← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 110

Sashe 44

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

____________________"Banji ba sosai Saboda na suma a lokacin amma kafin na ƙarasa fita hayyaci na,naji tana ƙara nanata sai ta kashe su,sai ta kashe ta,sai kuma bakin ta da na ga yana motsi a hankali tana faɗan wani suna nidai na kasa kawo shi Amma kamar yana tashi da Ta...,daga nan ban ƙara sanin abun da yake faruwa ba."
Nana tayi furucin cike da kalamai masu nuna tausayi dan Dagske tana jin Tausayin Ishaa Matuƙa.
Amoh ɗan numfashi ta sauke bata jin daɗin rashin jin ƙarashen sunan ba dan ta so ta ji sunan wa ta kama dan su har yanzu basu yarda da ciwon Ishaa ba saka hannun wani bane saboda yadda suke fafutika kan neman maganin ta amma abun babu gaba babu baya.Sai dai basu matsa ba sun dage da yin addu'a da miƙa lamurran su ga Allah shi ya jarabce su kuma shi ne zai yi maganin matsalar a lokacin da ya so.
Taimaka ma ta Amoh tayi suka fice a tare dan itama tana buƙatar ganin likita saboda yadda ta ji raunuka.
Suhaila ta yi driving na su dan su Rayyan da Daddy sun wuce.
A Chan a sibiti kuwa saboda sanin mahimmancin su Dady da matsayin da yake dashi da irin shares da yake da ita kaso biyu,na asibtin,aka karɓi Ishaa cikin sauri da karrama wa,da kulawa aka fara bata taimakon gaggawa domin dama duk sun san ƙaunar Dr.Suhail ce wanda sun san da ace yana nan shi zai kula da ita a gida ma ba sai anzo nan ba sai in abun ya ɓace.Cikin ikon Allah an samu ƙwararrin likitota suka hau kan ta sun ɗauki kusan awa ɗaya suna duba ta kafin suka samu Dawowar Numfashin ta da dai dai tar bugun zuciyar ta.Alluran bacci suka yi mata mai ɗan karfi saboda yadda jinin ta yake dan zata iya farkawa yanzu ba tare da tayi mata wani aiki ba.
Haka Ita ma Nana an karɓe ta anyi mata treating raunukan ta kamar yadda aka yiwa Ishaa nata aaka tsaftace mata jikin ta.
Tunda aka sanar da su halin da take ciki yanzu suke sauke nunfarfarshi kowa fuskar sa babu yabo babu fallasa sai dai tana cike da damuwa mai tarin yawa wadda suke jin babu ranar gushewar ta sai ranar da suka samu lafiyar yar su.
Rayyan ne ya sauke waya akan kunnen sa bayan ya gama waya da ɗan uwan sa da ya kira shi hankalin sa tashe saboda samun labarin halin da take ciki da Wani daga cikin friends ɗin sa Doctors ya sanar masa an kawo ƙaunar sa ciwon ta ya tashi,ta ji ma kan ta ciwo .Bawan Allah take hankalin sa ya tashi seminar da yaje yi yaji zai iya barin ta duk da kasancewar ta mai matukar Amfani dan International seminar ce sai dai a nan Nigeria za,a yita,Lagos.Kwantar masa da hankali Rayyan yayi kafin suka yanke kiran sai dai ya san cewa bai lallai ya saurare sa cewar da yayi masa da sauƙi ba.
Dan haka kai tsaye ya sanar da Daddy halin da ake ciki.
Shiru Daddy yayi kafin ya ce " kira mini shi ".
Babu musu kuwa Rayyan ya danna ma ñumban ta sa da yayi saving Yaya Suhail.
Ringing biyu ya É—aga dan baya wasa da lamarin ahalin sa musamman abun da ya shafi Ishaaa saboda yadda suke mugun Tausayin ta.
Miƙa wa Daddy wayar yayi ba tare da yayi Magana ba.Shiru yayi jin Dady na kiran sunan sa yana furta " Na san halin ka,kar ka baro abun da ka je yi zamu bata kulawar da ta dace,kaji ko,ta samu lafiya sai abun da ba,a rasa ba,Allah ya taimaka " .
ÆŠiff ya kashe wayar,Dan bai son ya masa wata magana,duk da ya san bazai Musa ba.
