Sashe 31
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kallon kallo aka fara tsakanin Amina da su jawairiyya kowa zuciyar sa na rawa har ta Bibu sai dai yafi su ƙarfin hali dan haka ya gyaɗa kai alamarsun amince.
Numfashi SHATOU dake jin kamar ta hau su da duka tayi dan yanzu su kaÉ—ai ne zasu kashe mata case É—in,ya kasu saboda tare take da su dole za,a yarda.
" Eh ta tafi Daji dan duk da mun riga ta fita, sai da muka jira ta,kuma tana fitowa ta kama hanya,zuwa daji kuma dama tace yau zata je wajen farauta,sai nace mata kar ta je saboda za,ayi baƙi kamar yadda na samu labari a makarantar,shine da aka tashi ta wuce,mu ma muka biyo bayan ta,zuwa gida,Sai dai hankali na bai kwanta ba,dan haka na yi niyyar bin ta dajin nace su Amina su wuce gida,nabi bayan ta sai dai kafin ma na ƙara wani tako muka hango ta a Guje,kuma na san duk abunda ya saka Adda SHATOU a tsoro babba ne,dan ta yuyu mafaɗaciyar kura ta haɗu da ita ta tsorata shine ta yo gari ".Yana kai ƙarshen zancen yayi shiru.
Kowa dake wajen ya ji ya gamsu sai yan kaÉ—an daga cikin su irin su Iro da su Zaidu .
Amina ce ta ƙara da cewa" ai ni na riƙa mata jakar ta gata nan wajen har da kayan farautar ta na ciki ma da ta manta da su ".
Ta Fiddo da kibiyar tana nunawa mai gari.
Su jawairiyya Nana ta zancen suka yi irin na Bibu.Kafin wajen yayi tsit bayan É—an cecekucen da aka fara.Wasu na furta Baffa na ya daina barin ta ai bai dace ba tana mace ma tana shiga daji farauta ,yanzu da kurar ta mata illa fa masu tausayi ke wannan zancen musamman ganin yadda SHATOU ke hawaye irin na tana cikin tsoro har yanzu.
Kafin ta kware ɗan ƙaramin bakin ta ta fashe da kuka tana furta " Baffa nidai mu bar garin nan,kar kurar nan ta zo har gida ta chanye ni,dan ta ga fuska na " .
Wata sabuwa Baffa na ya furta a ransa duk da ya san shirme ne irin na ta da rashin jin da yake hawa kan ta yanzu.
" Yi shiru ba zata dawo ba kinji zan je na farauto ta hankalin ki ya kwanta shikenan ".
Kai SHATOU ta gyaɗa tana share hawayen ta.Su ko su Amina da su Bibu dariya ce ke cin su sai dai babu halin yi dan sun san tayi duk wannan dan kawai mutane su ƙara yarda da ita.Shiru tayi ta makure kamar yar Marainiya.Sai kuma ta bawa mai gari tausayi musamman tuno da zancen Baffa na.Jikin sa ne yayi sanyi dan haka ya yi shiru shima kafin wurin ya ƙara samun natsuwa sannan ya furta " Daga shaidun da muka samu na tabbatar da SHATOU a kan gaskiyar ta take dan haka daga yau Jibril kar ka ƙara barin ta shiga daji,haƙƙin ka ne kare wannan yarinya kamar yadda ka ɗaukar wa Allah ya yan mu amana ne a gare mu,Dan haka ka kula da kyau,Na san ko ban bincika ba A'i na cikin tashin hankali a yau dan haka a kula da kyau,Shatou a daina shiga daji kinji Allah ya tsare gaba ".
Zancen mai gari.
Tun da ya fara zancen Baffa na yake murmushi cike da jin daÉ—i dan haka ya É—ago yayi masa godiya cike da girmamawa.
Ita kuwa SHATOU dariya ke cinta marar control dan haka ta cije bakin ta gamm ta ƙi cewa komai sai kai da take langaɓewa irin na tausayi ɗin da wanda yake cikin tsoro.Sai kuma Haushin mai gari da ya kira sunan Inna nin ta a gaban jama'a.
Miƙewa suka yi bayan furucin mai gari da ya furta " Na sallami kowa ".
Sake da baki Iro ke kallon SHATOU da ta sakar masa muguwar harara da Gwalo dan cike take dashi jin shine munafikin da ya ƙarya ta ta ashe.Dan haka yanzu ƙyat take jira ta masa rashin mutunci cikin ruwan sanyi duk da har yanzu bata haƙura da sunan da yayi mata ba ya tozar ta ta,dan ma tsaye take da sunan ya bita dan kowa na shakkar ta ne da tuni ba shatou take amsa wa ba.
A ɓangare ɗaya kuwa zuciyar sa kwata kwata bata yarda da zantukkan su Amina ba.Dan haka yake bin su da kallon tuhuma yana son su Kalle sa cikin ido sai dai kowaccen su tayi ƙasa da kan ta ta ƙi bashi dama.
