← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 110

Sashe 68

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren LEENA kuwa Haushin maganar Ummah ta ji dan haka ta kwasa da gudu tana fashewa da kuka ta shige Bedroom ɗin ta ta saka lock.Sai da ta rushi kukan ta na rashin dalili kafin Bacci yayi a won gaba da ita.Dan haka koda BILAL ya dawo bata sani ba.
Ita kuwa Ummah cigaba da ayyukan su suka yi tare da sauran masu aikin da ke ta kai kawo suna haɗa duk wani abu na buƙata kasancewar BILAL da Ummah ta sanar musu ya iso ya kafin ya shigo tana son komai ya zama ready.
Koda Su Rabi suka dawo sun tarar da motocin su B É—in ga kuma yawan sojojin da aka samu a estate É—in.
A kafaɗa Junaid ya ɗaura REENA dan tayi baccin a zaba sauƙin ta ma sun bi ya wani Babban Pharmacy an siya mata pain relieve anan kuma ya saka ta dole ta sha sannan suka yo gida tare da yar siyayyar chocolate da yayo mata.
Da sallama ya shiga a Babban Falon Na Umma.
Sauke ta yayi akan doguwar kujerar da Bilal yake zaune a gefe ya gyara mata kwanciya tare da ɗaura hannun inda ya dace da ya sha ɗauri sai walƙiya yake yi an shafa masa magani.
Sannan ya ajiye magungunan a kusa da ita,tare da ledar chocolates É—in.
Cikin ɗan kamewa B da ya kasa haƙuri ya kalli Junaid dake gayar dashi cike da girmamawa da yi masa sannu da zuwa ya furta.
"Me ya same ta ne naga an ƙudundune hannun haka,kamar wanda ya samu dislocation"?.
Cike da girmama Junaid yace masa eh shine sai dai shima bai san inda ta samu raunin ba dan Baba Rabi ta kasa faÉ—a masa.
Tunda ya ji cewa Rabi ta ƙi faɗa ya san inda matsalar ta afku sai dai cikin mamaki yake ƙara kallon REENA da fuskar ta tayi jaa idanun ta sun kumbura wnada da gani na azabar da ta sha ne.
Ya ce " OHk "
Sai a Sannan ya karɓa gaisuwar Junaid da ya ƙara maimaita masa dan ya san ya'yan nasu baya ɗaukar wasa.
Cike da kulawa yake amsa masa da masa tambayoyi yana bashi amsa cikin basa girman sa.
Dai dai nan Ummah ta fito Gaisawa suka yi da Junaid ɗin kafin ya fice dan ya samu kiran Abba ƙarami da alama aikar sa zai yi ko abinci za,a kai masa office,dan haka suke yi dukkanin su daga shi Har Abba idan aiki yayi musu yawa sai a dafa akai musu ba sai sun ci na cafteria"n ma'aikatar ta su ba ko na restaurant.Duka wannan sabon Matayen su ne,Ummah da Hajiya dan sun fi sauran kulawa duka a gurin mazajen su duk da suma sauran nayi amma na su na dabanne..

Ficewa yayi yana musu Sallama tare da ƙara yiwa Reena Addu'ar samun lafiya.

Ummah da ta ga Bilal dan bata san har ya dawo ba ta zata idan yayi fresh up ɗin tunda ya cika tun bin sa ya ɗan kwanta ya ɗan huta sai ta gan shi zaune fuskar nan cike da masifa da ko bata tsaya bincike ba ta san ya gane inda matsalar take,dama tun wajen cin abinci yake ta tambayar Inda suke Ummah tace Leena bacci take yi Sarina kuwa sun fita da rabi sai bata faɗa masa ba,dan haka ya kasa yin Bacci ya zo ya ga ƙannnen na sa da yake jin ya shekara bai saka su a idanun sa ba yayi kewar su.
Dan haka yanzu bata ce komai ba sai É—aukar Reena ta yi ta haye sama da ita ta kwantar akan bed É—in ta.kan ta,ta sha fa kafin ta tofa mata Addua sannan ta rufa mata blanket mai taushi ta fito tana sayo mata bedroom É—in.
Rabi ce tsaye tana masa sannu da dawowa cikin girmamawa haka ya amsa mata shima yana sauke kan sa kafin ya ce '' Me ye silar gocewar SARINA ".
Rabi ta fahimci bada wasa ba jin yadda ya kira Sarina É—in dan bata cika jin ya kira su da cikakken sunan su ba.
Cikin ɗan damuwa ta ce '' Ba wani abu bane ba fa Alhaji ƙarami dama chan wajen wasar sune da yar uwa .." ..
Shiru Rabi tayi ganin kallon da ya sauke mata.
Hakan ya sa ta yi shiru ta kasa ƙarasa zancen.
Shima komawa ya jingina da kujerar yana sauke numfashi da ajiyar zuciya wani irin damuwa na dabaibaye shi ya rasa wace irin Masifa ce wannan ke bibiyar rayuwar ƙannen sa shi har ya fara zargin lamarin na su.
Rabi kuwa kuÉ—in da ta zo kawo ma Ummah ne na aikin da Junaid É—in ya biya ta koma kitchen da sauri dan ta ga zuciyar sa ta motsa idanun sa har sun garwaya sun rikiÉ—a.
Yadda jijiyoyin kan sa suke harbawa hakan ya ƙara tabbatar wa Ummah da ta ke ƙare masa kallo tun saukowar ta.
Ta san cewa ya tabbatar da aikin na Leena ne Ita ma ajiyar zuciya ta sauke cike da damuwa.
Kafin ta zauna kusa da shi cike da so ta kamo hannun sa É—aya da ya dafe goshin sa dashi da yake É—an sara masa.

