Sashe 27
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ɓangaren Ummah yarda bulalar tayi cike da tausayin LINA ta rungume ta dan ta daku kukan ma ta daina sai zubar da hawaye da take yi a galabaice dan ta ma fi REENA da kuwa.Toilet Ummah ta faɗa kamar zata zubar da hawaye ta haɗa mata ruwan wanka masu ɗan ɗimi sannan ta tada ita da taimakon ta suka shige toilet ta bar ta ta yi wanka da kan ta dan taƙi yadda Ummah ta mata wanda sai abun ya ba ummah dariya wanda ka raina da hannun ka gashi har yanzu bai wuce wanka ba shine da ɓoye ɓoye kamar wani girman tayi.fitowa Ummah tayi ta bar ta tayi wankan Sannan sannan ta haɗa mata shayi mai kauri tare da bada umurnin kawo mata bread da sauran kayan karin kumallo masu kyau.
Tana fitowa ta sanya kaya masu ɗan nauyi saboda zazzaɓi da ya fara saukar mata a jiki na azaba.Da dabara Ummah ta shayar da ita shayin saboda sai wani sabon babin kuka ta buɗe mai cike da shagwaɓa.Maganin da Ummah ta bata kuwa ta kanne shi ƙasan harshe ita kuwa Ummah ganin ta kora ruwa bayan ta saka maganin ba tare da wani musu ba duk da tayi mamaki sai ta ji daɗi dan ta san yadda ake rigima da ita kan magani.Rufa mata tattausan duvet Ummah tayi bayan ta hau gadon da ta so ta zille wai ɗakin ta take so da ƙyar Ummah ta rarrashe ta ta zauna kusa da yar uwar ta zata ji daɗi idan ta farka.Fitar Ummah keda wuya ta buɗe idanun ta tare da ciro ƙwayar maganin da ta ɓoye a ƙasan harshen na ta.chan ƙasan katifa ta ɗaga kaɗan ta sanya shi dan har ya fara watsewa.Ya ƙune fuskar ta tayi kafin ta miƙe ta shige toilet ta kuskure bakin ta.
Sai a lokacin ta kallo kan ta gaban madubi yadda jikin ta yayi Jawur abunka ga fata mai haske ko ina shatin bulala ne.Hawaye ta ji sun silalo mata masu zafi da ƙuna,babu ma abun da ya ƙara gudun kukan ta tuno yadda ta mayar da REENA cikin ƙanƙanin lokaci ita kan ta abun ya bata tsoro dan idanun ta a rufe suke bata san ta aikata ba sai dai Allah ya kawo Ummah da ƙila sai dai ta kashe yar uwar ta,da ita ma ko sai dai ta kashe kan ta.Ta bawa kan ta amsa daga tunanin na ta.
Sai da tayi kukan ta na ƙuruciya da tausayin yar uwar ta kafin ta fito ta je ta kwanta take bacci ya kwashe ta mai nauyi.
***" Ɗan Baiwa Wallahi ina cikin farin ciki dan haka na kasa haƙura na same ka,ɗan baiwa aikin nan bai wargaje ba yana nan,babu abun da ya chanza,da kace sun je Hutu, na kasa yarda ashe dagaske ne,lallai na yarda dakai Ɗan baiwa na yi imani da kai,Lallai kai abun ruƙo ne dole na zube maka manyan chanji yau dan nuna murna ta " " ga na ka gana jajayen aljanu da baƙaƙe a yi musu yan ka a zubda jini su sha su ƙoshi yau ranar su ce hhh ta kece da dariya ".
Macen da ke durƙushe gaban wani yaƙususasshen mutun mai zubin bokaye take zancen, dan babu inda yayi kama da mutanen kirki ko daga inda yake zaune zaka fahimci cewa Boka ne mai saɓon Allah mara imani dan bukkar da yake kai ita kan ta Abar kallo ce Dan upside down take kuma duk da haka rana bata kan musu sai ma wata irin inuwa da ke zagaye da rumfar mai cike da wasu irin surƙulle ɗaure ɗaure gwanin ban tsoro,ga wani irin sauti mara daɗi dake fita shi ba kuka ba shi ba dariya ba,amma matar nan babu alamar tsoro atattare da ita dan da alama ta saba da gurin kuma gurin zuwan ta ne.
Dariya ya kece da ita kafin ya natsu amma dariyar ta cigaba da tashi itama kamar sabon kamu ta riƙa dariya,dariya ta ƙeta harda hawaye.
Wata irin ƙwarya ya nuna mata abun da ta gani ne ya sanya ta ƙara sakin wata irin mahaukaciyar dariya harda kwantawa ƙasa.
Miƙewa tayi zaune jin yana furta " Natsu " Cikin wata birkitacciyar murya mai ban tsoro.
Idanun ta ta zuba masa daga cikin baƙar abayar da take saye da ita da baƙin niƙab da idanun ta kawai zaka iya hange a ciki.Cike da rashin tsoro haka take bin shi da kallo cike da azarɓaɓin son jin abun da zai furta.
" Ai na faɗa Miki ta Baiwa,kin ƙi yarda,sai ma kin so ki watsa muna ƙasa,dan har sun hasala sun so a cire Miki aikin zana,amma tun da kin yi imani da mu kin sha haka muke so mu ɓace tare hhhhh ".
" Kinga yadda kika ga haka haka zasu koma a duk inda suke,mai iya cire wannan aikin sai ni hhh aikin mugaye kenan,ki kwantar da hankalin ki,zai kai ga ci ".