Ajiyar zuciya ya sauke yana ajiye wayar bayan ya gama ƙare mata kallo kamar zai ga komai a cikin ta..
Numfashi ya sauke yana komawa ya zauna daga tsayen da yake bakin window yana shaƙar iskan da yake kaɗawa mai daɗi yana ji kamar yayi tsuntsuwa ya samu kan sa a cikin asibitin..
Dady Saboda yana da wani meeting da zai yi hakan ya sa ya bar su Amoh nan sai dai yana fitowa yayi murmushi ganin securites nasa da suke tsaye cogai cogai.
Bata re da yace komai ba ya shiga motar da ya tuƙo da kan sa sai dai a wannan karon wani daga cikin su ya tuƙa ta.
Amoh ma gida suhaila ta matsa mata ta koma saboda yana yin jikin ta ga ciwon ƙafafu da take fama dashi dan haka kai tsaye aka mayar da ita gida inji ɗai daga cikin securites da aka bar musu.
Nurse Mira da bata san abun da ke faruwa ba ta zo gidan sai dai tun abakin gate ta samu labari ga securites cewa an fita Ida Ishaa amma Hajiya da Alhaji sun dawo dan haka cike da tashin hankali ta faÉ—a gidan.A kitchen ta tarar da Amoh tana bawa masu kula da girki umurnin abun da zasu yi wadda bata daÉ—e da shigowa ba.
Amoh fuska cike da damuwa ta faÉ—a mata duk abun da ke faruwa,kamar yadda Nana ta mata bayani yadda ta fara,Hawaye ne suka wanke mata fuska cike da tausayin Ishaaa.
" Bari na je na gyara komai kafin su dawo da ita,kuma fa na cire duka kwalaben turaren nan na mayar da su toilet ban san wanda ya dawo mata da su ba anan kan mirror ".
Tayi zancen tana mamaki gashi Itama Nana ta ce wa Amoh ba ita ta jera su ba.Dan haka sai suka yi ta mamaki da tsoro domin sune abinda suke ji mata ciwo a tashin farko idan ciwon ya tasar mata.
" Nikaina abun yaÉ—aure mini kai ".
Amoh tayi furucin fuskar ta cike da damuwa.
Nurse Mira da ta rasa abun cewa ne ta ce " Allah ya bata lafiya,Amoh bari na yi sauri,ina son naje a asibitin " .
Kai Amoh ta gyaÉ—a mata tana wucewa itama tana wuce wa bedroom É—in ta.
Wani irin hawaye ne ya ƙara wanke mata fuska ganin yadda ɗakin ya ƙara hargitsewa komai ya farfashe ya koma kamar ba,a taɓa zama a cikin sa ba har ta mirror ta fasa shi ga kwalabe nan zube an farfashe wanda ita kanta idan bata yi ta ka tsantsan ba zata jima kan ta rauni.Dan haka babu jira ta cire hijab ɗin ta ta lankafe sannan ta koma ta ajiye jakar ta a ɗakin Nana da shima farkon shi a hargitse sai da ta shiga ciki ma ne shima ta ga ga kaya nan a watse.
Cike da rashin kuzari na Tausayin Ishaa ta fara gyara komai bayan ta kwashe kwalaban turaren da suke masu kuɗi saboda manya ne dukannin su babu karami sai Shegen ƙamshi da ɗakin yake ta yi saboda yadda turarukkan suka watse akan carpet da ta mahe ɗakin.
Tsaf ta gyara É—akin ta sanya sabon bedsheet dan wanda aka cire ko kwana biyu bai yi ba.Dan jiya Nana ta saka mata shi..
Dai dai ta gama Amoh da masu girki sun kimtsa komai dan ba wani abu mai wahala aka yi ba irin wanda zata iya ci ne ruwan zafi sai masan ƙwai da irish da suka soya mata irin mai haɗe da kayan miya da kuma ƙwai a cikin sa.
Nurse Mira kuwa kwasar kayan tayi ta fice da su inda dama bata saka motar ta a garage ba dan haka ta jata ta fice.
Koda ta isa Nana ta ɗan wartsake saboda ruwan da aka ƙara mata ta samu ɗan ƙarfin jiki.Sannu ta yi mata cike da tausayin ta tare da furta Allah ya tsayar nan da tsare gaba ya bawa Ishaa lafiya.
