Sashe 8
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zama tayi jagwab akan gadon tana sauke ajiyar zuciya kafin ta saki guntun murmushi tana kallon wayar ta da ta gama amfani da ita yanzu bayan shigowar ta É—aki.
Wani kiran ne ya sake shigowa akan wayar hakan ya sa ta É—aga da sauri tana furta " Abban su Barka " Bayan amsa Sallamar sa.
"Sun dawo school ko,Injin ba,a yi halin ba " .Kai ta girgiza kamar yana gaban ta kafin tace ''Basu yi ba yanzu haka ma sun fito yin lunch "Murmushi yayi mai sanyi yana jin wani irin farin ciki na mamaye sa.Itama murmushin ta saki kafin suka ƙara yin maganar dawowarsa dan yaje yayi attending wani business class a Morocco wanda yana yawan tafiye tafiye kasancewar sa ɗan kasuwa Babba,A halin ma gaba ɗaya tunda ga kakan su Yan kasuwa ne familyn basa wani aikin gwamnati face kasuwancin su in ka cire Bilal da yake da muradin aikin soja wanda shima yana taɓa Business ɗin sosai bai saki gadon gidan na su ba.
SHATOU
Yau ta tashi da wani matsanancin ciwon kai wanda ya hana mata zuwa makarantar allo ta safe a safiyar lahadin,tare da ayyukan da ta saba É—an jagwalgwalawa mahaifiyar ta,tunda ba wani iya wa tayi ba ita dai barta da aikin gidan ta horu da iya share share da yan goge amma ta fannin girki ba,a cewa komai.
Baffa yau ya ma kasa iya fita farauta ko kaɗan,Bibu ma da ƙyar ya iya tafiya makarantar.Kula take samu ta ko ina Baga Baffa ba Baga Inna ni ba ita kuwa an samu abun yi sai ƙara lanƙwashe wa take yi,dan ko abin karin daƙyar ta tsakura ta sha magani ko shi sai da INNA Ni tayi daƙyar.
Sai zuwa maraice ya ciwon ya lafa mata dan ba kasa fai take kwanciya ciwo ba tun dai wanda ta sha yi lokacin tana ƙarama saboda rashin samun kulawa ta uwa dan Inna ni tayi wata rashin lafiya sosai Alokacin Baffa na bai ma taɓa tunanin zata iya samun lafiya ta koma dai dai ba.
Da ƙyar Baffa na da Bibu suka iya fita shi ya wuce farauta shi ko ya wuce makaranta,wadda sai da aka rarrashi shi sannan ya wuce harda yan hawayen sa.
Cikin abinda bai wuce daƙiƙa ba jikin Shatu ya ƙara rikicewa Hankalin Inna ni ya tashi matuƙa musamman ganin yadda jikin ta yake jijjiga tsoro abun ya bata wanda ya sa ta zuba ma yar Tata idanun ta kawai tana kallon ta,tana fatan abun ya tsaya nan, kafin wasu hawaye masu zafi su zubo mata dan ko rantsuwa tayi bazata yi kaffa ra ba tsohon ciwon ta ne ya tashi na matsalar jinnu da tayi fama dasu shekaru uku da suka wuce dama shine abinda take gudu tun safiyar yau da ta tashi da matsanancin ciwon kan cikin ɗarr take na abinda kan iya zuwa ya dawo.Riƙo hannun ta tayi.tana tofa mata Addua,a kafin cikin wani irin kuka Shatou ta fara magana ƙasa ƙasa ganin bata jin abun da take faɗa hakan ya sa ta kara kunnen ta a bakin ta " Suna cikin matsala rayuwar su na cikin hatsari,Kuyi wani abu zasu hallaka su,zata samu sauƙi zata samu waraka zata sami lafiya ".
Tana gama furucin kuma sai wani irin bacci ya kwashe ta,mai Nauyi.
Wani irin kuka ne ya ƙwacewa Inni ni wanda ya sa ta durƙushe wa nan tana rungume yar ta cikin wani irin baƙin ciki mara misaltuwa itama take jikin ta ya ɗau zafi saboda kukan da ta yi gashi babu mai rarrashi.........
Meye matsalar Inna ni wai ???
Haba na san a rina shatou ku ba ita kaɗai take ba ahe 😂😂Mai gari ya mata uzuri🚶🚶
Wasa farin girkiâœï¸âœï¸
Wannan labari na kuÉ—i ne akan N#1000. Yanzu muna kan free pages, kuma baza,a same su da yawa ba gaskiya dan haka kuna iya fara yin payment.
1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
*08069059746*
Daga
AlÆ™alamin âœï¸
GIMBIYAR TASKIRA 👑
FA'EEH BG âœï¸
FIRSTLADY 🙌
LIKE,REACT, COMMENT sune kawai nake buÆ™ata,shine zai nuna mini yadda kuka karÉ“i book É—in..âœï¸
_*Typing*_
Update 👇
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn
*Masu son ganin ƙarshen labarin sai suyi following channel ɗita.👇*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*💋KURMAN ƘADDARA💋*
©®Fa'iza Almustapha Murai
Daga Alkalaminâœ
*FA'EEH BG*
💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18.A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
_Daga marubuciyar littafin_
*A MAFARKI NASANTA 1&2(paid)#500*
*RAYUWAR MU A YAU complete (free)*
____________________________________
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
___________________
*MUNA TALLATA HAJA KOWACE IRI CE A FARA SHI MAI SAUƘI...*
*BOOK ONE*
free pages👌
P...0ï¸âƒ£5ï¸âƒ£
Sai da tayi mai isar ta Sannan ta share hawaye ta tare da gyara ma Shatou kwanciyar ta dan baccin take mai nauyi kuma da alama yayi mata daɗi.Dan rage ma kan ta tunani ne da yake son kutso mata ya sa ta janyo wata tsohuwar saƙar da ta fara ta cigaba da yi tare da ƙara sautin redion da yake fitar da sautin Qira'a mai daɗi ta Sheikh sadiqu Sadiq Gusau.
