Sashe 103
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hmmm to Allah ya bada mai albarka "
Cewar Inna ni idanun na ja sauya wa daga farin madarar su izuwa duhun damuwa da ya fara lulluɓe su.
" To me ya sa ki ka bar É—an mutane a tsaye oh ni Indo ".
" Ai shi ne naga yana mun amfani shi ya sa,amma Ni kam bana son sa wanda ko bakin sa baya wanke wa,duk wari yake yi sauƙin ta ma shima yana saka dan turare ko kaɗan ne,Kai saka turare sai Batu.."
Shiru tayi ta ƙi kai ƙarshen maganar sai kuma ta ja guntun tsaki ta ce " Maye "
A bayyane.
" Waye maye kuma " ?
Cewar Inna ni.
" Da wannan Baturen nake wallahi Inna ni ba a daɗe ba na gan sa a mafarki na kusan sau uku wai yana riƙo hannu na na zo mu tafi ".
Cewar shatou.
" To fa ku je ina " ?
Inna ni ta tambaya.
" Waya sanar masa,ai ni da zan ƙara ganin sa da nace masa wallahi yayi wa aljanin sa magana duk na ƙara ganin sa sai na ƙona su,har dashi,dan na san Aljannun sa ne ƙila ".Tayi maganar da iyakar gaskiyar ta.
Inna ni dake sauraren ta murmushi kawai ta yi.
" A,a shatou mutanen birni kike ƙokarin faɗa da su ki rufa mini asiri ki bar natsuwar da nake da ita yanzu ta zauna kar ki fara kin ji ki bar ni da sauran farin ciki na".
Shatou dai sauraren ta kawai tayi ba tare da ta fahimci komai ba na inda zancen Inna ni ya kaɓa.
Shiko Bibu sai dariya yake yi yana kallon Shatou dake maganar cike da ƙuruciya yana tunanin taya za,ayi ta iya faɗa da aljani bayan ga Shamsu ma ba ta iya karawa da shi duk yadda take cika baki idan ta gan sa zata masa rashin mutun ci.
Inna ni dai bakin ta kawai take kallo tana dariya.
Dan labarin yadda ta tare musu hanya ta basu kafin kuma koma bada labarin yadda Mopol ɗin nan yake tafiya da yadda Ogan su yake wani shan ƙamshi harda kwaikwayon tafiyar sa.
Daga ƙarshe dai bayan Inna ni ta gama shan dariya ta mata nasiha da kulawa da barin raina manyan ta.Tana bin ta da addu'ar shiriya.
Sannan ta ce ta cigaba da Addu'a rashin Addu'a ne ka saka ta yawan wannan mafarkin.
Salloli da aka fara ne ya tayar da su daga firan da suke yi ta bikin sallah da suke bawa Inna ni yadda wasu suka yi kyau wasu basu yi ba,wasu ma basu samu É—in kin ba take ce musu su gode wa Allah.
Masallaci Bibu ya wuce.
Tare suka dawo da Baffa na aka sha fira kafin kowa ya wuce makwancin sa.
Sai dai fa shatou maganganun Shamsu sun sako ta gaba ji take kamar yanzu yake nana ta su,sai kuma maganar Auren ta da Iro da Inna ni tace mata wasa take yi mata ko maganar bata yi da Baffa na ba ganin ta matsa mata da tambayar bayan sun gama sallah wai dagske take yi.,Bacci ɓarawon ne ya kwashi shatou a yau bayan ta gama Addu'a.Dan musamman maganganun Shamsu sun mata tasiri ƙwarai da gaske..
Yau Sallah kwanan ta goma sha biyu ciff inda ya kasance saura kwana biyu Abbu su shigo wajen ƙaddamar da ayyukan da aka kammala.
Shatou ce zaune ta buga ta gumi idanun ta sun zubawa waje É—aya ido kamar hankalin ta baya jikin ta.
Inna ni ce ta fito tana cewa " wai baki wuce wajen Sallahn ba har na gama na fito "
Ganin shatou bata ma nuna ta san da ita take ba hakan ya sa ta ƙare mata kallon ƙwass ga wani irin tsoro na kama ta domin kuwa ta lura da shatou cikin yan kwanakkin nan tana yawan yin shiru ko ta makure gefe ta zubawa waje ɗaya ido ga shi ta ƙara yin wata irin rama kamar mai ciwon yunwaaaa...
Ajiyar zuciya Inna ni ta sauke kafin ta matsa kusa da ita ta dafa ta ta kira sunan ta.
"SHATOU"!
Ai ko da sauri shatou ta kalli gefen irin a tsorace take babu zaton nan.zuba mata ido Inna ni ta ƙara yi kafin ta ce " Me ya ke damun ki wai,ke ba Damuwar komai ba amma ki zauna ki yi mini shiru ga ramar da kike ta yi,me yake damun ki ".
Kuka ta fashewa Inna ni dashi wanda ke fitowa har ƙasan zuciyar ta sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi shiru Inna ni bata samu damar rarrashin ta ba domin mamaki abun ya bata da tsoro dan tsoron ta kar ace wani abu ya faru da shatou bata sani ba duk yadda take saka ido akan ta.
" Me yake faruwa wai ko sai na ƙara saka ki kukan yin kukan mai dalili ".
Ajiyar zuciya shatou ta sauke kafin ta ce.