" Sai abu naga ba akwai wani duhu da yake bibiyar ki,shima zamu Miki aiki kan sa,zamu cire sa kar ki damu,Zamu bi hanyar da ta dace idan ta kama muyi farfesun É—an sabon jariri da naman alade dan mu haska wannan duhun muga abun da ke cikin sa "
"Ungo wannan"
Ya furta yana miƙa mata wata irin gora tana ɗauke da fararen ruwa sai dai ga wasu irin halittu nan na yawo a cikin su kamar tsutsotsi.
" Kin san abun da zaki yi da wannan É—in ba sai an maimaita Miki ba ki tabbata komai ya tafi yadda ya dace ".
" An gama ÆŠan Baiwa,É—an gado kafi gado,ko waya ja da kai sai ya bar duniya aikin ka ya ci dubu,babu abun da ke karya ka sai ikon ka,shine ajalin ka ".
Tana gama zancen ta juya bayan ta ta ɓace ɓatt tana sakin wata irin dariya ta ban tsoro.
。â ☬☬â 。☬。â ☬☬â 。
Tun da ya dawo daga ɗakin motsa jiki yaga fitar sa tare da yaran na sa cike da mamaki ya ke bin motocin da kallo har suka bar harabar gidan aka wangale musu gate.Kai ya girgiza dan ya san bai saba hakan ba yayi kwana ɗaya ya wuce ba tare da yayi wa kowa sallama ba.Tunanin da ya shigo sa na ƙila kiran gaggawa ne ya samu hakan ya sa ya cigaba da tafiyar sa yana sauke gajiyar da ya kwaso tare da ta tsufa da take tattare da jikin sa.Hankalin sa ne ya kasa kwantawa hakan ya sa yana shiga Sashen na su bayan ya zauna ya ce " Uwani bani waya ta ".
Miƙa masa wayar tayi tare da ruwan sha da ta ajiye ɗauko masa masu ɗan ɗimi saboda an hana sa shan abu mai sanyi haka ma an saka shi yawan motsa jiki saboda sugar dake barazana a jikin sa.
" Ina kwana Yaya ".
"Lafiya lau,An tashi lafiya ya ƙarfin jiki " Sir ya amsa daga chan ɓangaren dan ba su samu haɗuwa masallaci ba ɗazu.
" Alhamdulillah yaya jiki sai na tsufan mu na ji sauƙi ".
Murmushi Sir yayi yana furta " Allah ya sa mu yi kyakkwan ƙarshe ya raya muna zuri'ar mu ".
"Amin" Ya amsa harda Uwani da ke gefen sa dan wayar handsfree take.
" Yawwa Yaya nace ko Lafiya,naga BILALU ya fice yanzun nan bayan na baro wajen É—an motsa jikin Nan da Turawan chan suka tilas ta mini,kuma kamar tafiyar sauri ce zai yi "
" Shi BILALUn ai bai yi Sallama da kowa ba tun da har kai ma ba ka yi magana dashi ba,to Allah ya sa lafiya,ta yuyu tafiyar gaggawa ce a ka kira sa,amma na san ko ta waya ya na sanar wa ko É—ayan mu ne,bar shi zuwa anjima zan kira sa muji ko lafiya idan bai kira ba. "
Sallama suka yi kowa na fatan Allah ya sa lafiya ce ta fitar da BILAL gidan tun da safe ba tare da yayi sallama da kowa ba...
ä¹âœ¿à¼¼âœ¿â˜¯â ‿â ☯â ✿â ༽✿ã„
A ɓangaren Ummah wanka ta fito tsaf ta shirya cikin shigar ta mai kyau da ke ƙara fitar da ainihin kyaun ta da kamala.
Falo ta dawo cike da bada umurni take bawa su rabi umurnin abun da take son a girkawa su REENA wanda ta san favorite na su dan in ba haka ba ta san da ƙyar su ci abin ci.
Class teacher ta su ta kira bayan ta zauna akan cusion cike da mutun ta wa suka gaisa sannan tayi mata bayanin rashin zuwan na su LINA school sun tashi babu lafiya gaba ɗayan su.Cike da tausaya wa malamar ta musu Allah ya sauƙaƙa tare da furta dama yan biyu haka suke ai ciwo lokaci ɗaya suke yin sa bare su da suke Identical.Sallama suka yi ta ajiye wayar.
Miƙewa tayi tana barin wayar nan tare da shigewa kitchen dan ganin yadda suke gudanar da komai dan ta san BILAL bai da jimirin yunwar safe.
🕳ï¸ðŸªðŸ•³ï¸ðŸª
A ɓangaren SHATOU kuwa da ido tsaitsaye take kallon motocin har suka fice daga makarantar, kallon da ya jefa mata yanzu bayan miƙewar sa na dawo mata,duk da kallo ne na ƙasan ido ta san na rainin wayau ne bai san dama shima cike take dashi ba,Hararar bayan sa tayi wanda shi Mubarak ya gani kai kawai ya girgiza lamarin yarinyar na bashi tsoro bata da tsoro ko kaɗan,sai dai abun da bai sani ba Hararar a kan idanun sa ta sauka saboda ya ɗan juya kaɗan yana kallon yadda take durƙushe babu tsoro akan fuskar ta,kuma ya san cewa dole zasu iya hukun Tata tun da malaman ta ne.
Suna fita ta miƙe tana kakkaɓe hijab ɗin ta cike da ɓacin rai take furta " Wallahi Iro bai isa ya saka ni abu nayi ba ko yanzu biyayya ce nayi ga Malan Bello,amma wallahi Indan iro ne sai dai a yi gunduwa gunduwa da nama na ".