← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 110

Sashe 14

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana yin maganar cikin ɓacin rai da haushi tana gugar rubutun,su dai sauran yan Ajin su kowa zuba mata ido yayi wasu kuwa dariya suke yi ƙasa ƙasa ba damar a fitar an san halin ta.
Sai da ta goge Allo tass sannan ta dawo tana nishin Masifa tana kallon yan Ajin na su,Amina ta hango daga gefe wadda tayi tagumi dan ta san yau akwai matsala taso ta goge rubutun wasu yan Ajin suka hana ta,ashe ma a banza dan kowane aji dake makarantar anyi rubutun,rubutun da ma yake chakuÉ—e kamar na yan koyo.

" Amina wa yayi rubutun nan,waya tsokano fitinar da tafi ƙarfin sa,na rantse da Allah idan kin san kowaye karki ɓoye ni,dan idan na gano wallahi sai na bar ƙawance dake " Tayi hakan ne dan ta san yadda Amina ta tsani kalmar ta san dole in ta sani ba zata taɓa ɓoye mata ba.

Idanun Amina cike da hawaye ta ce " Wallahi na yi miki rantsuwa da Allahn da ya halicce ni ban san wanda yayi shi ba nidai ko da na zo na tarar dashi na so na goge suka hana ni,Kuma Kiyi haƙuri gaba ɗaya ajujuwan makarantar nan aka yi rubutun amma ni da su Ramata mun goge shi wanda koda muka goge wasu sun riga sun gani ".

Ran shatou ne ya ƙara ɓaci kamar ta fasa kuka dan da gaban su Inna ni ne da ta yi kuka sosai yadda ran ta yake ɓace ko zata rage hasahi.

Zama tayi bata cewa kowa ƙala ba har su Ramata da suke son cewa wani abu,amma bata basu dama ba.
Ajin sai kallon ta suke yi kowa na son ya maimaita sunan yana gudun ruwan masifa dan daga Mazan har matan su babu wanda take shakku.

Har malamin su ya shigo yayi karatu bata sauko ba duk yadda yake jan ta da magana saboda tana cikin ɗalibban Ajin masu hazaƙa tana da kai, sosai take gane karatu both Arabi da boko.

Har aka tashi makaranta shatou bata wani gane ma kan ta ba saboda yadda ta sanya son gane wanda yayi rubutun ta rasa wanda zata hasasowa gaba É—aya kan ta har ya fara ciwo saboda tunani.
Ko ba,ayi ba daga makarantar ta kama hanyar gida,daga zuwa fitsari,da shigar ta ko sallama ba tayi ba ta shige É—akin ta, littafan ta na makaranta ta janyo tun na aji É—aya da suke É—auke da sunayen halittu a bayan su saboda Amina ta faÉ—a mata ance mata wata dabbace ake kira haka mai Shegen gudu.
Tana cikin dubawa kuwa taci karo da ita mummunar halittar dabbar ran ta ne ya ƙara ɓaci har wani numfashi ta ke sauke wa na yadda zuciyar ta take cike da Masifa.Kuka ta fashe dashi na yadda aka haɗa sunan ta da dabbar.kukan ta ne ya ankarar da Inna ni Dawowar ta, kasancewar tana sallah koda ta shigo.Kuma cikin natsuwa ta shigo babu guje guje.

Cike da mamaki ta faÉ—a É—akin na ta zaune ta isko ta haÉ—a kai da guiwa ta na ta darzar kuka.
" Ke lafiya, , wa ya mutu ne,ina kika baro mini yaro na "
Inna ni ta jero kalaman cike da son samun amsar su.

" Yana makaranta ni dawowa nayi saboda kaina na ciwo yake ".
" Shine saboda kan ki na ciwo shatou sai ki zauna kiyi ta kuka".takai ƙarshen zancen cike da tausayin ta dan a tunanin ta Dagske zazzaɓin ne.

