← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 110

Sashe 82

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Bibu yayi maganar yana kallon ta.
Kai ta girgiza masa kafin ta ce a hankali " Lafiya ta lau fa barci ne kawai ya kashe n,kuma Inna ni bata tashe Ni Sallah ba,gashi sai dai nayi ranko ".Tayi zancen kamar zata fashe wa da kuka dan bata son fashin sallah ko kaɗan ta san zunubin da mutun ke samu wasu malammai ma sunce ba,a karɓanta.Haka malamin su ya sanar musu dan haka take jin tsoron fashin sallah wanda zai saka ta tarikussalah ba tare da dalili mai ƙarfi ba.Na daga cuta,ma,ana rashin lafiya ko tafiya.d.s.
Shiru gurin yayi Baffa na kuwa ajiyar zuciya ya sauke domin kuwa abun da yake zargi ne ya ga ya tabbata dan har yanzu ko kwanto yake yi.
Inna ni kuwa ba tace komai ba itama sai cigaba da jan charbin ta da tayi tana sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya.
Shatou kuwa daga gama maganar Addu'oin ta, ta fara yau babu wanda ya ji abinda take cewa dan cikin zuciyar ta take yin abarta.
Yau Baffa na sai ya ga kamar ta ƙara hankali dan haka ya ke satar kallon ta kafin a hankali murmushi ya ɗan suɓuce masa na gefen baki.
Bibu shiru yayi yana mamakin ta kafin kuma ya miƙe ya ɗauko Kitabul azkar na su bayan Baffa na ya bashi umurni sannan ya dawo ya zauna.
Baffa na ya cigaba da bita masa haka Shatou jikin ta har rawa yake yi ta zo ayi karatun da ita aiko tana gamawa ta dawo kusa da Baffa na bayan ta gayar da Inna ni da ta amsa mata fuska sake.
Haka shima Baffa na tayi masa ina yini duk mamaki suka yi dan ba kasafai take wannan gaisuwar ba Ƙiriniyar ta bata barin ta gaisuwar maraice ta safe ce kawai wannan babu fashi dan Bibu yafi ta ƙoƙarin musu ina yini bayan Sallahn magriba.
Daga shi har Inna ni murmushi suka yi Acikin zukatan su dan mamakin ta sai dai sun shanye abun su ba zaka taɓa ganewa ba.
A haka Baffa na ya cigaba da bita musu azkar É—in suna sakawa akan su har suka yi wanda ya wadata kowannen su ya bita da kan sa zuwa lokacin kuwa an kira sallahn Ishai.Baffa na da Bibu masallaci suka wuce su kuwa suka tada Sallahn su anan take.

Koda suka gama Sallah Shatou ka sa haƙuri tayi dan haka ta buɗe bakin ta tace " Inna ni wai banda lafiya ne,naji Bibu nace wa wai Ya jiki na,kuma lafiya ta ƙalau bacci kawai na sha ".

" Sai kuma kema É—azu da na tashi naga kamar kinyi kuka wani abu ya shigar Miki ido ne " ?

Haka ta jerawa Inna ni tambayoyin wadda ke jan charbin ta hankali kwance.
Ɗan kallon ta Inna ni tayi kamar bazata tanka mata ba sai chan ta ce " wai dukan da malam Abu ya Miki ne ya ke Miki ya jiki kan sa,Nima kuma ɗazu wani abun ya faɗa Mini ido kamar kin sani da ƙyar ya fita ido na ".
Kai shatou ta gyaɗa cikin yarda ta ce " Sannu " cike da tausayin mahaifiyar ta ta. kafin kuma ta ƙara furta " Inna ni Zanje Dandali yanzu ".

" Da wuri haka ".

Inna ni ta furta tana jin babu daÉ—i dan bata son fitar ta gaba É—aya kwanan nan an ma yi sa,a yau ta tambaya da sai dai a neme ta a rasa ta ja Bibu sun fice.

" Ehh wasan gala gala zamu yi,kuma yau bana son Rakiyar Bibu yayi baccin sa ".

Kai Inna ni ta jinjina tana sauke ajiyar zuciya kafin ta ce.

" Abin cin kin fa ba,ba kya jin yin wa ne " ?

" Eh na ƙoshi sai na dawo ".

Kai Inna ni ta girgiza kawai kafin a hankali ta furta.

" Ki kula in kika fita kuma banda yin dare ".

Cike da farin ciki Shatou ta ce.

" Tau zan kula ".

ko gama Addu,an bata yi ba kuwa ta miƙe ta chanzo riga yar doguwa ta atamfa da ta ɗage mata sannan ta ɗauro ɗankwali irin dai shigar da kuka san matan ƙauye na zuwa dandali da ita ta fice bayan ta yiwa Inna ni sai ta dawo.
Koda ta fita Inna ni ajiyar zuciya ta ƙara saukewa tare da bin ta da addu'ar kariya.
A ɓangaren Shatou kuwa tana fita gidan su Jawairiyya ta fara shiga da ke kusa da su maman Jawairiyya da gama sallahn ta kenan ta kalle ta da mamaki ta ce.

" Wai dandali za,a je yanzu da wuri haka,Amma dai A'i bata gan ki bata san kin fito ba ko,wannan irin sako haka " ?

" Sai da na tambaye ta sannan ".
Chapter 82 · 0% Book details