Sashe 98
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
*A ɓangaren Abbu bai samu ganin Mahaj ba sai bayan sallan Magriba.
Da sallama ɗauke a bakin sa ya shiga room ɗin sa kasancewar ya gan sa masallaci kafin ya ƙara sauke kallon sa kan sa ya ɓacewa ganin sa.
Dan haka ya kasa hakurin ya isko sa ya same sa da kan sa.
Kunya ce ta kama Mahaj ganin Abbu dan haka ya sunkuyar da kan sa ƙasa bayan yiwa mahaifin na sa kallo mai ɗauke da soyayya da ƙauna irin ta ɗa da uba.
Dan shi da ya ji knocking a tunanin sa Mubarak ne.
Zaune yake kan ɗai daga cikin rugs dake ƙawace da Falon na sa ya sha baƙar jallabiya yar Moroccco Black color ta masa kyau matuƙa kyau ya haɗu da kyau.
Sai da Abbu ya gama ƙare masa kallo sannan ya saki ɗan guntun murmushi dai dai lokacin da Mahaj ya ɗaga idon sa ya kalle sa ganin bai zauna ba har yanzu ga shi yana jin idanun mahaifin na sa akan sa.
Ɗan lumshe idanun sa yayi a hankali ya buɗe yana zubawa mahaifin sa su da bashi da na biyun sa a wannan duniyar mamakin murmushin da yake ta saki yake yi gashi ya kasa magana bare shi kan shi ya yi magana dan murmushin ya bashi mamaki taya za,a yi mutun yayi ta Murmushi haka babu dalili duk da ya san abbu mutum ne mai sakin fuska amma ya san akwai wata ƙasa.Anya kuwa Abbu lafiya yake zuciyar ta furta masa.
Shima kan sa murmushin ya jefa shi wani irin yanayi sai dai ba zaka iya gane hakan ba kai tsaye dan fuskar sa babu wani alamar murmushi a cikin ta sai dai a sake take.Kasa haƙuri yayi cikin sanyayyiyar Muryan sa da take fita cike da natsuwa da sakewa irin ta ɗa da mahaifi da yar chakuɗaɗɗiyar Hausar sa ya ce " Abbu wani abu ya faru ne " ?
Kai Abbu ya girgiza yana ƙara faɗaɗa murmushin sa kafin a hankali shima ya ce " Kawai farin cikin ganin ka nake yi nayi kewar ka ,shine da ka dawo daga masallaci mai makon ka fara zuwa ka ga sanyin ranka ka shige ".
Murmushin gefen baki ya saki wanda Abbu ne kawai yake samun sa yana yin ƙasa da kan sa.
Riƙo hannun sa Abbu yayi wanda ya san ba zai ce masa komai ba a bazata kuwa ya ji ya ce " I'm sorry bayan isha'i na so naje wajen ka ".
Murmushi ne ya ƙara fita akan fuskar Abbu.
" Bani labari ya komai yake tafiya "
Cewar Abbu kafin ya ƙara furta " Da abun da ya faru da wanda bai faru ba "
ÆŠan kallon sa Mahaj yayi yana zuba masa idanu kamar mai nazari kafin ya janye idanun sa akan Abbu.
Abbu kuwa ya lura dan haka ya ce " Kai nake jira malam ".Ya na haÉ—iye dariyar sa.Ganin kallon da yake masa.
Shiru ne ya biyo baya kowa da tunanin da Yake a ransa Abbu na jiran amsar da ya san ba samu zai yi ba har a zuciyar sa ya sani babu abin da zai faÉ—a masa.
Shi ko mahaj haka kawai zargin Muby ya É—arsa masa amma sai ya haÉ—iye komai bai nuna ya É—an fahimci abun da Abbu ke son ji ba.
Abbu kuwa cike da tsokana ya ce " Ni fa yarinyar nan shatou nake son jin labarin barafasar da kuka sha,Ance ...."
Shiru Abbu yayi yana rufe bakin sa domin ya san kai tsaye zai zargi Muby É—in.Wanda bai sani ba tuni hakan ya faru dan yana jin sunan ya fito bakin abbu sai da ya furta a cikin zuciyar sa I know.
ÆŠan lumshe idanun sa yayi kafin ya buÉ—e su ya ce " Wa yace Abbu " ?
Ɗan shiru yayi kafin kuma ya ce " Wace ce Shaaaa touuu " Ya kai ƙarshen sunan A rarrabe kamar mai tsoron kiran sunan.
Yana sauke Numfashi.
Abbu kuwa zuba masa ido yayi sai dai murmushin sa ko kaÉ—an bai bar kan fuskar sa ba mai cike da kamala da dattijan ta ka.
" Manta kawai ".
Cewar Abbu.
" Shatou kake tambaya ta,ai ka fi ni sanin wace ce hakan,ko ba haka ba ".?
Shiru yayi wa Abbu yana ƙara yin ƙasa da kan sa.Sai dai Abbu na lura da shi domin kuwa bakin shi ya tura gaba da jan guntun tsakin kan leɓɓen sa na tuna riginar su da shatou ɗin yanzu,wanda Abbu ya ji fitar sa a kunnen sa dan haka ya tabbatar da rainin hankali ne kawai na ɗan sa tun da ya mayar da shi abokin wasan sa dan haka ya share zancen yana cigaba da sakin murmushi inda ya canza wani zancen daban.
Mahaj kuwa tunda Abbu ya chan za magana ya É—an saki jikin sa suka fara yar fira irin ta É—a da uba wadda ta shafi rayuwar su ta baya da ta mahaifiyar Mahaj É—in.
Suna a hakan a ka kira sallan Isha'i a tare suka fice kasancewar dukkanin su sunada Alwallan su.