Ficewa tayi sai gata ta dawo tare da magani da ruwa.
Ɓalla mata tayi ta bata babu musu kuwa ta karɓa dan ta san halin inna ni yanzu sai ta hasala dan tana da saurin hasala dan kamar duk ita ta biyo.

" Sannu,yanzu ki tashi ki watsa ruwa sai ki samu ki ci abinci ki kwanta ko ".

Kai shatou ta gyaɗa kafin ta miƙe ta cire kayan jikin ta nan gaban Inna ni ɗin ta koma daga ita sai ɗan kan fai dan babu ruwan ta Indai ta so cire kayan jikin ta kowa ke wajen tana iya wa sai dai bazata cire gaba ɗaya ba,gaban Inni ni kuwa zama take da ɗan kanfai.Inna ni tayi faɗa amma ta kasa bari,har gaban Bibu wata rana ta kan cire kayan jikin ta.
Shi ko yayi ta tsokanar ta da "Adda SHATOU ƙatuwar banza mai cire kaya a gaban mutane ".
Daga haka kuma suyi ta zagayen gidan har su gaji.

Kai Inna ni ta girgiza tana murmushi ganin yadda ƙiren dangin na shatou suke maƙale a jikin ta,lallai girma yana hanya.
Jikin ta ne ya mutu mutus hakan ya sa ta fice daga É—akin tana share hawayen da suke son silalo mata masu zafi cike da tausayi Shatou.

Ruwan wanka ta haÉ—a mata ta kai mata makewayi.

Shatou na fitowa ta san cewa ta kai mata su chan hakan ya sa ta wuce makewayin.

Sallamar su Amina ce da Bibu ta cika gidan.

Amsa musu Inni ni tayi fuskar ta wanze da murmushi ta furta " Ya na gan ku fuskokin ku kamar babu lafiya ".

" Eh dama Shatou ce " ....
Amina ce ta fara maganar sai kuma ta yi shiru.
Cigaba da maganar ki.
Nan ta kwashe komai ta faÉ—awa Inna ni.
Kai Inna ni kawai ta girgiza ita sai ma abun ya bata dariya wai shatun ta ce ake kira da kosongo sunan ma abun dariya.
Yar dariya tayi kafin ta furta " Oh ni indo kowa ye da wannan É—an yen aiki " ita kuma shine ta dawo ta zauna tana rusar kuka saboda sakalci ".

Ku tafi kawai sata sauko kunji.

" Toh " suka haÉ—a baki wajen faÉ—a kafin suka bata jakar ta suka fice daga gidan.

" Inna ni,Adda Shatou fa na san bazata bar zancen nan ya tafi ba sai ta nemo wanda yayi aikin nan ".Furucin Bibu.

Kafin ta basa amsa sai ga shatou ta fito tana bin su da kallo dan taji duk taji komai.

Alwallah tayi bata ce komai ba ta shige É—akin ta.

Da kallo duk suka bita ganin yadda ran ta yake jagule har yanzu.
Murmushi Inna ni tayi tana furta "Lallai ran maza a ɓace yake,Bibu kuka fa ta zauna ta shara,dole na taka mata burki ta haƙura.

Ɗakin ta bi shatou tare da jakar ta sallah ta tarar da ita tana yi,aje mata jakar tayi tare da zaunawa har sai da ta gama sallar tayi Addu,oin ta, Sannan ta kamo hannayen ta,ta ce " Shatou na kiyi haƙuri kinji koma wane ne ki bar shi da Allah,zai saka Miki,kuma ma shatou ai ba abun tashin hankali bane tun da bakalar dabbar zaki koma ba.Ta kai ƙarshen zancen tana sakin yar guntuwar dariya tana kallon yar Tata cike da ƙauna.