" Soja "

Ta kira a hankali Muryan ta ƙasa ƙasa.

" Kai kake ƙarfafa mini kai da Abban ku,kune na farko wajen ƙarfafa mini akan yara na,me ya sa yanzu zaka bayyanar da taka Damuwar da zata iya linka mini ɗimbin Damuwar da nake ciki,ya ra na suna cikin wata irin jarabawa mai tsani, ban taɓa sanin yan biyu na tsanar junan su ba sai akan na wa,ban taɓa sanin suna cutar da Junan su irin haka ba sai akan nawa shin me ya sa,me ya sa BILAL, Wannan wace irin jarabawa ce ".??
Kuka ne ya ci ƙarfin ta cike da wani irin ɗaci ya rungume ta ya fara rarrashin ta.
" Me kake tunanin mutane zasu faÉ—a akaina akan tarbiyyan su,ina jin tsoro Mai girma akan rayuwar da suke yi mai ban al'aja.."
Kuka ne ya ci ƙarfin ta a karo na biyu Shi kan sa BILAL hawayen ya share masu ɗan ɗumi.
Ya cigaba da rarrashin Mahaifiyar sa Abar son sa yana haɗiye wani irin dutse mai ƙarfi na baƙin ciki mai girma da ya tsaya masa a maƙoshi..
Shiru falon yayi sai Shesshekar kukan Ummah gwanin ban tausayi.
Abba ne da ya shigo tun ɗazu yayi gyaran murya.Shima idanun sa sun kaɗa sun yi jazir wani irin yanayi yake jin zuciyar sa ciki wanda ya daɗe da shuɗe masa wanda yake haɗe da damuwar ya yan sa da yanayin da suke ciki da har yanzu ya kasa natsuwa da zantukan malam Hambali sannan yana tsoron kuskure masa kasancewar ya san Malam babban Malami ne masanin Addini ya san ba zai mishi ƙarya ba duk inda zai je dai maganar ɗaya ce ko kuma ya samu aka sin ta makaman ciyar ta amma har yanzu abunda malam yayi yana ransa na rarraba shafa ruwan addu'ar a tsakanin su Leena,yana jin tabbas akwai abinda malam yake ɓoye masa.✍️

Nifa kaina cigaba da yake da ƙullewa🚶🥺
Amma dai muje zuwa zamu🚴🚴

Wannan labari na kuÉ—i ne akan Naira#800

# _FA'EEH BG CE✍️_

Book one free
Book two paid N#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haÉ—a document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Daga Alƙalamin✍️
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞

Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔

_*KURMAN ƘADDARA*_

_©®Faiza Almustapha Murai_

_FA'EEH BG✍️_

P________3️⃣2️⃣➖3️⃣3️⃣

*BOOK ONE*
_FREE._

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t

*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*

Ba tare da ya ce komai ba ya haye upstairs jiki a saɓule daga ganin yadda yake tafiya sun san yanayin da zuciyar sa ke ciki kai Ummah ta ɗauke daga kallon sa tana sauke a jiyar zuciya kafin ta miƙe ta bi bayan sa.
Guntun murmushi ta sakar wa Bilal kafin ta bar wajen bayan ta É—an bubbuga kafaÉ—ar sa.
Numfashi ya sauke mai zafi tare da ajiyar zuciya kafin ya miƙe ya bar Sashen gaba ɗaya domin wani irin sarawa kan sa ke masa.
Sashen sa ya shige dake iri É—aya da sauran ginukan.
Zaune ya kai kan Corner seater da ke kusa da ƙofa yana sauke numfashi.
Ganin damuwa na neman dabaibaiye shi hakan ya sa ya miƙe ya shige Bedroom ɗin sa da babu wata hayaniya a cikin sa so simple sai ƙyalli yake Saboda ana gyaran sa duk bayan ɗan lokaci.
Hayewa yayi kan gadon na sa bayan ya zare rigar sa Gudun Ac ya ƙara ta hanyar remote ɗin sa kafin ya rufa tafkeken blanket mai taushi dake ƙawace da bed ɗin.
Addu'a yayi ya tofa kafin a hankali bacci ya fara fisgar shi,sai ya fara bacccin ya farka kuma a firgice kamar mai jin tsoro da alama akwai shuÉ—aÉ—É—en lokacin da yake tunowa ko yake gani a idon sa a wannan É—an baccin dake fisgar sa.Addu,oi ya cigaba da yi,Har kuma a hankali bacccin ya É—auke sa mai nauyi dan tafiyar safe ce yayo.

" Na daina damuwa fa Abban su Alina,Kawai dai ina cikin wata irin damuwa ce akan yanayin su Twins,Zuciya ta na shiga ƙunci a duk lokacin da na gan su haka,Abubuwa da dama nake tunawa, abu mafi muni ace naka sa tarbiyyantar da ya ya na "
Hawaye ne suka silalo mata masu zafi kafin ta kalli fuskar Abba da ta yi jaaa Shima idanun sa kamar sun tara ruwa.
Chapter 68 · 0% Book details