Sashe 93
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ne muka yi,abincin mutuniyar ka ". Ai ko shatou take ta wartsake ta miƙe jin abinda Inna ni ta furta nan ta fahimci Inna ni tsokanar ta take yi shi ya ƙara sakar mata da jiki tabbatar da cewa ta haƙura. " Yeeehhh Dankali dankali " Shatou ta furta cike da farin ciki miyan ta har katsewa suke yi.Saboda yadda take son sa. Lokaci guda ta manta abun da ya faru yanzu.Murmushi Inna ni tayi cike da farin cikin sakewar shatou tana cigaba da saƙar ta tana yiwa ya yan nata addu'ar shiriya.Bibu da sauri kuwa ya ɗauko musu abincin tare suka zauna suka ci suka ƙoshi kowanensu na ta zuba santi.A ɓangaren Baffa na kuwa fadar Mai gari ya wuce a chan ya tarar da mai gari ana ta fadanci da jama'ar sa ana ta yaba irin ƙokarin Abbu da Mahaj.Ganin sa da mai gari yayi kuwa dai dai wannan lokaci ya ce " Malam Jibril Sai yanzu ". Murmushi Baffa na yayi kafin ya ce " Eeh wallahi na samu kira tun ɗazu sai dai rikicin Shatou ne kasan ba ƙarewa yake yi ba shine ya tsayar da ni,nan ya labarta ma mai gari komai " ai ko mai gari ya yi dariya Sosai wanda har ya bawa jama'ar fadar mamaki shi kan sa Baffa na Murmushi yake yi. Sai da duk jama'ar suka watse kasancewar mai gari ya ce kowa ya zai iya tafiya. Sannan ya kalli Baffa na ya sake yin murmushi. " Tabbas Farauta Haske zai samu a cikin duhu a cigaba da addu'a Allah ya tabbatar mana da Alkhairiin sa a ko da yaushe ". Amin Baffa na ya amsa yana ƙaƙalo ɗan murmushi da bai kai ciki ba. Sai kuma suka miƙe suka shige wani ɗan ɗaki na mai gari ban san abinda suka tattauna ba amma sun jima sannan Baffa na ya fito zuwa lokacin an fara kiraye kirayen Sallah la,asar. A ɓangaren su Mahaj kuwa suna fita Babban titi suka koma yadda suke kafin suka fara sharara gudu kamar zasu tashi kasancewar Umurnin Ubangidan na su ne. Basu daka ta ba sai da suka samu waje suka yi Sallahn azahar da ke neman wucewa,Sannan suka kama hanyar asalin Abujar.Koda suka isa anyi Sallan La,asar dan haka kai tsaye masallaci Suka sauka suka fara sauke farali. Babu kowa cikin Babban falon dama bai tsammana ba dan haka kai tsaye ya shige Sashen sa.Kai tsaye wanka ya faɗa bayan tuɓe kayan jikin sa.Ya daɗe ruwa na sauka jikin sa masu ɗumi kafin ya ɗauro wanka. Ɗaure da guntun towel ya fito fari ƙar wanda yayi wa ɗaurin saɓu saɓu ga kan sa na ɗigar da ruwa kaɗan kaɗan kasancewar ya ɗan goge sa da towel a cikin toilet ɗin.Bakin fankacecen mirrorn sa da ya kusa ma he rabin bango wanda yake shaƙe da kayan gyara masu tsada da kyau da inganci ga lafiyar fata da kuma turarukkan sa masu Shegen ƙamshi da ƙamsasawa wayen da suka kama bedroom ɗin sa sai kace wani Company na turare. Hand dryer ɗin sa mai kyau ya kunna wadda take a jiye a waje mai kyau ya busar da gashin kan sa tass kafin ya kashe ya koma murza mayukkan sa sai da ya bi ko ina na jikin sa da man sa mai kamshi sannan ya koma gyara gashin sa da ke ta shinning kamar an masa ruwan mai aiko take ya ƙara yin wani irin haske da shinning har wani kashe ido yake yi. Sai da ya gyara sa tass sannan ya taje ya koma ya bi jikin sa da Haɗaɗɗen body spray na sa.Haka kan sa ma sai da ya ji na sa turaren sannan a ɗan gaggauce saboda baccin da ke idanun sa ya bar bakin madubin yana komawa gaban sip ɗin sa kasancewar sip ɗin ta sa mai taya ce kafa kawai ya saka ta buɗe da kan ta ƙananan kaya ya zaɓa mara sa nauyi daga cikin dubannin kayan dake tsare cikin ta cikin tsari mai kyau gwanin burgewa komai dai irin na luxury life babu ƙaramin abun a ciki. Saka kayan yayi wanda suka kasance guntun wando ne na mai santsi mai haɗe da vest fara ƙal kamar yanayin wandon. Yana gama kimtsawa ya saka turarukan sa masu ƙamshi.Masha Allah, yayi kyau kamar wanda zai je wani taro ɗan tsaye yayi bakin mirrorn ya ɗan zuba ma kan sa ido kafin wani tunani ya shigo ƙwaƙwalwar sa hakan ya sa shi jan guntun tsaki mara sauti kafin ya ɗaga ƙafa a hankali ya kwanta kan gadon sa bayan ƙure gudun A C,da rage haske. Yana kwantawa kuwa bacci mai daɗi ya kwashe sa duk da ya ɗan yi ta juye juye Kafin ya kwashe sa. Muby kuwa Bai zame ko ina ba sai part ɗin Abbu cike da zumuɗi. Koda yayi sallama tare da knocking a ƙofar falon Abbu,Abbu na zaune yana duba wata tsohuwar jarida ya zuba mata idanu bazaka taɓa iya tantance yanayin da yake ciki ba sai dai daga yanayin fuskar sa zaka shaida ba mai kyau bane,domin kuwa jikin sa a sanyaye yake dan tun bayan dawowar sa meeting da Mr president ya ke aikin karatu ko muce na zarin wannan jarida dan yau ko Amma bata gane wa kan sa ba abinci ma bai saka a bakin sa ba wanda kuma bata damu ba domin inda sabo ta saba da wannan yanayin na sa dan haka ta share sa kafin ya dawo dai dai. Koda Abbu ya ji knocking kuwa ɗan zuba ma ƙofar idanu yayi dan hankalin sa na kan su Mahaj ɗin sa dan haka yayi zaton shi ne ya dawo,miƙewa yayi ya mayar da wannan jarida cikin wata locker mai kyau sannan ya saka makulli ya rufe ta yana saka keys ɗin a cikin bedside drower. Sai da ya ɗan sanya wa kan sa jarumtar ɓoye yanayin da yake ciki kafin ya bada izinin shigowa.Cike da Sallama Muby ya buɗe ƙofar yana kutsa kan sa ciki bakin sa dauke da murmushi,cike da girmamawa ya duƙar da kan sa ƙasa ya gayar da Abbu da yi masa Barka da gida wanda ke zaune a kan kujerarar sa ya ɗan miƙe kafafun sa akan Centre table. Cike da farin ciki Abbu da yayi zaton Mahaj ɗin ne wanda sai yanzu ya tuna da sai ya huta yake zuwar masa idan ma har yanzu suka dawo. " Kun dawo kenan ya hanya ".