Sashe 63
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Aaa ga Umman ku chan "
" Amma mata ta bata isa haihuwar irin ki ba ga dai iyayen ku nan " Ya nuna Ibrahim da suke kira Abba ƙarami.
Murmushi Abba ƙarami yayi yana karasa shigowa ciki dan baya nan bai daɗe da dawowa ba daga tafiyar kwana ɗaya da yayi,dan haka yau koda ya dawo bai samu shiga Sassan iyayen na sa ba, sai a masallaci suka haɗu da sir yana son yaga mahaifiyar su,da rigimammar kakar ta su dan haka ya fara shiga sashen Ummu Uwani ya gaida ita sannan ya yo nan.
" Abba ƙarami ina wuni " Leena ta faɗa kamar wata mai hankali ita kuwa Reena hannun sa ta maƙalkale tana dariya tana cewa " Abba Wai Ummu Uwani bata haife Ni ba ".Dariya yayi ya shafa kan ta kafin ya ce " kin ga ummun ku chan,waccan tsohuwar mara haƙora,gashi kun ƙi saka mata artificial ta samu na cin kilishi ".
" Wacchan ta chan ta mu ce "
Dariya ta yi haka kowa dariya yayi yadda Abba ƙarami ke bayanin kamar irin yana mata wani karatu ne da ake buƙatar demonstration dan fahimtar ɗalibai.
Hajjow ma murmushin ta yi tana masa daƙuwa.
Kan sa ya shafa kafin cike da girmama ya gayar da Su Sir,Dada ,Hajiya Sannan cike da girmama Ya gayar da Abba shima cikin basa girman sa na Babba.
Amsa gaisuwar Samir yayi yana hararar sa.Dariya Samir yayi yana shafa kan sa dan ya san dalilin hararar ta sa bai shiga Ya masa sannu da dawowa ba dan sashen Momcy ya sauka chan,sannan bai faÉ—a masa zai dawo ba.Sai dai ganin sa yayi É—azun a masallacin Sallahn la,asar shine har yanzu bai huce ba.
Matsawa yayi kusa da Maama cike da tsokana ya ce " Yar tsohuwa mai ran ƙarfe an buga dake an barki,ni da Yaya Sai zancen Jallof ɗin ki mu ke yi "
Yanzu kam Maaama bata yi kuka ba sai wata harara da ta sakar masa tana É—auke kan ta da tura baki gaba kamar dai yadda kuka san Leena na yi.
Dariya duka suka sanya har su Hajow haka suka cigaba da tsokanar ta Samir na karewa yana juya abun kan Su Sir Abba ƙarami na masa daƙuwa shida Abba. Lafiyayyar Dinner ɗin da Mai aikin Hajjo ta haɗa suka zauna gwanin burgewa kowa ya ci ya ƙoshi suna gamawa suka fara taɓa ɗan fira kaɗan wadda ke nuna shaƙuwar dake tsakanin a halin kafin suka yi sallama a tare Abba ƙarami da su Leena da Samir suka fito daga sashen harda Dada sai dai kowa na sa ɓangaren ya nufa.
Ummah da ke zaune falon ce ta rafka ta gumi kamar wadda ke cikin damuwa ta ga shigowar ta su idanu ta zuba musu cike da so da ƙauna kafin ta yiwa Abba sannu da zuwa yana zama kuwa ta miƙa ta shige kitchen ta haɗo masa shayin sa da yake sha asashen ta kusan kullum dan ta san sun ci abinci chan kamar yadda suka saba yi idan sun tafi Sashen Hajow ko Dada ɗin,sai bata tambaya ba.
Su Leena kuwa kasancewar akwai school gobe Abba ya ce kowa yaje yayi brush yayi alwallah ya yi wanka ya kwanta dan su tashi da wuri haka kuwa ya kasance babu musu suka wuce sama bayan sun yiwa iyayen na su sai da safe.Daki ɗaya suka shiga na Reena dan ita giwar shiga na ta rigima ne da matsala ga Reena ɗin dan duk abun da ta taɓa sai an yi faɗa kan sa amma ita idan shekara za,ayi akan na Reena ko a jikin ta haka ita mai ɗakin bata taɓa damuwa ko kaɗan sai ma ta ka tsaan tsan da take yiwa halin yar uwar ta ta,tun da ta fahimci saurin fushin ta akan ta yake.
Abba na shan shayin suna taɓa fira a hankali cike da so da ƙauna basu ko share awa ba wajen suka miƙe suka wuce sama a tare suka shige bedroom ɗin Abba dake sashen wanka ko wannen su ya yi suma kafin suka bi lafiyar gado shi dai Abba bai daɗe ba bacci ya kwashe sa rungume da matar sa a jikin sa.
Amma Ummah ta daÉ—e tana juye juye Kafin bacccin ya kwashe ta mai nauyi.
Chan ba,a haura ko awa ba ta miƙe a firgice tana sakin ƙara wadda ke nuna alamar tsoro miƙewa Abba yayi yana Nana ta Inna lillahi wa Inna ilaiihi raji'un yana kunna bedside lamp dake gefen ta ai ko ta haɗa zufa sharkaf.