Tana nan zaune har aka kira sallar la,asar sannan ta miƙe ta gabatar da sallah tare da jerawa Ubangiji damuwowin ta da suka cike zuciyar ta.Tana gamawa ta tsakuri abinci kaɗan Dan bata jin ɗanɗanon sa ko kaɗan saboda yadda zuciyar ta take harbawa tun bayan kalaman da suka fito daga bakin Shatou suka shiga kunnen ta.Duk ta tuno da zantukan sai jikin ta yayi wani irin mugun sanyi sai ta ƙara jin wani irin rauni ya ta so mata.Bata da mafitar da zata iya yin komai akan zancen da Kunnuwan ta suka jiye mata face ta miƙa lamurran ta ga Ubangiji shine wanda ya san damuwowin ta.Zama tayi a kusa da SHATOU tana zuba mata idanun ta wasu irin hawaye masu zafi suka silalo mata wayen da bata ma shirya wa fitowar su ba.A hankali ta ware idanun na ta da suka bayyanar da yanayin rashin lafiyar ta ta sunyi wani irin garai garai ta zuba su kan fuskar Mahaifiyar ta ta da ɗigon hawayen ta ya ɗigar mata a kan fuskan ta, da ta ƙara yin fayau tsantsan yarinyar ta ta ƙara fitowa ƙarara dan Shatou da ace irin gidajen masu kuɗi ne masu sangarta yara da har yanzu babu aikin da ta iya saboda shekarun na ta da kuma girman ta bata da wani girma haka take yar firit da ita.
" Inna ni " Cikin sanyi Sautin ya shiga Kunnuwan Inna ni da ke duƙushe gaban shatoun.Idanun ta ta share da sauri tana goge hawayen da ke ƙoƙarin sake fito mata.Da murmushi ta zuba ma Shatou idanun ta kamar yadda ta zuba mata nata tana ƙaƙalo dariyar farin ciki ganin shatou ta tashi garass babu wani ciwo à jikin ta da alama zazzaɓin ya sauka ma gaba ɗaya." Sannu kin tashi ya jikin,ina yake Miki ciwo yanzu " Inna ni ta jera wayen nan tambayoyin tana shafa fuskar Shatou cikin Tausayin ta.
Kai SHATOU ta gyaÉ—a mata tana kallon ta cikin ido ganin yadda idanun ta suka yi jaa kaÉ—an na kukan da tayi a É—azu.
"Inna ni kawai dan ban da lafiya kika yi kuka haka,?Ashe haka kike so na ban sani ba ".Shatou tayi zancen kafin kuma ta ƙara sa zancen Baffa na dake tsaye a gefe ya sauke Numfashi tare da girgiza kan sa cikin tausayin su.Sannan ya ƙara so ciki yana maimaita wata sabuwar Sallamar dan tun ɗazu ya shigo tun lokacin da Inna ni ta durƙushe ƙasan idanun ta na tsiyayar da hawayen da bai san dalilin zubar su ba a wannan karon duk da ya saba da irin wannan yanayin nata.
Amsa masa sallamar sa suka yi a tare cikin washe baki Shatou tayi masa Barka da dawowa tana miƙewa daga kwance cikin ɗan ƙarfin da ya rage mata.Washe bakin sa yayi yana kallon ta yana furta " Shatou na ta murmuje sosai ko dan da alama Kwana kika yi mai daɗi ".
Murmushi tayi tana gyaÉ—a masa kai dan ita kam iya sanin ta tunda su Baffa suka fita bacci ya kwashe ta sai yanzu.Kuma gashi baccin ya tafi da ko wane ciwo na ta.
" Masha ALLAH,Allah ya ƙara sauƙi Shatouwa ta ".
Ya furta yana cigaba da murmushi mai cike da natsuwa.Baki ta Turo gaba jin ya kira ta da Shatouwa sunan da bata so,kuma shine ƙaɗai ya ke kiran ta da wannan Sunan.
Kayan farautar ta sa ya ajiye a ma,ajiyar su sannan ya zo ya zauna yana ƙara yi ma Shatou ya jiki tana Amsawa fuskar ta a washe.Inni ni kuwa abun farautar ta sa da ya ajiye ta miƙe ta ɗauka ta ajiye shi a inda ya dace zuciyar ta cunkushe da tunani kala kala.
Baffa na dai idanu kawai ya bita da su yana jin wani Tausayin ta na mamaye shi kafin ya sauke idanun sa ƙasa yana tasbihi Sannan ya mayar da kallon sa kan SHATOU " Baffa Banyi Sallah ba fa,Inna ni bata ta da ni nayi Sallah ba ta bar ni ina ta barci ".Kan ta ya sha fa a hankali sannan ya furta " Inna ni bata kyauta ba gaskiya tashi kiyi Alwallah ai lokacin ta bai wuce ba ''.
Cikin ɗan kuzarin ta kuwa ta miƙe tana washe baki Ruwan da ya ajiye mata yanzu a buta ta ɗauka ta zaga makewayi sannan tana fitowa ta ɗaura Alwallah ɗakin ta ta shige ta ɗaura zani mai girma ta kabbara Sallah.