Ƙyafci yayi wanda ya sauka a cikin Kunnuwan SHATOUn kuma ta san da ita yake dan haka ta ƙara sakar masa muguwar harara kamar idanun ta zasu zube gaba ɗaya sannan tayi gaba a bin ta su Baffa na a bayan ta.
Haka taron ya watse wanda kafin ma ya watse mai gari ya miƙe dan zagawa.
Dariya take ta wangala tana tsallen murna in ta rungumi Amina ta rungumi Bibu Takoma ta rungumi Jawairiyayya,Ramata,sai yanzu dukkanin su suke sauke kwandon dariyar dake cikin su.Baffa na da suka baro Baya kallon ikon Allah kawai yake yi tare da sakin murmushi dan shi kan shi ya san babu gaskiya ko ɗaya a zancen su bai ma san sadda aka saka kibiya a jakar ta ba,mamakin ma.wayon su yake yi yana musu kallon haka haka yara masu cike da ƙuruciya dukkanin su dan har bibun bai yi tunanin zai iya tsaro zance haka ba wanda ba,a yi ba.
Har suka kawo gida suna dariya tare da gwada irin yadda wani ɗai daga cikin masu kuɗin garin su ya ke gudu ciki ture sai su ƙara tintsirewa da dariya suna cigaba da kwaikwayon sa,Tafiyar Iro ce ta ƙwanbo ta faɗo ma SHATOUn arai hakan ya sa ta ƙara sakin wata mahaukaciyar dariya dai dai ta shiga gidan babu ko sallama sai gata ƙasa tana dariyar ƙeta tana ambaton Iro tare da yin tafiyar ta sa wadda ba SHATOU ba har su Amina da Inna ni da ke kallon ikon Allah sai da ta dara haka ma Baffa na dariya yayi kaɗan kafin ya samu kujerar roba da suke da ita gidan ƙwaya ɗaya ya zauna yana sauke numfashi.
Inna ni da ta tsinci kan ta cikin nishaÉ—i ganin farin cikin yar ta hakan ya sa ta cigaba da sakin murmushi fuskar ta na washe wa da ga Damuwar da ta ke ciki wadda suka bar ta ciki tun fitar su.
Ruwa ta É—ebo ma Baffa na masu sanyi a randa ta ajiye masa.ÆŠauka yayi ya sha yayi hamdala.
" Ke wai uban me kuke yi wa dariya haka kamar wayen da suka kode eh,babu sallama haka kuka faÉ—o mana cikin gida "
Cewar Inna ni.Tana son tambayar Baffa na amma ta san ko ta tambaya idan bai ga damar faÉ—a ba ba faÉ—a zai yi ba.Haka ma su Amina ta san idan har SHATOU bata basu dama ba,ba faÉ—a zasu yi ba sai dai ayi ta yar kallon kallon tsakanin su.
Shiru SHATOU tayi tana dakatar da dariyar ta har su Bibu ma kafin cike da murmushi tace '' Babu komai Inni ni dama Iro ne ".
Sai ta kwashe labarin yadda yayi ta ƙwanbo a ɗazu.Inni da ta gama jin komai dariya tayi mai isar ta sannan ta ce " Allah ya shirye ki Shatou ".
" Amin,Inna ni ta "
SHATOU ta amsa.
Baffa na dai murmushi yayi kawai yana ƙara mamakin wayan Shatou yanzu ƙiri ƙiri ta ɓoye wanchan laifin dan ta san halin Inna ni yanzu sai dariyar ta koma kuka.
" Yanzu dai kuzo na zuba muku abinci kuci sai kowa yaje yayi wanka a fara shirin makarantar islamiyya ".
Cewar Inna ni wadda take mamakin wayon SHATOU dan ba wannan zancen ta so ji ba dalilin kiran mai gari take son sani,amma Æ™iri Æ™iri Shatou ta kawo mata maganar da ba ita ba.Kuma ta san cewa dagan gan tayi dan ta É“oye wancan zancen kuma tun da aka yi haka zai yi wahala ta san abinda ya faru waje.Amma zata bincika ko mene ne dan mai gari baya kira banza musamman kiran Shatou.âœï¸
Ayi haƙuri ba yawa.
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Commente,and like pls ðŸ™
_*💋KURMAN ƘADDARA💋*_
_©®Faiza Almustapha Murai_
_FA'EEH BGâœï¸_
P..1ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
*BOOK ONE*
PAID
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*
🕳ï¸ðŸ•³ï¸ðŸ•³ï¸
Tun da suka isa bai fito ba ko nan da falo ne.Babu abun da ya taɓa tunda ga abincin rana har dare da ke jere a kan dinning da aka shirya masa saboda sun san da zuwan sa AB ya sanar da Dawowar su.Ganin hakan ya sa suka kasa haƙura ganin shirun yayi yawa gashi ya kashe duka wayoyin sa dan haka suka kira Ummah kai tsaye tsakanin wadda itama hankalin n ta tashe dan ma su Sir sun kwantar mata da hankali zai neme su dan ta basu labarin abinda ya faru,dan suma sun jinjina lamarin na su Reena.