Sashe 69
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
" Ƙarfin gwiwar da kike bani itace nake kai Bary,da Badan yadda kike ƙarfafa mini ba da bana tunanin zan kai wannan lokaci bary me ya sa ƙaddara ta mana haka,wace irin jarabawa ce yaya na suke kai ".Shiru yayi,Ɗumin da ya ji a gefen idon sa ya shafo hawaye dai ne masu ɗumi ɗan murmushi ya yi yana haɗiye sauran kafin ya shafe ma Ummah na ta da suke cigaba da kwaranya.
Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi wadda har shi kan sa sai da ya ji ta dan haka ya zuba mata idanu.
Sanin ma'anar ajiyar zuciyar ta ta da tayi ne,dan haka a hankali ya furta " ina ƙara baki haƙuri Bary ki cigaba da haƙuri komai zai wuce jarabawar mu ce hakan ina iyakar ƙoƙari na gurin nema mana sauƙi wajen Ubangiji abinda yake damuna ya yaye muna baki ɗaya ".
" Kuma in sha ALLAH Allah zai yaye muna zai dubi zukatan mu masu kyau ".
" Komai zai zama tarihi ki cigaba da haƙuri Sannan ba zan gaji da neman gafarar ki ba."
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi bayan jin ta akan ƙirjin Abba wanda yake sauke numfashi a jejjere kamar wanda yayi tsere dan a duk lokacin da ya samu kusanci da Ummah haka ya kan ji sauyin yanayi a jikin sa sai dai yana iya ƙoƙarin sa na dannewa.
Sun jima a haka kafin ya sake ta yana rintse idanun sa.
Miƙewa yayi ya shige toilet ruwa ya sakar ma jikin sa kafin ya zare kayan jikin sa ya ɗauro wanka.
Ummah kuwa idanun ta ta rufe tana jin gina da gadon tare da sauke ajiyar zuciya.
Sai kuma ta buɗe idanun ta ta zuba ma ƙofar toilet ɗin idanu.
ÆŠan murmushi ta saki a hankali kafin ta share wani hawayen da ya silalo mata.
Sannan ta fice daga É—akin tana shigewa nata.
Kayan jikin ta ta cire itama kafin ta shige toilet wanka.
*Tsut haka ta bayyana gaban sa kamar yadda ta saba zuwa wajen sa a koda yaushe cikin shigar ta da ta saba.
Hahahhahhha Dariyar shi ta karaÉ—e ilahirin dajin.
Wadda take fita iri daban daban.
" Ta Baiwa yar Baiwa Uwar Mugaye yau da wace aka zo,ki faÉ—a da bakin ki aiki ya fi ci haka ".
Gyaran zaman ta tayi kafin ta gyaran zaman mayafin abayar ta cikin wata murya dake nuna damuwa ta fara magana
" Hankali na ya kasa kwantawa ne Dan Baiwa,Har yanzu gani nake kamar babu abun da zai ci da kyau game da aikin mu duk da akwai wasu alamomi da suke bayyane,Sannan Duhun nan da ka yi magana akan sa ya kamata na san me ne ainahin abunda ke cikin sa,haka kawai nake jin kamar akwai matsala ".
Dariya ya fara gaggaɓa yana kallon ta idanun sa na wani irin fitar da hucin zafi na kalmomin ta da take fitarwa kamar bata yi imani da shi ba kamar yadda ta faɗa baya.Dan haka cike da wani irin haushi ya ce " Ta Baiwa kin halaka,kin halaka ".
"Mun halaka ÆŠan Baiwa,ka wuce gado,ba gaba da gaba ko ta baya sai an shirya,Sarkin mugaye uban su É—an duhu da duna ".
Ta yi Zancen itama hankalin ta kwance dan ta san zai sauko saboda ɓacin ran da ya shiga yanzu.
Laƙwass Haka Ƙaton bokan nan yayi kafin ya kece da Dariya har sai dai ya kai ƙasa yana mulmulawa jikin nan na sa kamar tsohuwar ƙwarangwal.Abun dariya abun haushi.
Sai da ya gama sannan ya miƙe ya ce " kwantar da hankalin ki Lallai sai na bincike wannan abun da ke cikin duhun nan,Bana son ki koma damuwa akan sa,maganar hankalin ki tashe yake ki ƙara imani zai kwanta Ta Baiwa,aikin mu yana nan yana tafiya dai dai kedai ki cigaba da zuba ido ki gani zaki ga kammaluwar sa dai dai lokacin da ya kama ta " .
Kai ta gyaɗa masa kafin ta kece da dariya kamar zararrriya ta furta "Lallai nayi imani da kai Ɗan Baiwa na san zaka cika mini buri na,Ka ƙara mini maganin masu mini kutse na fara hango cigaba ".
" Hhhhh Ta Baiwa ta Ɗan Baiwa Mai ja dake sai ya shirya,Son zuciyar ki na burge Ni,Rashin imanin ki shine ya ƙara wa su ɗan duhu ƙarfin Miki aiki lallai kin ci lambar yabo nan gaba kaɗan za,a Miki naɗin Uwa ta su ɗan duhu aiki ɓagass,ki saka ki hana ".