Da Amin duk suka amsa mata har Suhaila da ke zaune jugum dan yanzu ta baro sashen da Ishaa take har yanzu ta lura ko motsi bata yi,babu abun ke raba ta da gawa face ɗan ƙirjin ta dake ɗagawa tayi fayau da ita gashi dama ba wani auki ne da ita ba.
Haɗa ma Nana shayi tayi ta haɗa mata duk abun da ta san zata buƙata,Babu musu dama yunwar take ji dan haka ta fara cin abin ta hankali kwance dan ta saba mafi yawan lokuttan da ta kwana gidan a tare da mutan gidan take breakfast sai dai in ya kasance Suhail na kusa ita kan ta gizagon sa take gani dan haka take ka sa iya motsi duk yadda za,a ce ta zauna bazata zauna ba sai dai a saka akai mata ɗaki,har ya kai ta saba mafi yawan lokutta a tare da Ishaa suke yin breakfast ko lunch wanda ake kare shi alalala ce dan ita Ishaa babu hankali ita kuwa sai ta yi ta biye mata,suyi ta haukar a tare.
Cike da kulawa Nurse Mira ta isa ɗakin na ta cikin tausayi ta ƙare mata kallo tare da share ƙwalla sannan ta mata Addua ta rufo ɗakin.
" Ta Baiwa kin halaka,arniya,Ta Baiwa baki da imani,ta Baiwa magajiyar baƙin aljani,baƙin duhu ba naki bane " ..Ya kai ƙarashen zancen yana gaggaɓan dariya mai tsoratar wa dan duk wani cikakken mai lafiya dariyar tsafff zata iya mayar da shi mara hankali dan abun tsoro ce.
Kamar ko yaushe zaune take gaban shi ta tanƙwashe ƙafafun ta cikin baƙar a baya da uban niƙab wanda yake fallasar da manyan idanun ta dake ciki,sai dai ba su bayyana sosai ba dan wanda ya santa ma sai yayi da ƙyar ya gane ta.
Dariyar take gaggaɓa itama wanda ya Kaita har ƙasa kwance kafin a cikin yar bukkar ta sa da kullum take upside down sai dai inuwa ta ko ina duk da ranar da ake watsawa a cikin ƙungurmin dajin.
Sai da tayi mai isar ta tana taya shi sannan ta yi shiru ganin ya sha fuska,ban sani ba ko dama dariyar limit gare ta Amma haka wajan yayi tsit har kukan tsuntsaye ma babu a wannan karon.
" Ta bai wa faɗi damuwar ki da bakin ki,ke nake son jin yadda abun ya dame ki,duk da ɗan duna,da baƙi sun faɗa mini komai,faɗi Damuwar ki a yaye miki,ina son ki ta Baiwa ke ta amana ce, imani da aiki na shine ke ƙara mini ƙaunar ki ta Baiwa tare zamu halaka "...
Ya saki kukan jarirai mai ban tsoro wanda sai kayi zaton ba shi ke yi ba dan kukan bana jariri É—aya ba ne.
Cike da ƙwarin gwiwa da rashin tsoro da rashin damuwa ta ce " Ɗan Baiwa maganar gizo ce bata wuce ta ƙoƙi kuma na san kasan da haka,abun na ƙara ƙuntata ni,Yau naga haske gobe na ga duhu,ya kamata ayi wani abu dan bana buƙatar mai mai ta magana ɗaya Ɗan Baiwa,a wancan karon har su duna na bawa a shayar da su jini amma ban ga wani Haske ba sai duhu da yake ƙara da baibaye ni " .
" Ni yanzu Babbar Damuwa ta ma,kan wannan munfukar matar ne a yi mini maganin ta ta cika shige mini hanci da yawa ".
Ta kai ƙarshen zancen tana jan dogon tsaki.
" Hhhhhhh ta Baiwa ke makakka ce,ai irin su ba da wuri ake kame su ba,ita kan ta ba tsaye take ba haka nan,Rame mara zurfi ba wurin ɓoyon ɓera bane,ki riƙa nazartar wasu abubuwan,zan Miki maganin ta,zamu saka yan jajaye su karya ta,idan har tana taƙama da wani abu ".
Ya kai ƙarashen maganar yana ganɓalan Dariya.
Chapter 44 · 0% Book details