewa ne suka silalo mata kafin ta ji saukar su akan wuyan ta,hawaye ne masu ɗumi dake nuna tsantsar damuwa da baƙin cikin abin da yake tabbas a gare ta wanda ya bar ta cikin kokwanto.
Kuka ne ya ƙwace mata tuno da wani lokaci da ya shuɗe na rayuwar ta,da ta yi cikin gata da soyayya.Sai da tayi mai isar ta sannan ta Share hawayen na ta.Abincin ta fara turawa A hankali tana jin shi kamar tana haɗiyer magani mai ɗaci saboda ƙunci da kewar da ke dabaibaiye da zuciyar ta mai cike da rauni da bege da kewar da bata san adadin ta ba.
Sai da taci rabi sannan ta sha ruwa kafin ta yi addu'a ta nemi waje ta kwanta kan É—an gadon ta.
Wani sabon tunani ne ya ƙara kutso mata dan haka ta kai shi gefe ta rufe idanun ta tana ambaton sunayen Allah.Cikin yardan Ubangiji Kuwa Bacci mai nauyi ya kwashe ta.
Baffa na ya daɗe yana Zarya a Cikin Dakin sa ya kasa bacci,dan ya so ya ji ya ta kaya tsakanin mai gari da shatou ɗin duk da ya san abu ne mai sauƙi amma lamarin na Bashi tsoro shi bai shirya kai yar shi gidan kowa ba yanzu,Sannan yana da dalilin sa mai ƙarfi akan wannan maganan,dan haka duk yadda ya so ya share ya kasa duk da abun ya san mai sauƙi ne.
Numfashi ya sauke kafin shima ya koma kan gadon sa yayi addu,o I ya kwan ta cike da yar damuwa.
Shatou ma babu kwane kwane bacci ya kwashe ta saboda an sha ƙiriniya sosai,haka ma ta ɓangaren Bibu dan shi dama baya wasa da bacci ko ƙanƙani ne.

" Oummm !Oummm! Oummm "
Wannan sauti shine ke shiga cikin Kunnuwan ta yana karya duk wasu gaɓɓan jikin ta wani irin zubawa yaran tayi idanu daga bakin bishiyar da take zaune ta jingina bayan ta da alama iska take sha,tana bin su da kallo kamar ta ga sabuwar halitta.
Sai dai murmushi ta samu kan ta da sakar musu cikin mamakin kiran ta da sunan da suka yi.
Tana ƙokarin riƙo hannayen su ne ta ji an fisge su da ƙarfi ana ƙoƙarin jefa su a wani rami mai zurfi cike da tashin hankali ta ke ƙoƙarin ganin mai shirin yin wannan aika aikar da hana afkuwar hakan cike da tashin hankali...A zabure ta tashi tana mai nana ta Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un fuskar ta jage jage da hawaye na tausayi ga wata irin rawa da zuciyar ta keyi kamar ana kaɗa ganga mai taushi.
Mafarkin take ta, tariyo wa sai dai mamaki ne fal a ranta na wannan suna da suka kira ta da shi.
Fuskokin su take ƙoƙarin hasasowa sai dai ta kasa amma duka muryoyin sun zauna a cikin ƙwaƙwalwarta wanda har yanzu sautin yake ƙara hargitsa tunanin ta tare da girgiza naman jikin ta.
A jiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana shafe zufan da yake tsiyayar mata na tashin hankalin abinda ta gani yake shirin faruwa kafin ta miƙe Tayo Alwallah Nafila tayi gwargwadon iyawar ta sanann tayi Addu'oin ta ta koma bacci sai dai abun ya gagara dan bacci ya ƙi kwasar ta wanda bata samu, ya kwashe ta ba sai gangar asuba.

Yau kusan wata guda kenan Iro bai ƙara tuntuɓar Shatou da wata magana ba Shatou bata san abinda mai gari ya ce masa ba amma ko mene ne taji daɗi sosai dan haka ta cigaba da rayuwar ta hankali kwance cikin rashin damuwa, haka ma Baffa na.Yayi matuƙar farin ciki.Yanzu hankalin Shatoun sa ya kwanta.
Bawan Allah in suka haÉ—u kan hanya yayi ta kallon ta cike da mamakin abun da zai sa mahaifin sa yi masa kashedi da dakatar dashi da soyayyar sa ga shatou duk iya tunanin ya rasa madafa.
Sai dai ya ƙwallafawa ran sa sai da ya samu shatou ko ta ƙarfi ne kuma zai nemi soyayyar ta ko mai gari bai so ba dan shi Dagaske yanzu,son ta yake yi har cikin ran sa,kuma idan har bai samu Shatou ba sai dai abin da ake gudu ya faru a ƙauyen,dan ba zai bar kowa ya same ta ba ya sha wannan alwashin ya fi a ƙirga.
A ɓangaren shatou ƙiriniya yanzu sai abinda yayi gaba ga karatun yan zu idan an tura ta sai ta yi daji wajen farauta tun Inna ni da Baffa na na faɗa har sun zuba ma sarautar Allah ido dan ƙiriri take nuna rashin son karatun na ta yanzu Addu,a kawai suke bin ta da ita.
A ɓangaren Aikin da ake yiwa ƙauyen an samu cigaba sosai aiki na ta kan kama babu kama hannun yaro abun ka ga an zube kuɗi ƙasa.

" Ummahhh " !

REENA ce ta zo da kuka tana sanye cikin wando da t-shirt masu kyau gashin ta ya sha gyara kai da ka gan ta kasan suna cikin gata.Kuka take tana nunawa Ummah É—in hanunn ta wadda ta sha ado itama cikin wata dakakkiyar shadda ta yi kyau har ta gaji.
Dan yanzu ta fito da ga kitchen ta É—an duba abubuwan da aka jera kan dinning.
Hannun Ummah take kallo, ganin ta sangaye shi kamar ya samu rauni da yawa.

" Me ya samu hannun ta furta a natse cike da yar damuwar kukan na REENA "

" Hannu na LEENA ta karya daga kawai na taɓa nata chocolates na tsarabar Yaya Samir ita bata shanye nata ba shine na ɗauka zan sha ko fasawa ban yi ba ta murɗe mini hannu tana kira mini ɓarauniya ".Ta kai ƙarshen maganar tana fashewa da wani sabon kuka.
Chapter 66 · 0% Book details