Wal iyazubillahðŸ˜ðŸ˜ Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un 😠Masu halin ta baiwa fa suna da yawa wallahi suna nan atsakankanin wannan duniya suna aikata É“arna son ran su.Ba tare da tunanin yau da goben su yadda zata kasance ba,ba tare da tunanin hukuncin da Ubangiji ya tanadar ma masu aikata shirka ba,Lallai Allah mai jin Æ™aine ga bayin sa.HaÆ™urin da ubangijin mu yake yi damu wani bawan sa ba zai iya yin sa ba.Mukan yi laifi mai muni,mu yi mu maimaita mu nemi gafarar sa ya yafe muna,Lallai ubangiji Mai Rahama ne,Dan haka masu zuwa wajen bokaye ko malaman tsibbo ku ji tsoron Allah ku tuba ku nemi gafarar Ubangiji.
Allah mai yafiya ne da jinƙai ga bayin sa.
Allah ka yi mana shiriya ka hana muna zuwa wajen da zamu haɗa Allah da wanin sa.Da duk wani wajen saɓon Allah,Allah ka bamu ikon tsarkake zukatan mu.Amin.
Dariya ta kece da ita tana gyara mayafin ta kafin kuma ta ce " Na tafi É—an Baiwa sai wata haÉ—uwar ".
Ta ɓace ɓatt anan wajen.
Shima kamin ƙayfatawar ido babu alamar zaman sa wajen dan itace ta fito da shi dama.
Allah ka yafe mana zunubban mu.ðŸ˜ðŸ™
A yau ne ake ta shirye shiryen zuwa da MA'ISHA waje kamar yadda suka gama shirye shiryen su dan Daga Suhail za,a je sai Suhaila da kuma Nurse Mira Duk wani shirye shiryen su an gama sa.Su Dady da Amoh sun Bisu da Addu'ar samun nasara cike da kewar ya'yan na su musamman MA'ISHA da tausayin ta ya gama mamaye zukatan su.Abba Saboda ayyukan office da suka masa yawa Suhail yace ba sai ya je ba shi kaɗai ma ya isa ita Amoh ba,a maganar ta saboda ciwon ƙafafu da take fama dashi.
Jirgin su ya tashi daga babban filin tashi da saukar jirage na Abuja.
In da bai yi tsinke a ko ina ba sai a Canada.
Sun sauka a wata asibiti mai suna British Family Hospital Canada Kasancewar asibitin sun san da zuwan su an riga anyi follow up aka tarbe su cikin karrama wa.
Da zuwan su aka karɓi Ishaa dake ta bacci na Allurar Baccin da aka yi mata kafin barowar su Nigeria dan har aka shirya ta bata san ana yi ba.
An mata gwaje gwaje aranar sai dai kamar koda yaushe bayanin irin ɗaya ne da sauran asibiton ke nuna wa dan basu ga komai ba duk da sun yi mamaki saboda ƙwararru ne ke kula da ita asibitin ma gaba ɗaya dan shi kan sa Suhail ba baya ba amma yana son wasu su ƙara bincika masa,ko za,a dace su san inda matsalar take.Dan haka suka bawa Suhail haƙuri tare da masa alfarmar zasu mata wannan checkup ɗin na wata ɗaya a gani ko za,a dace.
Cikin Tausayin ta ya amince ganin lokaci ne mai tsawo ya sa yace Nurse Mira ta koma gida aka bar Suhaila kasancewar akwai ƙwararrun likitotan Jinya dan haka Mira ta koma gida ta cigaba da aikin ta kafin dawowar su da suke fatan kafin lokacin an gano matsalar.
Amoh da ke zaune lokacin da Suhail yake yiwa Dady bayani a waya saboda handsfree take, wani irin hawaye ne suka silalo mata ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta isa wajen yarinyar ta amma ina.
Kuka ne ya ci ƙarfin ta haka Dady ƙarfin hali yayi dan lamarin Ishaa ya fara bashi mamaki matuƙa mamakin ma na ra sa abun yi amma duk da haka addu,a yake cigaba da bin ta da ita cikin zuciyar sa yana share ma Amoh hawaye da girgiza mata kai wadda kuka ya ɓalle mata.
Wanda da ƙyar ya samu ta natsu bayan ya bata baki wanda shima kan sa ƙarfin halin ne kawai yake yi.
A haka suka share wata ɗaya A Canada sai dai tsit kake ji babu wani bayani ƙarshe ma Dr Barack da yake abokin sa shi ya kira Suhail gefe ya bashi haƙuri dan sauran sun kasa tun kararr sa.
Cikin lafiyayyen turancin ya sanar masa " I'm sorry gaskiya ba zan ɓoye maka ba Dr.Suhail yarinyar nan ƙwaƙwalwar ta lafiya lau yake bata da matsalar komai,Ku cigaba da yi mata addu'a kuna kainta church,or mosques ana mata addu'a dan bamu ga komai ba ".
Shiru yayi yana sauke numfashi da ajiyar zuciya bayan gama sauraren sa.Dan haka godiya kawai yayi masa tare da amsa addu'ar samun lafiya da yake ta yi mata acikin harshen turanci tare da ambatar Jesus kamar yadda bakin su ya saba.
Koda ya isa ɗakin ta da take jin ya wanda itada Suhaila kawai ke cikin sa komai akwai shine kawai yake cikin otel ɗin da ke cikin Asibitin mai Shegen tsada da kyau dan saboda mafi yawan mutane suna zuwa hospital ɗin neman lafiya saboda ƙwarewar su.