Kallon Inna ni tayi kafin ta furta " Toh " tana cewa haka bata ƙara cewa komai ba.
" Allah yayi Miki albarka " Inna ta furta cike da murmushi tana ficewa daga ɗakin tare da sanar da ita abincin ta Bibu zai kawo mata idan ta ci ta kwanta ta huta kafin lokacin makarantar su yayi.✍️

***

" Hhhhh ki bar wannan aikin kawai an riga ki,kuma anyi aikin mafi hatsari,aiki ɗaya za,a Miki yanzu shine ƙara hana su kusantar juna,wannan shine kawai zaki yi "
Cike da mamaki take kallon Bokan na ta da ke zaune kamar wani malami sai buge buge yake yi a ƙasa.

" Amma Boka Gangaro yaushe hakan ya kasance dama an daÉ—e da yin aikin ne ".
Matar da ke zaune gaban sa tayi kamar wata baiwa tayi Furucin tana sanye cikin kayan alfarma da mayafin ta na manyan mata,mai tsada.

" An daɗe da yin sa,ya fi ƙarfin shekara goma,anyi shi tun kafin zuwan su duniya,kuma yana nan yana bibiyar su gaba ɗayan su,ki bar aikin a hakan karki shiga cikin wannan gamami aiki ne babba da ya ci shekaru dan haka ki fitar da hannun ki ".

" Boka Gangaro ko zan iya sanin wanda yayi aikin ".

" A'ah karki matsa kar ki jamin bala'i,aiki ne na duhu baƙaƙen Aljannu ke riƙe da shi ,Idan kika matsa zamu halaka mai aikin fitinanne ne,ki iya tunanin ki kar ki ƙara maganar kuma kar ki sanar wa da wani ki bar shi a cikin ki domin zaki iya shiga haɗari,ke kan ki,aiki nane ya cece ki da tuni an gama dake ".

Idanu ta zaro cike da tsoro kafin ta miƙe bayan karɓar yan ƙulle ƙullen na boka Gangaro sannan ta fice da baya daga ruɓaɓɓiyar rumfar sa,bayan ta ajiye masa manyan kuɗaɗe kamar yadda ta saba.

Sai da tayi tafiya mai nisa Sannan ta fice daga cikin ƙungirmin dajin.Motar ta,ta hau ta tada tana ƙara jan Niƙaf ɗin ta.
Sai dai zuciyar ta cike take da mamaki da al'ajabi me ya sa bata taɓa sani ba sai yau.To waye ne yayi mata rigaye gashi ya ce aikin ya daɗe wane mara imani ne wannan.Lallai dole ta ƙara riƙe Boka Gangaro kar ta rasa rayuwar ta.

Wal, iyazubillah 😭

Hmmm.🙄

Hmmmmm Kuna ganin haƙurin nan, na Shatou ya kai zuciya kuwa ?
Wa kuke tunanin ya aikata wannan aiki ?

Gaskiya duk wanda ya tado muna da rigima bai kyauta ba.🚶😂

Like share,and comment 🙏

Wannan littafi na kuÉ—i ne.
Amma in sha Allah Zan baku page goma sha biyu free kamar yadda nayi niyya..
Masu son fara yin payment zaku iya farawa ga details a ƙasa👇
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh 💞

*TAFIYAR TA DABANCE SAI AN BIBIYA AKAN GANE HAKAN.✍️*

*_Typing_*

*💋KURMAN ƘADDARA💋*

*©®Faiza Almustapha Murai*

*FA'EEH BG*✍️

*BOOK ONE*

free pages👌

P..0️⃣8️⃣

>>>>>>>>>>>>>> > >>>>>>>>>>>>>>>

*CONTACT DIS LINE👉08069059746 FOR ADVERT.*

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

Channel link
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

Posting room link
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn

*LITAFFAN MARUBUCIYA*
*A MAFARKI NA SANTA*
*RAYUWAR MU A YAU!*

🤳🤳🤳

Har ta isa aka wangale mata ƙaton gate ɗin gidan zuciyar ta cike take da mamaki mai yawa.Ta so kiran ƙawar ta ta sanar da ita sai dai ba zai yiyu ba saboda gargaɗin da Boka Gangaro ya mata dan haka ta kame bakin ta tayi shiru.

***
Chapter 14 · 0% Book details