" Inna ni ji nake kamar zan mutu kowane irin lokaci,sannan ƙirji na ke bugawa da ƙarfi kullum, taɓa ki ji fa,Ni na san tafiya zan yi na bar ku,ban ga kin haifa mini yar ƙanwa ba ".Ta kai ƙarshen zancen ta na ƙara fashewa da wani irin kukan da ya fi na ɗazu.
Ita kuwa Inna ni wani irin rintse idanun ta tayi jin yadda zuciyar shatou ke mugun bugawa da kuma kalmomin ta da suka jefa ta cikin wani irin yanayi na tsoro da firgici duk yadda ta so ta hana hawayen ta zuba a wannan karon gaban shatou sai da suka silalo suka sauka akan kafaɗar shatou da ƙirjin ta yake cigaba da mugun bugu mai hana jiki da ruhi zaman lafiya.
Chak ta tsayar da kukan na ta kafin ta ce " Inna ni kin ji ko "
" Dan Allah ki mini Addu'a Allah ya sa ba mutuwa zanyi ba,bana son na mutu yanzu na Barki ".
Wasu hawaye ne ke ƙoƙarin ƙara sauka akan fuskar Inna ni indata haɗiye su, Shatou kuwa jin hawayen Inna ni jikin ta sai ya ƙara karya mata zuciya sai take ganin kamar Dagaske mutuwan zata yi itama Inna ni ta ji tunda har ta ji danshi kamar kuma hawaye a kan fuskar ta.
Kuka ta ƙara fashewa dashi.
Wanda da ƙyar Inna ni ta rarrrashe ta tayi shiru..
" Je ki kiyi Sallahn ki in sha ALLAH ba zaki mutu ba sai kin haifa mini jikoki ".
" Ba zaki tafi ki barni ba cikin wannan duniya mai abun tsoro shatou ina ji a jiki na kece haske na,da zai yaye mini duhun da nake ciki ke ce zaki kai mu ga hasken da zamu yi farin ciki a tare ".Ta yi wannan furucin na biyu a cikin sauti mara fita wanda shatou bata ji ba.
Shiru shatou ta yi tana sauke ajiyar zuciya tana jin wani sanyi a ranta.
" Ki cigaba da na na ta Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un kinji wannan abun da kike ji zai daina babu komai in Sha ALLAH Alkhairi ne,bana son wannan yawan shiru shirun yanzu idan kin gama Sallah kije ki same su wajen farautar "
Aiko da sauri shatou ta washe baki tana furta " Dagaske Inna ni "? Kai ta gyaÉ—a mata itama cikin Murmushi mai haÉ—e da wani irin rauni da mugun tausayi.
Aiko cike da ɗan kuzarin da shatou ta samu ta yi alwallah sannan tana gama sallah ta yi addu'a Sannan ta fice dan dama tace zata je Inna ni ta hana saboda bata son tana Guje guje kuma ta san muddin suka fita sai ta yi gashi dai ta fara zama yar budurwa duk da ƙirjin na nan shafe har yanzu sai tsawo da take ɗan yi.
Da kyawun ta dake ta ƙara bayyana fili makerin kyau na ta aikin sa.
Ficewa tayi daga gidan bayan ta yiwa Inna ni sai ta dawo,yanzu bata ma yin fargaban fita saboda ta san Iro na kare ta dan duk inda ya san Shamsu yake yana bibiya.Da ya ji labarin zai je wajen ta sai ya tare shi su yi ta rafka artabu tsakanin su.
Kuma tun daga wannan rana sai Shatou ta saki jikin ta,saboda yadda maganar Inna ni ta mata wankin Damuwar da take ji a jikin ta da wani irin tsoro da ke shigar ta.
Duk da wani gefe akwai É—an tsoro sai dai mara yawa.
" Wallahi ni bana jin tsoron ka,dan haka baka isa ka kashe ni ba,sai lokaci na yayi ".
Kallon ta yayi da kyau ganin yadda ta riƙe ƙugu.Babu tsoro ko ɗar akan fuskar ta ko da chan tana shanye abun ta bai ta ɓa ganin Zallar tsoron sa ba a idanun ta
Wata muguwar dariya ya saki kafin ya ce " Ke ni zaki saka a tozar ta gaban abokai na ".
" Wallahi sai na illata ki,sai na cusa Miki baƙin ciki ".
Dai dai nan Iro ya bayyana yana furta " Allah kaÉ—ai ah haka ".
Kallon sa Shamsu yayi kafin ya ja tsaki yana jefa masa muguwar Harara.
Cikin rashin damuwa da son ƙara ƙure Shamsu ya ce.
" Shatou na ina zaki je ne "
Baki ta fara turawa gaba jin sunan da ya kira ta da shi da ta mugun tsana wai shatou na.Mugun jin zafin sunan take yi bata da yadda zata yi ne da ta hana shi kiran sunan ta ma gaba É—aya.
" Wajen Baffa na zanje farauta ".
Ta bashi amsa.
" To tafi,kuma ki kula da hanya ".
Ya furta mata yana sakin murmushi yana ƙara washe bakin sa ganin ta gyaɗa masa kai kamar irin yana da mugun iko da ita.
Hmmm.😠IRO yan love manya.LOl🤪
Bari dai nayi shiri kar shatou's fan su wullo mini daƙuwa.😂🤗