Addu'a yayi ta tofa mata kafin ta samu natsuwa ta fara sauke numfashi.
" Lafiya kuwa Bary mugun mafarki kika yi ne " ?
Kai ta girgiza masa tana É—an sakin murmushi sannan ta ce " Wai fa yanzu baccin ya kwashe ni,shine naji kamar kenkeso a cikin jiki na yana mini ya wo shine fa na tashi a firgice ka sanni da tsoron coacroch "
Abba dai zuba mata idanu yayi cike da tausayi dan ya san mafarkan da ta saba yi ne a chan baya wanda har yanzu ta ƙi bayyanar masa da asalin abun da take gani so ɗaya ne zai iya cewa ya ji ta yi wani furuci a cikin mafarkin wanda ya ɗarsa masa mugun tausayin ta,da na sa tausayin dana ya yan sa baki ɗaya, wanda kuma yana tunanin har yanzu bata tuna mafarkin ba,saboda bai taɓa jin ta masa zancen sa ba sai dai yana ganin ta cikin damuwa a wasu lokuttan ya san cewa abun ne ke damun ta matuƙa,dan haka kasancewar shi shirme ya ɗauki abun ya watsar dashi nan inda ya ji shi dan ya san wanda ya mutu baya taɓa dawowa duniyar nan ya tafi kenan dan haka mafarkin nata aikin shaiɗan ne musamman irin wannan.Ko yanzu ya san bai da na saba da irin wancan da ya ji dan haka yake cike da wani irin mugun tausayin ta da na su Leena.
" Kiyi abunda ya dace,Allah ya sauƙaƙa ya yaye muna damuwoyin mu "
A hankali ta furta
" Amin " Kafin ta juya gefen hannun ta na dama dama ta kuskure ne ta kwanta a na hagu.
Ta ƙara shafa addu'oi sannann ta rufe idanun ta.
Abba ma numfashi ya sauke kafin ya fara yin sabuwar Addu'ar ya tofa mata ya shafa mata sannan ya shafe ma jikin sa cike da kulawa.
Bai daÉ—e ba bacci ya kwashe sa.
Ita kuwa Ummah baccin ne ya gagara sai ma wani dogon tunani da ta lula a hakan bacci mai daÉ—i ya kwashe ta.
" Wai Ni Samir abokin wasan ka na koma eh "
Abba ƙarami ne riƙe da kunnen ɗan na sa na fari Samir yake zancen bayan fitowar su daga sashen Sir inda suka sosai sashen Hajiya mahaifiyar su Samir ɗin dan Sashen ta ya koma da daren nan kwanan ta ya fara.
Yar ƙara Samir ya saki kafin ya ce " Abba ƙarami na fa kira ka ba ka ɗaga ba kwana biyu da suka wuce niko na zata ka shiga busy shi ya sa ban neme ka ba ".
Dun gure masa kai Abban Yayi kafin ya shafa kan sa yana murmushi ya furta " Na yarda ka barranta ".
Dariya Samir yayi yana shafa kan sa da murza kunnen sa yana ɗan ɓata fuska.
Hajiya da ta fito yanzu jin motsin su ta saki murmushi kafin tace " Sannu da dawowa Abban su,Yawwa mar atussaliha"
Murmushi ta saki haka ma Samir dake shafa kan sa dan ya san halin mahaifin sa babu ruwan sa a gaban su yake yabon matar sa kuma eh ai Hajiya ta chanchanta rayuwar su da Ummah abun burgewa ce a gare sa dan haka yake son koda zai yi aure matar sa sai ta koyi dabarun zama da jama'a a da miji a wajen Ummah da Hajiya dan rayuwar su na burge sa.
" A kawo muku Dinner É—in nan ne "
" Kwantar da hankalin ki,kin dai ci kin ƙoshi ko keda zarata na ".
Kai Hajiya ta gyaÉ—a ma sa tana murmushi kamar yar yarinya.
Shima murmushin yayi ganin yadda ta bashi amsa.
Samir kan gaba yayi yana musu sai da safe.
" Mun ci abin ci sashen Sir da su Yaya "
Kai ta jinjina kafin ta mayar da komai inda ya dace sannan ta dawo ta kama hannun mijin na ta suka wuce na su Bedroom É—in su.
Koda suka isa Lagos lokacin magriba yayi dan dama tafiyar maraice ce suka yi manyan motocin na sojoji ne suka zo suka kwashe su cike da tsari sai a salin ƙaton gidan sa da ke nan.
Shaf shaf suka yi alwallah suka yi masallaci dan gabatar da sallah wadda har an wuce su da raka'a É—aya.
Bai fito daga masallacin ba sai da ya gabatar da sallahn Isha sannan gaba É—ayan su suka fito kafin suka yi sallama da ogan na su dan sun san da ya shige ya shige bare sun yi tafiya yana bukatar hutawa.
Kayan sa da Ab ya jera masa su a inda ya dace ya kalla kafin ya girgiza kan sa dan sai da ya ce masa kar yayi ya bari ya zo zai yi komai da kan sa.
Wanka kawa yayo ya bi lafiyar gado babu wani tunani bayan yin addu'a bacci yayi gaba da shi.